Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

me k'arfin gaske cikin kukan tana fad'in "Yah Sadeeq Raj, Yah Sadeeq Raj" be bi ta kanta ba se kwantar da kan nata da yayi a kan kafad'ar sa amma tak'i kwanciya ta cigaba da kukan ta kamar ranta ze fita, a haka yayi gaba. Lumshe idanun sa yayi sanda Ummeen sa ta d'ora hannun ta akan kafad'ar sa, yana jin wasu k'walla na tarar masa a cikin idanun sa, Ummee tace "Kada kayi kuka fa" kamar ma zuga shi tayi se kuwa hawayen suka cigaba da zuba yana saka hannu yana goge su, Umma data mik'e tace "Toh bari mu tafi" "Allah ya tsare Hajiya.." Inji Ummee "Ameen" Umma ta fad'a tana yin gaba... Tunda suke tafiya kukan take yi tana cigaba da ambatar sunan Raj, se rarrashin ta Yah Sadeeq keyi amma tayi kamar bata san yana yi ba, ta cigaba da rera kukan ta tana yi tana sauke ajiyar zuciya, seda suka kusa isa tasha sannan bacci yayi awon gaba da ita a kafad'ar Yah Sadeeq... Motar da zata kaesu Kano direct ita suka samu tana shirin tashi mutane 2 kawae ake jira ta tashi, ganin su Abba ya sanya su dakatawa kwandasta ya kalli Abba yana tambayar inda zeje, Abban ya fad'a masa sannan ya bud'e musu motar, Umma ce ta fara shiga sannan Yah Sadeeq daya zauna a maleji, kana Abba ya kalli wajen da yayi ragowa sannan ya kalli Abbu dake tsaye rik'e da kayan Abban yace bayan ya kalli kwandastan "Ae mu 2 ne kuma naga saura wajen mutum 1" kwandastan ya kalli Abba kana yace "Shawara idan zaka d'auka ku raba motar, idan yaso wasu su tafi yanzu wasu kuma idan wata za taje kanon seta d'auke su" Take Abba yayi na'am da shawarar ya kalli Abbu yace "Ko mu barsu su tafi, mu kuma ma taho?" Abbu yace "Alhaji kar a samu matsala tunda kaga basu ta6a zuwa kano ba se wannan karon.." "Hakane kuma" Abba ya fad'a yana tunanin mafita "Meze hana kuyi gaba ni sena taho daga baya?" Abbu ya katsewa Abban tunanin da yake, Abba ya d'aga kae ya kalle shi kana yace "Babu matsala?" "A'ah babu matsala" Abbu ya fad'a yana murmurshi, mik'a hannu Abba yayi da niyyar kar6ar kayan hannun Abbu, kwandastan yace "Yalla6ae cikin wajen nan wallahi babu wajen da zaka ajiye jakar nan, ko a jikin ka zaka rik'e zaka takura ne kuma ka takurawa mutane" Abba baya son dogon zance dan haka yace "Bud'e min bayan motar na saka to" "Ae da mutane a ciki" sauke numfashi Abba yayi yana tunanin meya kamata yayi yanzun, seya tsinto muryar Abbu na fad'in "Toh Alhaji kona taho maka dasu?" kallan Abbun Abba yayi sannan yayi murmurshi yace "Toh shikenan, yanzu zaka jira zuwan wata ne?" "Ehh In Sha Allah Alhaji, Allah ya tsare.." Abbu ya fad'a "Ameen Ameen, Allah ya tsare dukkan mu" "Alhaji lokaci fa na tafiya" kwandastan ya fad'a yana kallan Abba, kallan Abbu Abba ya sake yi sannan yayi murmurshi ya koma ya shiga cikin motar sannan kwandastan ma ya shiga, Abbu ya sake yi musu addu'a sanda drivern motar ke k'ok'arin tashin ta, be bar inda yake tsaye ba seda motar tasu ta tashi. Tafiyar awanni suka yi suka isa garin na Kano zuwa lokacin Ayrah ta tashi daga bacci ta cigaba da kukan ta, tayi kukan harta gaji ta hak'ura se ajiyar zuciya da take ta saukewa daga k'arshe wani baccin ya sake d'auke ta a jikin Yah Sadeeq dan shi kad'ae ne ze iya rik'e ta saboda yadda su Umman suke a matse a inda suke zaune, se