Chapter 34
Chapter 34
sannan tayi wucewar ta kan gadon ta, dukan su suka bita da kallo kafin Ruks ta jinjina kae tana ta6e baki cike da mamakin halin Ayrahn "Cha66 d'i jam!" Jidda ta fad'a tana cigaba da kallan Ayrah. Ta 6angaren Ayrah kuwa ba ta bi ta kan kowa ba ta zura hijab ta shige toilet, kamar wasu sokaye suka sake bin ta da kallo, yarinyar ta chanja musu sosae, duk da dama tun can sun fahimci miskila ce ta k'in k'arawa, amma yanzu abin yayi gaba sosae, dole su jira Abeeda dan su tabbatar da abinda ta fad'a musu, duk da abin ne akwae wuyar yadda. ... Babu nisa su Ayrah suka yi last paper d'in su ya zamana se komawa gida kenan. A 6angaren Abba kuwa se Allah ya taemake shi lokacin da ze je d'auko Ayrahn ya kar6i albashin sa, dan haka ba k'aramin dad'i yaji ba. Ranar daze tafi ya gama shiryawa cikin manyan kaya na wani yadi, daga d'aki ya fito lokacin Umma na d'akin Yah Sadeeq ta kae masa abinci, ta kalle shi tana murmushi tace "An fito kenan?" shima murmushin ya maeda mata sannan yace "Wallahi kuwa zamu wuce" yayi maganar yana d'ora hular sa samfurin zanna bukar akan sa "Toh Allah ya tsare.." "Ameen Ameen.. amma kafin nan zan biya nayi wa Baban Zaenab ya me jiki, saboda jinjirar da aka haefa masa da aka sallamo su daga asibiti" "Toh ayi mata sannu, gobe idan Allah ya kaemu se mu shiga mu duba ta" "Toh madallah" Abba ya fad'a yana yin gaba, seda ya shiga d'akin Yah Sadeeq dake zaune akan gadon sa yana danna er k'aramar wayar sa, Abba yace "Sadeeq!" "Na'am Abba zaka wuce ne?" "Ehh ba kaci abincin ba" d'an murmushi kad'an yayi sannan yace "A'ah yanzun dae zan ci, Allah ya dawo daku lafiya Abba" "Ameen_Ameen" Abban ya fad'a yana mik'ewa ya fice daga d'akin. Kae tsaye seda ya fara zuwa ya gaeda mara lafiyar sannan ya dawo ta hanyar gidan sa dan wucewa titi ya nemi abin hawa, a k'ofar gidan nasu yaga wata mota me kyau, tunda suka gan shi suka sauke glass d'in motar, wani malamin su Ayrah ya sauko ya k'arasa da murmushi kan fuskar sa yace "Barka da wannan lokacin Alhaji" yayi maganar yana mik'awa Abba hannu, shima Abban mik'a masa hannu yayi suka gaesa yana amsawa da "Barka dae, ashe kae ne?" "Wallahi kuwa, ina zuwa haka ne?" Abba yace "Zan je d'auko Ayrah ne kasan da yake sun gama exam" murmushi malamin nasu yayi sannan yace "Ahh toh ae dama daga makarantar ne aka aeko mu muzo mu d'auke ka a motar nan mu wuce can makarantar" "Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana bin motar da kallo, dan sosae abin ya cigaba da bashi mamaki, tabbas makarantar tasu Ayrah mutane ne masu karamci da sanin ya kamata "Allah ya saka da alkhaeri" Abba ya fad'a "Ameen Ameen.. Muje koh?" ya fad'a yana yin gaba sannan Abba ya rufa masa baya zuwa wajen motar, shi malamin ya shiga gaba yayin da Abba ya shiga baya, a haka driver ya soma driving babu dad'ewa suka d'auki hanyar Zaria. ... Ayrah ta gama had'a komae nata ta kammale shi inda ya kamata, wani irin d'oki ne keta d'awaeniya da ita, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta gan ta a Kano taga Abban ta, Umman ta da uwa uba kuma Yah Sadeeq d'in ta, gaba d'aya ta kasa sukuni tun d'azun wayar ta ke hannun ta tana jiran kiran Yah Sadeeq ko Abba, Jidda ce kawae a d'akin tun d'azu su Bahijja suka fita ko