Chapter 49
Chapter 49
"Raj!" muryar wanda yaji ne ta sanya k'irjin sa ya d'an buga sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Abbun dake k'arasowa inda yake "Ina ka shiga ne haka? Kasa hankalin mu duka ya tashi?" d'an yatsine fuska yayi lokaci guda kuma yana kae hannun sa kan sa sannan yace "Amm... Abbu ina so ne nayi settling abubuwa da dama, bana buk'atar takura ne yasa na kashe waya ta, ina fatan dae ban yi laefi ba?" ya k'arasa maganar yana kallan Abbun "Ohk tohm muje cikin Office d'in akwae maganar gaggawa da nake so muyi" be san sanda yayi gaba ba yana tarewa Abbu k'ofar shiga Office d'in ba sannan yayi wani murmushin yak'e yace "Abbu pls.." "Shikenan, kayi k'ok'arin gamawa, koma dae baka gama ba ka tabbatar ka dawo gida dan akwae muhimmiyar maganar da zamu yi bamu da ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an nazarin d'an nasa, ganin yanda idanun sa suka d'an tasa kamar wanda baya samun bacci, se kuma daya tuna yanzu yake fad'a masa aeki ne ya rik'e shi sannan ya d'an ji dama dama "In Sha Allah" shine abinda Rk ya fad'a yana d'an kaucewa kallan da Abbun ke masa, dan gani yake kamar yana kallan k'wayar idanun sa ze karanto rashin gaskiyar dake tattare da shi "Allah ya yadda" Abbu ya fad'a yana juyawa daga wajen, se a lokacin Rk ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanun sa, se yanzu ya gane shirmen daya aekata na zuwa da ita asibitin nan, me ya shiga kan sa ya kawo ta nan d'in? Hannu ya saka ya bud'e Office d'in ya shiga sannan ya kulle, idanun sa akan ta lokacin da idanun ta ke a rufe tana sauke numfashi a wahalce, daga yanayin yanda ta 6ata rae kawae zaka fahimci ba dad'in baccin take ji ba, ga kuma yanda ta d'an tura red lips d'in ta gaba kamar me shirin yin kuka, seya samu kan sa da lumshe idanu na tsawon second 10 sannan ya bud'e ya k'arasa bakin gadon bayan yaja wata kujera ya zauna, duk da yanda take sake had'e jikin ta waje d'aya hakan be hana gumi tsatstsafowa daga fuskar ta ba, ya sake sauke idanun sa kan fuskar ta sannan ya maeda kan jikin ta da har lokacin ke d'auke da hijab, a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in, kamar me tunanin wani abun ya dakata da hannun sa a sak'ale, ya kae wajen second 30 a hakan sannan ya k'arasar da hannun nasa zuwa kan hijab d'in nata ya fara janye shi sama, be sake shi seda yazo dab da fuskar ta, se a lokacin kuma ya fara tunanin yanda ze cire shi daga wajen fuskar ta dan baya so ya tashe ta dan kuwa be shiryawa abinda ze fad'a mata ba, be kuma shiryawa rigimar ta ba, a hankali ya d'an mik'e tsaye sannan ya rank'wafa ya kae hannun sa k'asan kan ta da nufin d'ago kan nata, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta da suka mata nauyi, se rumfar mutum kawae ta gani a kan ta, duk da yanda kan ta ke cigaba da mata ciwo hakan be hana ta sake ware idanun ta ba, duk da bata fahimci menene ba amma ta tsorata matuk'a dan haka bata san sanda ta mik'e zaune ba tana sakin k'ara, lumshe idanun sa yayi yana jin k'arar ta ta har cikin jikin sa, sanda ya ida bud'e idanun sa se nata idanun suka sauka cikin nasa, cikin wata rud'ewar ta saki k'ara tana yin baya gami da sake jan hijab d'in ta ta lullu6e kafatanin jikin ta tana sakin kuka kamar wadda aka daka, lokaci d'aya kuma jikin ta na cigaba da rawa, runtse idanun sa yayi saboda yadda yaji kan sa ya sara da k'arar da tayi har sau biyu, ya d'an dafe kan sa sannan ya bud'e idanun sa ya sauke su a kan ta lokacin da take cigaba da mak'urewa a jikin bango hannun ta rik'e da hijab d'in ta kamar zata maeda shi cikin ta, cikin karyayyiyar murya me had'e da kuka ta furta "Ina takadda ta? Meyasa baka maeda ni gidan mu ba?" tayi maganar sanda wasu hawaye masu d'umi suka samu damar zubowa akan kuncin ta, idanun sa yayi saurin janyewa daga cikin nata narkakkun idanun dake zubar da hawaye kamar an kunna famfo haka kuma sun cika taff da hawaye duk da wad'anda ke zuba, baya so tun yanzu raunin ta yaci galaba a kan sa dan haka ya d'an runtse idanun sa sannan ya bud'e su, ya d'auke su ya aza su a kan ta sanda ta cigaba da mutsu mutsu akan gadon tana cigaba da kukan ta "Me kike ci na baka na zuba Madam? Ae har yanzu yinin be k'are ba!" ya fad'a yana sakin wani miskilin murmushi.. Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 033 ___Ganin da yayi tana cigaba da bin sa da kallan tuhuma lokaci guda kuma tana sake kwa6e fuskar alamar koda yaushe zata iya sakin kuka ya sanya shi sake lumshe idanun sa sannan a hankali ya d'aga hannun sa dake d'auke da wani had'ad'd'en agogo ya juya mata dashi dan ta gani, bin hannun tayi da kallo dan fahimtar abinda yake nufi da hakan "Duba lokaci" ya fad'a har lokacin be d'auke hannun nasa ba, se ta sake bin hannun nasa da kallo sannan ta d'an runtse idanun ta dan har lokacin ganin ta be koma dae_dae ba, k'uri ta yiwa agogon kamar me k'irga sakannin da suke wucewa, ganin da yayi ta janye idanun ta daga kallan agogon ya tabbatar masa data gani, be sake cewa komae ba ya fice daga Office d'in, seda ya kulle k'ofar sannan ya tafi, bin sa tayi da kallo sanda ya fice d'in sannan ta dawo da kan ta kan gadon da sake kwantawa, ta k'agu ta koma gida, bata san nan d'in ina ne ba da babu shakka da kan ta zata koma gida. Wajen mintuna 20 se gashi ya turo k'ofar Office d'in ya shigo hannun sa d'auke da leda, se tayi sauri ta tashi dan tasan yanzu kam may be ya shigo mata da takaddar tane ta wuce gidan su, ganin yadda take shirin sakkowa daga kan gadon ne ya sanya shi fad'in "Kici abinci ki sha magani, sannan ki koma gidan" ya fad'a yana ajje ledar akan gadon ba tare daya kalle ta ba haka zalika fuskar sa a had'e, ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba d'aya bata ta wani abinci bare akae ga magani, dan haka ta d'auke kae kamar ba taji ba, d'an d'aga kae yayi ya saci kallan ta yadda take ta wani cic cin magani ita a lallae dole bata ji shi ba ya sanya wani murmushin gefen baki ya su6uce masa se kuma ya sake had'e fuskar sa sannan yace "Well, se kiyi ta zama anan d'in, ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ta6e baki gami da soma tafiya kamar ze bar Office d'in, se kuwa ta fashe da kukan tana sakkowa daga kan gadon gaba d'aya cikin kukan ta furta "Don girman Allah kayi hak'uri, bazan iya cin abinci ba, ka maeda ni gidan mu ko ka bani kud'in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70