Skip to content

Chapter 68

Chapter 68

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

fad'a tana k'arasawa kan gadon, a hankali ta haye kae ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin sa tana rik'o shi sosae kamar zata koma cikin sa tana sake shigar da jikin ta cikin jikin sa, da wani irin sauri ya bud'e idanun sa sanda yaji ta kane_kane cikin jikin sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janye ta daga jikin sa kafin ya mik'e yana kallan yanda take wani sake gaggantsarewa tana kuma narke fuska ita a lallae dole shagwa6a take yi, shi sam bema lura da abinda take yi ba, dan idanun sa na kan fuskar ta ne yace fuskar sa a tamke "Ke wae er kunyar nan irin ta mata baki da ita ne?" ya fad'a ran sa a matuk'ar 6ace cike da haushin wannan banzan halin na ta.... Mhiz Innocent......✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 040 ___Yanayin ta sam be nuna ta damu ko taji haushi ko zafin maganar daya fad'a mata ba, se dae ta kama kan ta bata sake gigin ta6a jikin sa ba, seda ta sauko daga kan gadon sannan ta sake basar da maganar daya fad'a mata kana tace "Amma dae ko ba komae ka fad'a min dalilin daya hana ka dawowa a jiyan koh?" k'aramin tsaki yaja har lokacin be kalle ta ba, baya jin ze k'ara koda rabin awa ne a cikin gidan nan da wannan matar, dan tabbas idan ta cigaba da wad'annan halayen na ta zuciya na iya tunzura shi ya fad'a mata maganar da ba zata ta6a mantawa da ita ba har abada "Zaki iya fita in shirya ko kuma na bar miki d'akin?" yayi maganar yana fiddo da wasu kayan daga cikin wardrobe, seda ta d'an sake gantsaro jikin ta kafin ta matso gaban sa tace "Bari na fita Baby, amma don Allah ka dawo da wuri.." shiru yayi na en wasu sakanni kafin yace sanda ya juya ya ajje kayan hannun sa kan gado "Sorry.. Ba'a nan zan kwana ba.." da mamaki take kallan kyakykyawar fuskar sa da kullum take gani take kamar ana k'ara masa kyau ne "Ba'a nan zaka kwana ba kuma Baby?" ta tambaya tana jin wani irin haushi ganin har lokacin yama k'i kallan koda shigar jikin ta ne ballantana hakan ya tabbatar mata da ze iya jan hankalin sa, jinjina kae kawae yayi "Amma meyasa? Amarya ce ni fa.." tayi maganar tana ji kamar ta rusa ihu, shiru yayi na en wasu sakanni kafin yace a nutse lokacin daya zubawa fuskar ta kyawawan idanun sa "Ohk in zauna kada in yi abinda ke gaba na koh?" ya tambaye ta cikin tsare gida, seda ta zame nata idanun da yanzun ma suke d'auke da lashes na kanti kafin tace "A'ah.. Ba haka nake nufi ba fa.." ta fad'a da er rikicewa da kallan da yake bin ta dashi, gefe guda kuma tana jin dad'i dan tasan yanzu kam tabbas yaga shigar jikin ta, abu d'aya take jira shine yayi wani abun daze nuna shigar ta ta ta tafi dashi, jin da tayi shiru har na wajen minti 1 ya sanya ta gyara tsayuwar ta tana d'an sake kad'a jikin ta kana tace "Bari na baka waje Baby, ina jiran ka da safe kenan? Amma ina fatan ya kasance daga yau kuma ba zaka sake fita ba se mun gama cin amarcin mu" ta fad'a tana jin kamar ta sake rungume shi dan dae kawae ta tuna maganar sa ne ta d'azu kamar be ji dad'i ba hakan ne ya sanya ta fasa yi d'in se kamo hannun sa da tayi cikin d'arr d'arr ta zuba masa wani kiss