Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ta kau, yanzu se yaji da d'ayar data rage masa "Nagode sosae Abba.. Allah ya saka da alkhaeri.. Umma nagode" ya fad'a yana mik'ewa "Allah ya tsare" Umma ta furta da murmushi kan fuskar ta dan seta ke ji kamar little Raj ne wanda ta sani tun shekarun baya, d'aukar envelope d'in yayi a ran sa yana sak'a lallae akwae aeki a gaban sa, Yah Sadeeq ne ya mik'e ya taka masa zuwa k'ofar gidan, be baro wajen ba seda Rk d'in ya hau motar sa sannan ya juya, ya kasa hak'urin rashin ganin ta tun shigowar sa dan haka ya furta "Amm pls Yah Sadeeq bata nan ne?" juyowa Yah Sadeeq yayi kana ya d'an yi murmushi sannan yace "A'ah tana d'aki, ko a kira maka ita ne?" da sauri ya girgiza kae yana d'an lumshe idanun sa, duk da yanda idanun sa ke k'ishirwar ganin ta amma gwara ya hak'ura dan haka ya furta "A'ah barshi kawae nagode.." daga haka yaja motar sa ya bar layin yayin da shi kuma Yah Sadeeq ya koma cikin gida. Kallan Abba Umma tayi bayan fitar Rk d'in "Abban su yaya wannan auren ze kasance kenan?" d'an shiru Abba yayi sannan yace "Wannan ya rage nasa Ruk'ayya.." "Ina ganin kafin ta koma ko kae zakawa Baban nasa bayanin yanda auren ya kasance?" da sauri Abba ya kalli Umma cike da mamakin jin kalaman ta "Ruk'ayya kin san me kike cewa kuwa? Ashe har Kabeeru yayi arzik'in da zan je wajen sa yi masa bayanin wani abu? Bakya tunanin wani abu ze d'arsu a cikin ran sa?" ya k'are maganar yana girgiza kae sannan ya d'ora da "Bana fatan wannan ranar tazo.." se kuma a lokacin itama Umman ta fahimci hakan dan haka ta furta "Toh Allah ya kyauta, zamu iya bashi ita?" "K'warae babu damuwa.." Abba ya fad'a. A hankali Umma ta yaye labulen d'akin ta shiga, tana kwance akan gadon ta kamar me bacci, k'arasawa Umma tayi kan gadon tana fad'in "Ayrah wae bacci kike yi ne?" da zata iya shiru zata yi dan haka kawae take jin kunyar Umman tun zuwan Rk "A'ah Umma" ta fad'a har lokacin tana kwance "Toh tashi zamu yi magana.." Umma ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna, tashi zaune Ayrahn tayi tana had'e jikin ta kamar me jin sanyi "Meyasa kika k'i fitowa ko gaesawa kuyi?" tura d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Ummaaa.." taja k'arshen sunan, murmushi Umma tayi tana girgiza kae sannan tace "Ki bar damun kan ki, In Sha Allah in dae mu ne mun amince da auren ku, dan haka ki bar damun kan ki haka nan, Allah ya tabbatar da alkhaerin sa" hannun ta ta d'auka ta rufe fuskar ta tana murmushi, duk da har lokacin akwae d'an haushin sa kad'an da take ji amma yanzu da Umman tayi magana taji matuk'ar dad'i, seta d'ora kan ta akan cinyar Umman kawae ba tare da tace komae ba "Ayrah.." Umma ta fad'a tana murmushi.. ... Kwanakin da suka biyo baya amarya Muneerah ta cigaba da shirye_shiryen aure, yayin da 6angaren ango Raj yama manta da maganar auren musamman ma daya kasance shi kan sa Abbun ya fita a harkar sa saboda yadda ya lura sam auren baya gaban sa, dan haka hatta lefe Ummee ce ta saka aka had'a aka kae, be tashi sanin suna nan kan bakar su ba duk da yanda aka bashi katin d'aurin aure wanda tunda ya ajje su be sake bi ta kan su ba ballantana ko gayyata ce yayi, se ana i gobe