Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kae Umma tayi "Toh shikenan, kukan ya isa haka Uhmm?" ta fad'a tana kuma shafa bayan ta, cigaba tayi da sheshshek'ar ta har zuwa sanda ta gaji tayi shiru a jikin Umman... Wajen k'arfe 7pm na daren ranar Umma ta shiga d'akin Abba, seta tarar dashi zaune kan gadon, a hankali ta k'arasa ta zauna tana kallan sa tace cikin nutsuwa "Abban su lafiya kuwa?" d'an gyara zama yayi sannan yace "Haka nan kawae nake jin kamar ba lafiya ba, ina tunanin zan koma in bincika dan har yanzu layin sa baya shiga, kuma yaci ace yanzun dae ya iso cikin garin nan" cikin kwantar da murya kuma dan ta k'ara bawa Abban k'warin gwuiwa ya sanya ta fad'in "In Sha Allah yana lafiya, lafiyar ce kuma ta 6oye shi.." "Allah yasa" Abba ya fad'a. Tun Abba na kiran layin Abbu har ya gaji ya hak'ura ya cigaba da addu'ar Allah yasa Abbun yana lafiya, duk kuma yabi ya takurawa kansa yana ganin kamar duk abinda ya samu Abbun shine sila, haka dae Umma ta dinga bashi baki akan ya kwantar da hankalin sa amma har zuwa dare babu kiran Abbu.. Washe gari Abba ya kasa sukuni dan haka tunda yayi sallahr Asuba ya shirya cikin wani yadi me kyau ya kalli Umma dake kallan sa "Har yanzu hankali na ya kasa kwanciya Ruk'ayya, gwara naje na duba da kae na" jinjina kae Umma tayi dan itama yanzun ta fara d'an shiga cikin tsoro gwara Abban ya duba ko lafiyar ce ta 6oye Abbu, amma dan ta sake kwantar masa da hankali tunda tafiya zeyi ya sanya ta fad'in "Hakan ma yayi Abban su, Allah ya tsare hanya..amma yadda nake ta tunani dae babu mamaki motar da zata zo zuwa Kano ne be samu ba shiyasa ya bari se yau ina ga" murmurshi Abba yayi kafin yace "Toh banda abun Kabeeru ae ya kira ni ya fad'a min ko dan kada hankalin mu ya tashi dukan mu" "Hakane Abban su, In Sha Allah lafiyar ce ma" "I hope so" Abba ya fad'a sanda yake d'aura agogon hannun sa. Sanda ya fito daga d'akin yayi dae dae da lokacin da Ayrah ke fad'in daga toilet d'in tsakar gida "Umma na gama" k'arasawa Umma tayi zuwa cikin toilet d'in ta yiwa Ayrahn tsarkin fitsarin da tayi sannan suka fito tare, da gudu ta isa wajen Abba tace hannun ta rik'e da nashi "Abba don Allah zan bi ka" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Tohm shikenan bari naje na dawo zan taho miki da tsaraba" d'aga idanun ta tayi ta kalli Abban tana murmurshi tace "Abba ni kad'ae ni da Raj zaka siyowa banda Yah Sadeeq koh?" shima murmurshin yayi sannan yace "Ehh.." seta saki Abban tana shirin shiga d'aki tace "Abba ada lafiya" kallan Umma yayi bayan ya amsa addu'ar Ayrahn yace "Ina tunanin zan d'akko Raj in had'a su da Sadeeq su cigaba da karatun su anan ko ya kika gani?" jinjina kae Umma tayi cikin na'am da zancen Abban sannan tace tana murmurshi "Hakan yayi Abban su, Allah ya k'ara taemaka maka, in dae hakan yayi maka nima ya min" "Toh gaskiya hakan ya min, ina tunanin zamu dawo ne tare da Raj yau d'in nan" "Toh Allah ya tsare" Umma ta fad'a.... K'arfe 2 Abba ya sauka a unguwar su Raj bayan ya sake trying number Abbu a kashe, ya sauka daga adaedaetar data kawo shi dan be kae ga d'akko motar sa ba, da k'afar sa ya k'arasa cikin layin cikin nutsuwa, tun daga nesa yake hango gidan kamar da kwad'o a jiki, amma be gasgata hakan ba seda ya k'arasa bakin gidan ya tsaya, kwad'on ne kuwa a jiki, mamaki ya sake kamashi kawae