da har seda ya bada wani sauti "Muaahh" wato tayi shi cike da salo na jan hankali, se dae abinda bata sani ba shi kam ko a jikin sa, ya k'yale ta ne ma yanzun kawae dan kada ya zama mara adalci, amma daga shigar ta ta har abubuwan da take yi babu abinda ya ji shi cikin jikin sa, kwata kwata banda ma takaeci dake mak'ale a cikin ran sa. Cikin wani irin salo take takawa sanda zata fice daga d'akin tana wani karaeraya kamar zata 6alle, shi kam gogan naku bema san tana yi ba dan gaba d'aya hankalin sa yayi gaba wajen Ayrah ne. ... A 6angaren ta kuwa tunda ya fita da daren nan bayan ta gama kukan ta ta godewa Allah seta koma ta zauna tayi shiru zuciyar ta fall cike da tunani, seda ta d'an jima cikin d'akin sannan kuma ta fara jin wani irin tsoro na ratsa ta, a hankali take duban k'ofar d'akin se taga kamar wata inuwa ta gifta, da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda ilahirin jikin ta ke rawa, tunda take zata iya cewa bata ta6a kwana a waje ita d'aya ba, ta saba da jin motsin mutane kafin tayi bacci, se dae yau kwata kwata bata jin motsin komae shiru ne kawae ya ratsa ko'ina, haka kawae tayi ta tsarguwa, da dae ta gaji gaba d'aya se kawae ta koma kan gadon ta shige cikin blanket gaba d'ayan ta, tayi lamo tana jin wata k'walla na sakko mata, har lokacin bugun zuciyar ta be koma normal ba haka zalika tsoron be ragu ba, dae_dae kuma lokacin da er k'aramar wayar ta tayi k'ara, k'arar data sake rikita ta, take jikin ta ya cigaba da rawa kamar mazari zuciyar ta na cigaba da harbawa, seda ta soma nutsuwa sannan ta fahimci ringing d'in wayar ta ne, ta d'an lumshe idanun ta a hankali kana ta mik'a hannun ta har lokacin tana cikin bargon ta d'auka, ba tare data duba me kiran ba kawae ta d'aga wayar ba tace komae ba se sauke numfashi da take akae_akae kamar wadda tayi tsere "Auta!" ta jiyo muryar Yah Sadeeq, wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta kwa6e baki da murya tace "Yah Sadeeq.." duk da yanda yaji muryar ta amma be kawo komae ba saboda ya riga ya san halin Ayrah ciki da bae "Shine kika tafi babu ko sallama koh?" "Kae Yah Sadeeq, Abba ne fa yace wae mu tafi.." murmushi yayi kana yace "Toh shikenan Allah yayi miki albarka Auta, ya baku zaman lafiya, duk sanda na samu lokaci zan shigo mu gaesa dan har na fara missing naki" zuciyar ta ce ta sake karyewa amma dan gudun kada ta tayarwa da Yah Sadeeq d'in hankali ya sanya ta fad'in "Nima haka fa.." tayi maganar a sanyaye, babu laefi sun d'an jima suna hira a wayar, wadda ta kwashe kaso da yawa cikin damuwa da kuma tsoron da take ji kafin daga bisani suka yi sallama, zuwa lokacin dama ta fara jin bacci, dan haka cikin sauri ta k'ank'ame idanun ta ta rufe su ruff tana jiran d'aukar baccin. Barcin daya d'auke ta dududu befi na awanni 2 ba, data fara baccin seta firgita ta tashi, dan haka tun kafin asuba ta mik'e zaune, zuwa lokacin tsoron nata ya d'an soma raguwa kawae seta fad'a toilet tayi wanka sannan ta fito ta tayar da sallah, bata tashi daga kan daddumar ba se wajen k'arfe 8 kana ta mik'e ta koma kan gadon zuciyar ta a matuk'ar karye, idanun ta sun cika taff da hawaye.. Wajen

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70