Chapter 32
Chapter 32
bakin ta gaba, iska ya d'an fesar daga bakin sa sannan yace "Ohh am sorry.." yayi maganar yana d'an dakatawa, yana tunanin tsayin maganar da zeyi, ya san tabbas ze dad'e yana yin ta abinda ya tsana kenan, dan haka ya janyo rubber water ya tsiyaya cikin tambulan ya sha, ya d'an sauke numfashi a nutse sannan ya d'ora da "Tun bayan rabuwar mu, Allah ya bud'ewa Abbu sosae, harkokin da yake yi sosae suka samu kar6uwa a wajen mutane, ban san meyasa tun bayan rabuwar mu daga mu har ku babu wanda ya sake waewayar wani ba, bansani ba, abinda kawae na sani na sha tambayar su Abbu ku amma bana samun cikakkiyar amsa wadda zan kama daga wajen sa, tun ina tambayar sa har nazo na dena tambayar sa, se dae har lokacin kina nan manne a rae na, ina jin ki ne acan cikin zuciya ta wanda hakan ne yasa na kasa manta ki a duk tsayin shekarun nan, a cikin wannan lokacin ne na gama secondary school kullum arzik'in Abbu yana yin gaba, dan haka dana tashi yin University ba'a nan nayi ta ba, sena tafi can Cyprus na karanci Medicine, yanzu haka ni cikakken likita ne, muna zaune anan cikin garin Kano saboda harkokin Abbu da suka cigaba, yanzu haka ina da asibiti na kae na wanda shima Abbun ne ya bud'e min, abinda ya kawo ni garin nan kuwa, sanadin k'anin mahaefi na ne da nazo sanda ze bud'e wani Company, tunda nazo kuma Abbu yace kar na zauna haka nan shi ya nemar min wannan lecturing d'in cikin makarantar nan duk da ni ba za6i na bane, da son raena ne aekin da nake kawae ya ishe ni, toh dae dan farin cikin Abbun yasa na fara lecturing d'in, se dae yanzu maganar da nake miki tuni Daddy (k'anin Abbu) ya gama bud'e Companyn komae ya kammala, dan haka ina saka ran ni kam daga wannan semester na gama koyarwa a makarantar nan... And.. ina me tabbatar miki In Sha Allah duk sanda muka had'u zan baki labarin a nutse" ya k'arasa maganar yana sauke wani gauron numfashi lokaci guda kuma yana 6alle murfin gorar ruwan daya ajje ya shanye tass sannan ya ajje ta yana sauke numfashi, dariya ya bata daga inda take zaune jin yadda yake sauke numfashi kamar wanda yayi wani aekin wahala, se dae kuma a ran ta tana cigaba da mamakin rayuwar Rk d'in, lallae Allah abin godiya ne da kuma d'aukaka, dan kuwa shine me yin yadda yaso a kuma lokacin daya ga dama "Uhmm, fad'a min kad'an daga naki kafin mu had'u" sauke numfashi Ayrah tayi sannan a hankali ta shiga sanar dashi makarantar da tayi da er gwagwarmayar da tasha har zuwa yanzun, duk da ba wasu shekaru ne da ita na azo a gani ba, ga kuma ga6un ta dake damun ta, amma duk yadda take ganin Raj d'in take kuma jin sa a jikin ta bata sanar dashi abubuwa da dama daga rayuwar su ba wanda take ganin kamar sirrin su ne wannan da ba kowa ya kamata ya sani ba, shiru Rk yayi yana nazarin maganganun Ayrah a ran sa yana sake tsarkake sunan Allah "Ikon Allah" kuwa ya maemaeta yafi sau nawa "Akwae wata magana dana ke so muyi, amma kafin nan ina so ki gama exam kafin ki koma gida.." "Wace maganar toh?" ta fad'a kamar za tayi kuka, murmushi me sauti yayi sannan yace "Ae nace se kin gama exam tukunnah" shiru tayi tana tuna yanayin Rk d'in a cikin aji da kuma yanzun kamar bashi bane, kamar mutum biyu ne masu kama d'aya