Chapter 37
Chapter 37
ya bud'e wajen me zaman banza ya shiga ya kalle shi cike da girmamawa yace "Yalla6ae daka bari dae ko zuwa goben ne kada su fahimci wani abun!" wani kallo Alhajin ya jefa masa se kuma yayi murmushi wanda ya sake k'ank'antar da jajayen idanun sa "Tunda kaga zan yi driving da kae na kasan abu ne me muhimmanci, na kasa jurewa gwara naje ko nan sati 1 ne a d'aura mana aure idan yaso seta cigaba da karatun a cikin gida na" jin maganar da Alhajin ya fad'a ne ya sanya Muttala jinjina kae kawae, bece komae ba har zuwa sanda Alhajin ya tayar da motar sa suka fice daga gidan. A k'ofar gidan yayi parking motar ta sa, sannan ya kashe ta ya kalli Muttala da tunda suka fara tafiya har yanzu be sake cewa komae ba yace "Yi mana sallama da shi pls" seya kalli Alhajin sannan yace bayan ya girgiza kae "A'ah fa Yalla6ae kada ka manta sirikin ka ne, ina ganin gwara ka fito ko kan dakalin can ne seka zauna" Muttala ya fad'a yana nuna wani dakali dake a k'ofar gidan dake kusa da nasu Ayrah, shiru Alhajin yayi kamar ba zece komae ba se kuma can yace "Toh yanzu kae dae je ka" yayi maganar yana sanya hannun sa ya bud'e k'ofar, kusan a tare suka fito, Alhajin ya kalli wajen yana yamutsa fuska sannan ya zauna yayin da Muttala ya tsaya k'ofar gidan ya k'wala sallama, daga can cikin gidan Abba ya amsa yana mik'ewa ya zura takalmin sa ya fito daga d'akin nasa, k'arasowa yayi yana kallan Muttala ganin da yayi be shaida fuskar ba, se dae ya mik'a masa hannu suka gaesa sannan yace da d'an murmushi kan fuskar sa duk da yanayin da yake ciki a yau d'in na damuwa "Se dae ban shaeda fuskar ba" murmushi shima Muttalan yayi sannan yace "Ehh dama baka sanni ba gaskiya, ga can wanda yazo wajen ka akan wata magana me muhimmanci" yayi maganar yana nuna Alhajin dake zaune kan dakalin yana kallan wani wajen, saboda k'arancin hasken dake a wajen ya sanya Abba be iya hangar fuskar sa ba, seya dawo da duban sa ga Muttala yace "Toh ikon Allah" ya fad'a yana yin gaba zuwa wajen da Alhajin ke zaune, dae_dae lokacin da Abban ke dab da k'arasawa wajen Alhajin haske ya kawo a wani k'wan lantarki dake k'ofar gidan dake kallan nasu, hakan ne ya bawa Abba damar ganin fuskar mutumin da akace shi ke son magana dashi, cikin son sake tabbatarwa ya sake bud'e idanun sa dan ganin da gaske fuskar da yake gani ita d'in ce ko kuwa dae? Shi kan sa Alhajin kallan Abba yake with shock all over his face, se yaji gaba d'aya jikin sa ya d'auki wani mahaukacin rawa, ya had'iyi wani yawu da k'yar sannan yace bayan ya mik'a masa hannu "Kae ne mahaefin Ayrah?" Alhajin ya fad'a yana kallan Abba, a ran sa yana tuna cikakken sunan Ayrahn, tabbas da gaske shine mahaefin ta, amma dae gwara ya tabbatar ta hanyar ji daga bakin Abban, da mamaki Abba ke kallan sa jin maganar da yayi, meya kawo zancen Ayrah a tsakanin su kuma? "Meya kawo ka k'ofar gida na?" Abba ya fad'a yana kallan sa fuskar sa a d'inke tsaff, jikin sa ya sake wani sanyi wata zufa na karyo masa yace bayan yayi k'asa da muryar sa "Kayi hak'uri mu zauna sena maka bayani, wallahi ba tashin hankali ne ya kawo ni wajen ka ba" "Alhaji Mato!" Abba ya fad'a cikin er d'aga murya, a