Skip to content

Chapter 67

Chapter 67

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

ita kae tsaye ya wuce part d'in da yasan anan ze same ta. Bin parlourn yayi da kallo wanda shima an zuba kaya kamar babu gobe, be bi takan komae ba ya k'arasa bedroom, knocking ya fara yi bayan ya dakata, tana zaune kan gado sanye cikin lifaya, tun d'azu dama ta k'agu yazo hak'uri kawae take yi, dan haka tana da tabbacin shine "A bud'e take" ta fad'a bayan ta bud'e fuskar ta dake rufe, wadda itace ta fara rufe ta se taga ba zata iya ba kawae ta bud'e ta, kallan sa tayi sanda ya shigo cikin d'akin tana jin wani irin farin ciki musamman idan ta tuna yau d'in ta mallake shi bayan duk wannan gwagwarmayar da ta sha. A nutse ya k'araso cikin d'akin har lokacin be kalli inda take ba, seda ya ajje ledar sannan ya nemi gefen k'aramar kujerar dake cikin d'akin, wajen minti 1 bece komae ba, ita kuma ji take kamar ta tashi ta rungume shi dan dae ta tuna fad'an da tasha a wajen Aunties d'in ta ne da babu abinda ze hanata aekata hakan, shiyasa yanzun ma kamar yadda suka umarce ta tayi shiru tana saurarar sa "Kina lafiya?" ya fad'a bayan ya daddanne zuciyar sa, murmushi ta saki jin tambayar tasa me nuni da kulawa ga wanda ake tambaya, hakan ne ya sanya ta karyar da kae sannan tace "Lafiya k'alau Baby, se dae gajiyar biki kuma!" "Ga abinci nan idan kina buk'ata, akwae komae a kitchen shima in kina buk'ata, bayan nan akwae wani abun da kike buk'ata?" ba tare da tunanin komae ba tace "A'ah Baby.." "Ohk" ya fad'a yana mik'ewa a nutse ya fice daga d'akin. Bin sa tayi da kallo sannan ta kalli ledar daya shigo da ita, wani murmushi ya su6uce mata data tuna yau d'in ita da Rk zasu zama abu d'aya. Tana zaune kan gadon ta cigaba da jiran shigowar sa, har wajen minti 30, awa 1, bata sare ba har lokacin, se dae gajiyar zaman da tayi, da kuma wannan shegiyar lifayar dake jikin ta, dan haka kawae ta sauko daga kan gadon ta ware lifayar gaba d'aya ta jefa ta gefe sannan ta koma ta zauna tana cigaba da jiran sa, tun tana cigaba da saka ran shigowar sa har ta sare, a lokacin ne kuma ta fara tunanin ko dae ta bishi d'akin na sa? Maganar Aunties d'in nata suka sake dawo da ita hayyacin ta seta koma tayi zaman da6aro kan gadon tana jin kamar ta rusa ihu, ita kam da sun bar ta da yanzun bin sa d'akin nasa za tayi ita babu abinda ya dame ta, basu san halin Rk bane, ita data san shi ita ta san shi, tun tana kokawa da baccin da ke ta kawo mata hari har ta bada kae bori ya hau kawae ta shiga sharara baccin ta. .. Shi kuwa 6angaren sa yana komawa d'aki wanka kawae yayi ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya sannan yabi lafiyar gado, gaba d'aya tunanin sa da hankalin sa na kan Ayrah ne daya baro ita kad'ae cikin d'akin, dan ma dae daga waje ya kulle ta ne in case, saboda akwae komae na buk'ata a cikin d'akin, a hankali ya lumshe idanun sa zuciyar sa fall da tunanin Ayrahn barkatae. Muneerah kuwa ba ita ta farka ba se wajen k'arfe 8 na safe, da sauri ta mik'e mamaki ya sake kamata ganin har lokacin babu shi cikin d'akin, kae tsaye wanka ta fad'a tayi sannan ta fito tayi Sallahr asuba, dan dama tun a gida ta riga