ya tsaya cikin rashin sanin abinyi, ya kae wajen minti 5 tsaye a wajen lokacin ya sake gwada kiran number Abbu har kusan sau 5, sega wani mak'ocin su Abbun yazo wucewa, ya kalli Abba dake kallan wayar sa yace "Salamu Alaekum" ya fad'a yana mik'awa Abba hannu, d'agowa Abba yayi yana kallan mutumin seya mik'a masa hannu suka yi musabaha sannan mutumin yace "Malam Kabeeru kake nema ne?" murmurshi Abba yayi yana jin In Sha Allah mutumin yasan inda yake sannan yace "Wallahi kuwa, tun jiya nake gwada kiran layin sa amma ban same shi ba, gashi kuma nazo gidan a kulle" "Ikon Allah" mutumin ya fad'a yana jinjina kae, jin abinda ya fad'a ne ya sanya Abba sake kallan sa sanda yake fad'in "Aekuwa da alama kunyi sa6ani dan kuwa jiya jiyan nan kafin azahar nazo na same shi suna had'a kaya shi da matar tasa a cikin wata mota, har nake tambayar sa dalilin tafiyar tasa haka babu sanarwa shine yake shaeda min tafiyar gaggawa ce ta kama shi da iyalan nasa shiyasa basu sanarwa da kowa ba amma muyi hak'uri zasu bar garin ne gaba d'aya" da sauri Abba ya sake kallan mutumin yana mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin mutumin, cikin watsi da kuma kokawa da abinda ya fara zuwar masa k'wak'walwa da zuciya yace "Anya kuwa? Magana nake fa akan Kabeeru.." "Shi dae Malam Kabeeru baban Suraj, ni kae na nayi mamakin tafiyar tasu kamar wad'anda ake kora, babu wanda suka yi sallama da su se wad'anda suka gansu sanda suke k'ok'arin barin layin nan, kuma har yanzu maganar da nake maka bamu san takamaemae dalilin barin su garin nan ba" "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shine kawae abinda Abba ke maemaetawa a cikin zuciyar sa, yayin da mutumin ya kalle shi cikin mamakin ganin yadda Abban yayi shiru bece komae ba amma gaba d'aya yanayin sa ya nuna yana cikin tashin hankali, d'an baya kad'an Abban yayi zuciyar sa na wani irin bugawa da k'arfin gaske "Subhanallahi" mutumin ya fad'a yana rik'o Abban, da sauri Abba ya nemi waje ya zauna dan yadda yaji kansa na wani irin juya masa ga wani jiri da lokaci d'aya ya nemi ya kayar dashi "Lafiya dae koh?" mutumin ya fad'a yana nazarin yanayin Abban, cikin k'arfin hali Abba ya furta "Lafiya k'alau, Nagode" "Babu damuwa" mutumin ya fad'a yana yin gaba. Seda Abba ya k'ara wajen minti 20 a wajen sannan ya mik'e zuciyar sa a cunkushe, yama rasa meya kamata yayi tunani, anya kuwa da gaske Kabeerun guduwa yayi masa da kud'i da takaddun sa masu muhimmaci? Anya kuwa ya kamata ya yadda da wannan maganar? Yana so ta k'aryata hakan se dae kuma duk wasu alamu dake nuna Abbun guduwa yayi sun bayyana "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" ya sake maemaetawa sanda ya ida fitowa titi, sam bashi da k'arfin gwuiwar yin tuk'i dan haka bebi takan fire service da yake ajje motar sa ba ya tari mota wadda zata kae shi tasha ya hau motar Kano.. Ko a cikin motar ma gaba d'aya zuciya da k'wak'walwar sa sun kasa sukuni, so yake ya gane cewa mafarki ya yi ba gaskiya bane ace Kabeeru wae ya gudar masa da dukiyar daya dad'e yana tarawa wata da watanni, takaddun karatun sa daya dad'e yana yi shekara da shekaru, anya kuwa ba'a chanja Kabeerun ba, Kabeeru mutum me kirki mutunci da kawaeci, rik'on amanar da shine ya zamo abinda ya birge Abban har ya koma yana masa

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70