ran sa Abba na sak'a lallae duk abinda Alhaji Maton yazo da shi me girma ne "Bani da lokacin 6atawa, idan ba kada abin fad'a na shige gida" Wani yawun Alhaji Mato ya sake had'iyewa shi kan sa yana tunanin ta ina ma ze fara sanarwa da Abban son er sa yake? So na aure, ganin dae da gaske Abban yake idan bece wani abu ba ze iya tafiya ya k'yale shi ya sanya shi fad'in "Wallahi abin alkhaeri ne ya kawo ni, d'iyar ka na gani kuma ina son ta da aure shine kawae abinda ya kawo ni, kuma kada ka damu wancan lokacin akasi aka samu na fad'i magana saboda 6acin rae amma zan dawo maka da kud'in daka biya ni, kuma zan baka sana'ar da zaka dinga yi kana.... " "Dakata Alhaji Mato" Abba ya fad'a bayan ya d'aga masa hannu, zuciyar sa na wani irin zafi da jin kalaman Alhaji Maton na son zuciya "Kada na sake ganin k'afar ka a k'ofar gidan nan, kud'i kuma har abada na riga na biya ka kuma bazan ta6a kar6a ba, saboda haka kada ka sake tunanin zan d'auki 'ya ta in baka ita bayan na san wanene kae, ka cire wannan ma a cikin ran ka" daga haka Abba ya juya yana jin wani jiri jiri na d'ibar sa kamar ze fad'i, da kallo Alhaji Mato ya bishi zuciyar sa na wani irin tafasa, lallae yau ya kuma yadda Abban matsiyaci ne, be san me ake kira da arzik'i ba, har yanzu dae yana zaune cikin duhun kae, har abada ma baya tunanin Abban nada rabon arzik'i a rayuwar sa, tunda gashi yanzu arzik'in ya biyo shi har gida amma ya saka k'afa yayi fatali dashi saboda wani banzan ra'ayin sa na rik'au. Seda Abba ya shiga gida sannan Muttala ya kalli Alhaji Mato cikin mamaki yace "Yalla6ae wae dama ka san shi ne?" "Bar shashasha me k'ashin tsiya, arzik'i na kiran sa yana guduwa, wani k'aramin abu ne ya ta6a shiga tsakanin mu amma da yake zuciya ce dashi irin ta kafirae ya kasa mantawa, toh se yayi tayi ae, ba dae er sa bace na gani ina so kuma sena aure ta, dan kuwa ban ta6a ganin abu inaso ban same shi ba, kuma baza a fara akan ta er talakawa ma da ita ba, ko da amincewar sa ko babu wallahi sena aure ta.. Wuce muje.." ya fad'a yana huci sanda ya k'arasa ya bud'e motar sa ya shige, Muttala ma ya shiga, Alhaji Mato yaja motar da wani irin gudu kamar ze tashi sama. .. Akan la66an sa kawae Abba yayi sallamar dan baya jin ze iya d'aga murya sosae saboda yadda yake jin jikin sa, da kallo Umma ta bishi dashi sanda yake shigowa cikin d'akin, seta mik'e da sauri cikin mamakin yadda taga yanayin nasa ya sake chanjawa fiye da d'azun "Abban su" shine abinda ta iya furtawa tana cigaba da kallan sa, Abba ya nemi waje ya zauna amma har lokacin bece komae ba, fita Umma tayi ta d'ebo ruwa me sanyi cikin randa sannan ta koma d'akin ta mik'a masa a nutse tace "Gashi" babu musu Abban ya kar6a kofin ya sha ruwan sosae sannan ya ajiye shi yana sauke ajiyar zuciya "Don Allah ka dena d'aga hankalin ka haka nan, in dae akan wannan maganar ne nayi mata bayanin dalilin ka na hana ta auren sa" girgiza kae Abba yayi sannan yace bayan yayi murmushi me ciwo "Ba wannan kad'ae ba, yanzu fitar da nayi wae neman auren Ayrah akazo yi" "Ikon Allah.. Amma shine ka shiga damuwa haka?" Umma ta fad'a tana sake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70