a lokacin Abba yayi dana sanin k'in tahowa da motar sa, daya sani ya kae ta gyara saboda matsalolin da take bashi a kwanakin nan, ganin tafiyar tasu me nisa ce ya sanya be taho da ita ba ko dan gudun matsala.... Sanda suka isa Kanon kae tsaye gidan da Alhaji Maton ya nemar musu suka isa, su Umma ne suka fara shigewa cikin gidan ita da Yah Sadeeq yayin da Abba ya tsaya ya lalubo wayar sa dan tuntu6ar Abbu yaji ko shima ya taho d'in dan yana ganin kamar wannan d'in nauyin sa, yana so kuma ya sanar dashi idan be samu motar ba ya bari se gobe kada yamma tayi masa a hanya, kiran farko da yayi ta shiga ta soma ringing, se dae har kiran ya katse ba'a d'auka ba, hakan ne yasa Abban ya sake kiran layin se dae ga mamakin sa se suke fad'a masa wayar tana a kashe ne, ya riga ya yaddarwa zuciyar sa matsalar network ne tunda a yanzu yayi kira na farko ta shiga yanzu kuma a kashe dan haka ya sake trying number sedae abinda yanzu kuma take fad'a masa shine kwata kwata ma ba zata shiga ba....... *Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)* https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page_006 ___Sosae tsoro ya kama Abba, a ransa yana fatan ba wani abin ne ya faru ba "Lafiya kuwa Abban su?" Umma da fitowar ta kenan ta fad'a tana kallan Abban da damuwa ta gama bayyana akan fuskar sa, kallan ta yayi sannan yace "Na kira layin Kabeeru ne da farko ta shiga yanzu kuma ta dena shiga" Abban ya fad'a "Ae Ina tunanin yanzu yana cikin mota ne, babu mamaki ko shiyasa kaji wayar a kashe" d'an murmushi kad'an Abba yayi sannan yace "Babu shakka ma haka ne" itama murmushin ta maeda masa sannan tace "Ya kamata muje ciki koh?" Babu musu yabi bayan Umman da tayi gaba zuwa cikin gidan daya kasance madaedaeci, gida ne haka me k'ofa da d'aku na 4 a cikin sa, 1 parlour wanda ya kasance shine na Umma sannan d'akin gado shi kuma shine na Abba, sannan ragowar d'aku nan da suka kasance madaedaeta su kuma Yah Sadeeq da Ayrah kowannen su ya d'auki d'aya, se kitchen da ban d'aki, babu laefi gidan yayi kyau duk da ba wani girma gare shi ba amma an masa k'yale k'yale wanda suka k'awata shi. Kae tsaye cikin d'akin Abban suka nufa wanda shima yake d'auke da d'an madaedaecin ban d'aki a cikin sa, Umma ce ta taemaka masa yayi wanka kafin ya fito su d'an zazzagaya gidan, kukan Ayrah data jiyo daga parlourn nata ne ya sanya ta fad'in "Ya ilahy" "Toh rigimatu ta farka kenan" Abba ya fad'a yana murmushi, mik'ewa Umma tayi ta fita daga d'akin dae_dae lokacin da Yah Sadeeq shima yake shirin shiga d'akin, ganin Umma ya sanya shi fad'in "Alhamdulillah, Umma gwara ki rarrashi abar ki" ya fad'a yana juyawa yayin da Umma ta shige cikin d'akin, k'arasawa Umma tayi ta zauna inda Ayrah ke zaune ta kamo ta cikin jikin ta tace "Kiyi hak'uri kiyi shiru kinji Auta" "Umma Raj" Ayrahn ta fad'a tana kallan Umma da jajayen idanun ta, lumshe idanu Umma tayi a ranta tana cigaba da mamakin irin wannan shak'uwa tace "Shikenan za'a kira Abban sa ya kawo miki shi kinji?" seta cigaba da kallon Umman kamar me nazari se kuma tace "Umma ze zo?" murmurshi Umma tayi kana tace "Ehh ze zo" "Kuma in be zo ba na dena kula shi" ta fad'a cike da sakarci tana ta6e baki, girgiza

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70