ta saba bata tashi Sallahr asuba se 8 wani lokacin ma har fin 8 d'in ma, duk da kasancewar safiya ce hakan be hana ta d'aukar nighties ta saka ba, wata shu'umar riga ce irin me net d'in nan kuma me bin jiki, gaba d'aya undies d'in ta ana ganin su saboda yanda rigar take me raga raga kamar gidan sauro kuma dududu da kad'an ta wuce gwuiwa, seda ta sake gyara fuskar ta sannan ta fito daga d'akin zuwa part d'in sa. Tura k'ofar tayi cikin sa'a ta jita a bud'e seta k'arasa fuskar ta d'auke da murmushi ta tura kan ta cikin d'akin, wani sassanyan k'amshi ne ya ziyarci hancin ta wanda ya tilasta mata lumshe k'ananun idanun ta kana ta cigaba da tafiya bayan ta chanja tafiya ta d'an soma jijjiga jikin ta da yanzun babu laefi akwae su saboda uban magungunan data dinga d'irkawa cikin ta. Fitowar sa kenan daga wanka d'aure da madaedaecin towel, hannun sa rik'e da comb yana taje sumar kan sa ta tura k'ofar d'akin, idanun ta suka sauka akan bayan sa da take iya hange, wata k'atuwar ajiyar zuciya ta sauke saboda yanda taji gaba d'aya jikin ta ya amsa da ganin sa da tayi a haka, dan kuwa tunda take bata ta6a ganin sa a haka ba, da sauri ya juyo dan be ta6a tunanin rashin kunyar ta ta zata bar ta ta shigo d'akin sa washe garin ranar da aka kawo ta ba, amma ga mamakin sa se yaga ita d'in ce, ajje comb d'in hannun sa yayi bayan ya d'auke idanun sa daga kan ta sanda ta sakar masa wani tattausan murmushi, sosae k'irar jikin sa ta tafi da imanin ta, a yau da take ganin faffad'an k'irjin sa a bud'e dake d'auke da wasu kwantattun bak'ak'en gashi masu kyawun gani, kawae seta k'arasa ba tayi wata wata ba ta rungume shi ta baya tana sakin ajiyar zuciya, tsaki ya saki cikin ran sa wani 6acin ran na taso masa, se yayi k'ok'arin danne shi kada 6acin rae yasa yayi abinda be kamata ba "Baby meyasa jiya daga fitar ka baka dawo ba? Nayi kewar ka Baby sosae, na d'auka za muyi spending night d'in mu ne cikin farin ciki, at least dae ka taya ni farin cikin wannan ranar dana dad'e ina jira" iska ya fesar daga bakin sa kafin ya d'an kautar da kan sa ya shak'i iska dan abinda ke tashi daga jikin ta sam be masa ba, dan in dae ba hancin sa ke masa k'arya ba wani d'an k'arni k'arni yaji tana yi, abinda dae be sani ba shine itace keyi ko kuma turare ta saka me k'arni haka? Me tayar da zuciya!? hakan ba mamaki bane dan kuwa bleaching d'in da take yi shahararre ne, tayi d'au da ita, kae seka rantse dama can farar ce ba bak'a ba, hannu d'aya ya saka duk da yadda yaji tsigar jikin sa na wani irin tashi ya janye ta daga jikin sa kana ya matsa gefe ya d'auki wata tattausar brown d'in jallabiyya ya d'ora akan towel d'in sannan ya zame shi ta k'asa, seta kalle shi duk da yadda ta d'an ji babu dad'i amma hakan be hanata furta "Haba Baby ka bari mana inji d'umin jikin ka don Allah" da sauri ya d'aga idanun sa ya kalle ta cike da mamakin kalaman bakin ta, se kuma ya d'auke yana neman kan gadon ya zauna ya d'an kishingid'a da pillown dake kan gadon sannan ya furta har lokacin idanun sa a lumshe "Ina kwana?" bak'in bakin ta ta tura gaba sannan tace "Kae Baby, toh lafiya k'alau.." ta

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70