Chapter 77
Chapter 77
Aunty Kharimatu bata gama rufe bakinta ba Juhud ta fito dauke da Muneefah da niyyar ficewa daga gdan Muneefah na ganin Rasheed ta fara zamewa a jikinta tana Kiran Dad sweet Dad biscuits...." Murmushin gefen baki yayi ya miqe ya nufi Meenah da takai bakin qofa yasa hannu zai karbe yarinyar ta juyo a fusace cikin bala'i tace “inada tabbacin bakada wata alaqa data wucce wan mahaifi gurin Muneefah domin kuwa qaddararta me qarfi ce itane ta sanya abubuwa da yawa suka faru a qarshe dai nida Kareem muka Samar da Muneefah saboda haka ikona ce" Sakin yarinyar yayi yayi baya jikinsa na daukar sanyi yanajin saukar kalamanta na dukan zuciyarsa, batare da wata damuwa ba ta fice ta jefa yarinyar da keta kuka a mota ta shiga ta figi motar a mugun guje ta fice a harabar gdan tabarshi tsaye kamar dashe Yana qara maimata kalamanta, Khamil ne ya dafashi yace “nifa Ina mamakin yanda dangantaka tayi tsami haka tsakaninka da Meenah meye ya farune mutumin bakada dama ne fah qila Kaine ka tabo zuciyarta" janye hannunsa yayi yace “koma mene ban cancanci wadannan munanan kalaman akan yar qanina ba Amma zan gwada mata haihuwa ce tata nafita qarfin iko" Yana fadin haka ya fice Yana huci ran maza ya baci Jabir ne yazo yajasu suka nufi gda ganin motar da ta hau ta fito yasashi tabbatar da gidan ta dawo, bai shiga cikin ba ya nufi sashin baqin ya cire kayansa ya zauna yana fitar da iska me zafi zuciya na raya masa meye zaiyi ya rama wannan wulaqancin da Meenah tayi masa? Ya jima bacci bai daukeshi ba sai juyi yakeyi da safe ya fiçe ya nufi cikin gdan Meenah bata tashi daga bacci ba a zahiri ba baccin takeyi ba kawai juyi takeyi, shiga yayi part din kumbo Hami suka gaisa ya wucce bangaren Alh Garbu suka gaisa yayi shiru na dogon lkc kamo hannunsa yayi yace “meye yake faruwa ne Dan Boko?" Qasa yayi da kainai Yana shafa sumarsa can Alh Garbu ya sake dubansa yace bai wucce kace kanason tafiya da matarka ba ko?" Jinjina kai yayi yace “hakane Alh inason jibi idan zan tafi mu tafi gabadaya saboda dawowa zatayimin wahala kusa" jinjina kai Alh Garbu yayi yace “shikenan zan fadawa kakar taku inyaso saisu fara Shirin abinne yazo Babu tsammani Amma fah akwai abinda bazan dauka ba cikin lamarin aurenku duk wani cin Kashi da akayi mawa Aminah a baya yanzu ko ita ta daukeshi ni bazan daukaba" ya jima yana kafa sharrudansa shidai Rasheed jinsa kawai yakeyi har ya gama ya tashi ya fice. Lkcn da Kumbo Hami taji Shirin da Alh Garbu yayi taso tace aa Amma ya hanata katabus dole hakanan ta hqr tana jiran ranar zartaswa aikam ana samun Meenah da mgnr tayi tsalle ta dire tace batasan zance ba duk Wanda suke tunanin zai fada aji ya fada tayi kunnen uwar shegu Rasheed kam abokin gaba ya zama batako kallonsa bai wani damu ba saidai ya kalleta yayi murmushi ya barta tayi duk abinda yasan na dan lkc ne da lkcn ya wucce shikenan, ana gobe tafiyar da dare ya shiga har dakinta ya tarar da ita itada Aunty Kharimatu da Kumbo sai aikin rarrashinta sukeyi suna ganinsa suka miqe suka fita ya mayar da qofar ya rufe ya nufota ta miqe tsaye ya tsaya Yana murmushinsa na isa tare da zura hannunsa a aljihunsa ya harde qafarsa ya jingina jikin bango yace “banzo domin na baki hqr Kona rarrasheki ba saboda Ni nasan banyi miki laifi ba hasali ma nine nake tuhumarki so inada