wanda wancan da yake shigar musu aji daban shi kuma wannan da suke waya daban "Promise?" ta fad'a tana d'aga yatsan hannun ta kamar yana gaban ta "Yeah.." "Ohk". Wayar sa da tayi k'ara bayan ajiye wayar Ayrah yabi da kallo, ji yayi kamar kar ya d'aga dan a yanzun yana so ne ya dinga samun lokacin daze zauna kawae ya dinga hasaso kyakykyawar fuskar ta, kallan wayar yayi dan ganin me kiran nasa, seya kae hannu ya d'auki wayar ganin Daddy ne ke kiran, ya kae kunnen sa da sallama d'auke a bakin sa "Likita kana ina ne?" "Ina d'aki" yayi maganar cikin girmamawa "Ohk ka same ni a d'aki na idan babu abinda kake" babu musu ya amsa da "toh" sannan ya mik'e bayan ya jefa wayar a aljihun sa ya zura takalmi ya fito daga d'akin nasa cikin nutsuwa. Kae tsaye parlourn Daddyn ya wuce, a hankali ya zura kan sa ciki yanzun ma da sallama a bakin sa cikin nutsatsiyar muryar sa, amsawa Daddy yayi yana kallan sa lokacin da yake k'ok'arin zama a k'asa "Tashi ka zauna akan kujera magana nake so muyi ae" seya d'an yi murmushin nan nasa me tsada wanda ke sake fito da aenahin tsagwaron kyawun sa ya zame akan kyakykyawan Carpet d'in dake shimfid'e a k'asan d'akin yace "Daddy nan ma ya isa" murmushi Daddy yayi a ransa yana sake jaddadawa kan sa lallae abinda suka yanke ba suyi laefi ba "Amm yaushe zaku yi hutu ne?" seda ya d'an yi shiru sannan yace "Ina tunanin baza mu wuce 1 month ba" "Toh Allah ya taemaka, me kake shirya mana zuwa lokacin?" yamutse fuska yayi dan shi sam bema fahimci maganar Daddyn ba dan haka ya furta abinda ke ran sa "Daddy ina ganin zan ajiye lecturing d'in nan gaskiya am tired" ya fad'a dan da gasken ya gaji da lecturing d'in musamman daya kasance dama ba za6in sa bane, ga kuma muhimmiyar maganar da yake so daya koma yayi wa Abbun magana akae, wadda yake had'e da albishir d'in daze fad'a musu su duka cewar bayan tsawon shekarun nan ya had'u da Ayrah, wanda hakan na nufin Abbu ze had'u da Abba, may be ma abotar su ta da ta dawo sabuwa duk da be san abinda yasa kowa yayi watsi da d'an uwan sa ba "Haba haba dae Raj ka gaji kuma?" jinjina kae yayi ba tare daya kalli Daddy ba "Toh ya za kayi da Abbun ka kuma?" Daddy ya tambaya yana kallan sa "Zan same shi da maganar In Sha Allah" "Toh hakan ma yayi, seka maeda hankalin ka waje guda kenan, Allah ya taemaka.. Ameen" shiru ne ya biyo baya Daddy na tunanin ta inda ze farawa Rk maganar se can dae yayi k'arfin halin fad'in "Kana jina koh?" "Ehh.." Rk ya fad'a, kafin Daddy ya kae ga cewa komae wayar sa ta shiga ruri, seya janyo wayar yana kallan me kiran, da sauri ya kalli Rk yace "Raj je ka, za muyi maganar In Sha Allah, zan yi waya ne yanzun" jinjina kae kawae yayi ba tare da yace komae ba ya mik'e ya fice daga d'akin. ... A d'aya 6angaren kuwa Umma ce ta fito daga d'akin ta, dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ke tsaye bakin k'ofar d'akin sa hannun sa dafe da k'ofar d'akin yana sauke numfashi kamar wanda yayi tsere, da sauri Umma ta k'arasa tana kallan sa "Sadeeq lafiya kuwa?" tayi maganar tana rik'o shi "Haki kake?" ta fad'a sanda ta gama d'ago shi tana kallan fuskar sa, da sauri ya k'ak'alo murmushi ya wanzar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70