sallama ba suyi ba, bata k'ara minti 5 ba kuwa sega kiran Abba a wayar ta ta, zumbur ta mik'e dan dama k'iris take jira ta d'aga wayar tana karawa a kunnen ta "Abba kunzo?" ta fad'a tun kafin Abban yace komae, murmushi Abba yayi kana yace "Qwarae kuwa ke muke jira yanzu haka" jin da tayi yace suke ya sanya ta tunanin tabbas shi da Yah Sadeeq suka zo dan haka da sauri ta kalli Jidda tace "Mu dae mun tafi" ta fad'a tana Allah Allah Jidda ta amsa ta fice daga d'akin "Ba zaki tsaya kiyi sallama dasu Ruks ba?" 6ata fuska tayi sannan tace bayan ta girgiza kae "A'ah ki fad'a musu na tafi ni dae, se an dawo hutu bye.." ta fad'a tana ficewa daga d'akin "Toh Allah ya kaemu" shine abinda Jidda ta fad'a tana bin Ayrah da kallo sanda ta fice daga d'akin cikin d'oki kae seka rantse tafi shekara ba taga Abban ba. Sosae taji dad'in ganin Abban dan murna gaba d'aya ta kasa dena murmushi se dae tayi mamakin rashin ganin Yah Sadeeq tare da Abban, dan haka ta kasa shiru seda tace "Abba Yah Sadeeq fa?" "Yah Sadeeq na gida, kin san yanayin aekin su hutu yake shiyasa.." se tayi murmushi, a yanzu da taga Abba se d'okin nata kuma ya koma na son ganin Yah Sadeeq da Umma, suna tafiya a hanya suna hira sosae cike da farin ciki da kewar juna, Abban ya zage yana jan d'iyar ta sa da hira, se dae da yake basu kad'ae ne a cikin motar ba ya sanya yawanci hirar tasu bata wuce akan karatu. ... Da wani sauri Bahijja ta turo k'ofar d'akin hannun ta d'auke da wayar Abeeda, Abeeda da Ruks suka biyo bayan ta, idanun ta a warwaje ta furta "Ina Ayrah take?" tayi maganar cikin d'aga murya, da mamaki Jidda ke kallan ta yadda take a wani birkice kamar mahaukaciya tace "Meya faru?" "Ke dae ina take kawae?" "Yanzun nan aka zo aka d'auke ta" Jidda ta fad'a sannan ta d'ora da "Pls meya faru?" komawa Bahijja tayi ta zauna, tana tuna yau da taga Ayrah a cikin d'akin nan babu abinda ze hana ta shak'e ta ko zata ji sauk'in abinda take ji a cikin zuciyar ta, kar6ar wayar hannun ta Ruks tayi sannan ta mik'awa Jidda tace "Kalla ki gani" hannu Jidda ta saka ta kar6i wayar sannan ta shiga kallan hoton sannu a hankali, tana kae hannun ta tana zooming, ta kae wajen minti 1 tana kallan hoton sannan ta d'ago ta kalle su cike da mamaki akan fuskar ta "Kenan abinda Abeeda ta fad'a gaskiya ne?" tayi tambayar tana kallan su su duka, kamar wata k'adangaruwa Bahijja ta shiga girgiza kae tana jin kamar ta rusa ihu "Shegiyar yarinya ta cuce mu, dama seda nayi tunanin kyawun ta ze iya rud'ar shi, ashe mu bamu sani ba ma sun dad'e suna soyayyar su amma shegiyar yarinya seta dinga nuna kamar ma tsanar sa tayi, bamu sani ba ashe wawaye sakarkaru ta maeda mu, k'aramar yarinya tayi wasa da tunanin mu kenan?" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kana tace "Lallae kam, ni kae na abin ya bani mamaki wallahi, yaushe muna zaune har hakan ta faru bamu sani ba? Ya akayi hakan?" tayi maganar cike da mamakin dae, girgiza kae Ruks tayi kafin tace "Wallahi ku bari kawae, ni dan mamaki ma na rasa wane tunani ya kamata nayi" Abeeda tace "Ahh toh, ni kae na nasan amanar ku akaci shiyasa naga bazan k'yale ba gwara na sanar daku" "Aekuwa wallahi za taci uwar ta yarinyar nan"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70