d'aurin aure ya sake tabbatarwa sanda yaga gidan nasu ya fara cika da jama'a, haka zalika har lokacin be huta da sak'onni da kuma kiran wayar Muneerah ba, wanda gaba d'aya baya kulawa ita kuma kamar tsohuwar mayya bata hak'ura duk da yadda Mummyn ta tace tayi watsi da shi ze neme ta da kan shi amma ita ta kasa hak'uri, shi gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa ya ta'allak'a ne akan yanda ze sami Abbu suyi magana akan zancen Abba amma be san ta inda ze soma ba shi kan sa. .... Washe_gari, fitowar sa kenan daga wanka wayar sa dake ajje kan gado tayi k'ara, seya k'arasa da mamakin me kiran nasa ganin asuba ce "Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seda ya sake kallan agogon wayar dan sake tabbatar da lokacin da gaske ne ko dae shine yayi mistake, haka d'in ne dae dan haka kawae ya d'aga wayar yana karawa a kunnen sa "Raj!" "Na'am" ya fad'a muryar sa a d'an cunkushe "Ina fatan kana sane da d'aurin auren ka yau d'in nan koh?" Abbu ya fad'a shima ran sa a 6ace kuma babu fara'a dan yadda ya fahimci Rk d'in akwae rashin daraja a al'amarin sa kwana biyun, shiru na wajen second 30 sannan yace "Ehh.." daga haka Abbu ya katse wayar sa, gefen gadon ya nema ya zauna hannun sa dafe da kan sa yana jin yanda yake cigaba da sara masa, ga kuma bugu da k'irjin sa ke tayi kamar wanda yayi gudu, shi har yanzu ya rasa gane matsalar Abbu, Ummee, Daddy da kuma ita kan ta Muneerahn, shin ita bata da zuciya ne a k'irjin ta? Ya fad'a mata baya son ta baya son ta amma tak'i hak'ura, ya share ta ya share ta duk da haka tak'i hak'ura, toh ya suke so yayi da ran sa ne shi kam? Me zeyi da wata Muneerah a matsayin mata? Sam bata a gaban sa, kwata kwata yana ganin kamar za'a k'ware shi ne kuma itama a k'ware ta, amma tunda sun nace kuma sun dage bari ya bar su suyi auren duk abinda ya biyo baya kuma suyi kuka da kan su ba dae shi ba, tunda shi kam ya riga ya nuna musu baya ra'ayin ta ko kad'an. .. A cikin garin Kano aka d'aura auren Raj Kabeer da kuma Muneerah Abubakar, wanda saboda Abbu shine waliyyin amarya shi ya nemi da akawo auren Kano, shi kuma mahaefin ta bek'i hakan ba ya kawo shi nan d'in, daga lokacin da aka d'aura aure aka nemi ango aka rasa dama kuma da k'yar yazo wajen, seda Abbu ya masa tass sannan yazo wajen dan da farko cewa yayi ba zeje ba. Kae tsaye gida ya wuce ya sauya jamfa da wandon dake jikin sa da k'ananan kaya, fuskar nan kamar wanda akawa albishir da mutuwa, ya had'e ta tsaff kamar ze rufe wanda ya masa magana da duka, babu 6ata lokaci ya hau motar sa yaja be tsaya ko ina ba se gidan su Ayrah, dan yanzun ita kad'ae yake son gani ko ze samu sassaucin abinda yake ji a cikin zuciyar sa, a k'ofar gidan ya dakata ya lalubo number Yah Sadeeq sa suka yi exchanging ya kira, bugu 1_2 ya d'aga, a dak'ile ya furta "Pls.. Idan tana nan, ina waje zamu d'an gaesa ne.." "Ohk" Yah Sadeeq ya amsa yana ajje wayar, sannan ya k'arasa cikin d'akin Ayrah dake zaune ita da Umma yace "Umma Raj na k'ofar gida, wae zasu gaesa da Ayrah.." da sauri Ayrah ta d'aga kae ta kalli Yah Sadeeq se kuma ta sadda kan ta k'asa cike da kunya "Tohm shikenan" Umma

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70