abinda yafi haka muhimmaci kin fadamin wata mgn ne da nakasa jureta shine nazo baki amsa Meenah yes na amince keda Kareem kuka Samar da Muneefah Amma kada ki manta kafin Kareem ya baki da nine na fara baki na farko kika zubarmin na biyu kika haifamin gashi ya zama saurayi so wannan kadai ya isa ya tabbatar miki ni na wucce kiyimin gatsali akan Muneefah Kuma ko kinaso ko bakiso dole kibarni da ita domin ba saboda ke nakejin yarinyar a Raina ba saboda mahaifinta yayimin kyautarta ne" Shafa gemunsa yayi yayi murmushin gefen baki yace “shekarar Muneefah daya da rabi ki shirya karbar qaninta kowanne lkc daga yanzun ni bana wasa da dama amfani nakeyi da ita sosai" ficewa yayi daga dakin yabarta tsaye da zubar hawaye takaici kamar ya kasheta taja qwafa ta koma ta zauna. Duk wani shiri da Kumbo Hami taso yi mata taqi bata hadin kai sai huci takeyi kamar ta kashe kowa haka takeji batasan meye yasa takejin haushin Rasheed ba ko ganinsa batason yi sauqinta daya dake tunda ta haihu Kumbo take hadata da magungunan da tasan bazasu cutar da itaba so data fahimci ba hadin kai zata bata ba saita tattara mata ta zuba mata cikin kayanta ta hade mata komai washegari kuwa da wuri suka dauki hanyar 9ja aikam anyi tafiyar kurame Babu me cewa wani qala garama shi da Khamil suna hira jefi² inda suka sauka ta tsaya tana kallo bata taba zuwa Lagos ba hakanan takejin to Ina ya kawosu?" Bai bata damar tunanin mafita ba motar office dinsa tazo ta daukesu suka nufi unguwar da yake da zama tasha mamakin gidan da aka kaisu ta tsaya tana qare mawa gidan kallo. Plat ne me kyau sosai Rasheed akwai son qyale² ya qawata gidan tsaf ta tabe baki tajishi ya saqali hannun Muneefah ta sakar masa ita ya nuna mata dakunan yace gasunan keda yaranki duka sun isheku fatan nasara" dakinsa ya shige da Muneefah tabisa da kallon takaici ta gyada kai ta bude dakin kusa da ita ta shiga komai na dakin a tsare yake sosai abin gwanin birgewa gefe ga wasu manyan set na akwatuna guda 12 ta zubawa akwatunan idanu tana tunanin to na meyene?" Tabe baki tayi tace “nima dai da son wahalar da kaina kulle dakin tayi ta cire kayanta ta bude akwatun da ta taho da ita ta dauko wata qaramar riga Mara hannu ta shafanta turaruka ta nufi bayi tayi wanka ta fito ta shafa mai ta zura rigarta ta haye gado taja duvet tunda ba sallah zatayi ba nan take baccin gajiya yayi gaba da ita batasan sanda ya shigo ya kwantar mata da Muneefah ba sai wajen hudu ta farka taganta kwance ya cire mata riga daga ita sai Pampers tanata baccinta. Yunwa ce ta fafareta ta miqe ta fito tana hamma ta nufi kitchen din taji qamshi na tashi ta qarasa da sauri ganinsa tayi dagashi sai boxes da headphones a kunnensa ya zage sai yankan alayyahu yakeyi ta juya zata tafi ashe ya ganta taji yace “kije ki huta idan na gama zan sammiki nasan cikinki ne Babu alert shiyasa kika fito Yayi tsammanin zata kulashi yaga ta juya tayi tafiyarta ta koma dakinta yaci gaba da girkinsa Yana waqoqinsa bayan ya gama ya jera a dinning ya bude dakin ya isheta tana waya daga yanayin wayar yasan da Mom dinsa takeyi ya shafa kansa ya juya ya fice, koda ta idar bata nemesa ba har ya sake gajiya ya shigo ya tararta ta hade kai da gwiwa tanata jan zuciya ya matsa gabanta ya tsugunna yasa hannu ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82