Chapter 29
Chapter 29
wata takarda qarama dake a ciki miqa mata takardar sukayi taqi karba saima miqewa da tayi Mom tace “ungo ana Kira ki daga kije me zaace miki" noqe kafada tayi tace “Mom....." Hannun Mom ta Dora a bakinta tace “shitttt Amina banson gardama da fada da Wanda baka sani ba ai gara kayi da wanda ka sani ko banza akwai sanayya" Hannu tasa ta karba tanabin number da kallo hannunta na rawa ta danna wayar ta Kara a kunnenta yaja ajiyar zuciya daga yanayin saukar numfashin ta gane wayene nan take zuciyarta ta hau kai kawo a qirjinta. Bai bata damar tunanin komai ba yace “baki tausayin me tausayinki ko Meenah?" Shiru ce ta ratsa ta juya ta dubi Mom ta nufi qofar dakinsu yafi minti biyar kafin ya qara qutawa yace “banyi tunanin wannan sakayyar daga gareki ba inaji a Raina a baya idan kowa ya juyamin baya ke zaki kalleni da idanun Rahma ashe ban fahimta daidai ba Meenah meye aibuna da kika kasa maye gurbin rashin cancanta da cancanta a tunanina ko ban cancanta ba ya kamata ki kama hannuna ki dagani matsayin gwaninki....." Shiru yayi saboda numfashinsa da yake sarqewa yaja numfashi sosai sannan yaci gaba da cewa shekaruna 37 bantaba ji ko a wasa ina muradin rayuwa da wata mace matsayin mata ba sai a wannan gabar da qaddarar ta hadani dake tabbas da nasan cewa kedin zaki zamo masheqin rayuwata da ban fara jin tausayinki a farko ba" jikinta ne yayi sanyi da kalamansa zuciyarta ta karye bai Bari tace komai ba yace “bansan meye laifina ba don nace inasonki wlh tallahi duk duniya babu namijin da yakeyi miki irin son da nakeyi miki Meenah ba iyakar farin cikina zan fansar gareki ba har rayuwata da mutumcina duk zan iya sallamasu dominki na rantse da Allah idan ban sameki ba matsayin mata to kuwa shima Kareem bazai sameki ba saidai muyi ragas gara ki fita waje ki auri wani Amma a gdanmu ki auri qanina ki rayu dashi gani Ina bulayi Ina bazan iya ganin wannan baqin cikin ba, yess kince yanada nagarta nasan haka Ni banida nagarta Mazinaci ne ni yanzu Kuma soyayyarki ta mayar dani mashayi Kuma a haka zakizo ki rungumeni ki rayu dani dole idan kinqi bani hadin kai don Allah zaki bani don dole Meenah kiji a ranki ni mijin mace daya ne Kuma kece ko babu aure zamu rayu tare" Cikin tsananin fusata da kalamansa tace “ya Isa Baffa'am bantaba ganinka matsayin qasqantacce ko marasshin daraja ba wlh ko lkcn da nasan kana zaman dadiro da arniya mara Imani banji na tsaneka ba Amma yanzu kalamanka suna aika saqo cikin zuciyata duk da kasancewata mara galihu na shaida niba banza bace kamar yanda kakejin izzar sarauta a cikin jininka nima inajin izza a nawa jinin saidai Ni bansan ta meyece ba da wannan nake son sanar dakai na gode da kulawarka gareni Amma bazan taba kwarewa Mai Martaba baya ba saboda jin ya isa dakai yasa yaji a ransa nima ya isa Dani ya zabamin Ya Kareem batare daya nemi shawararmu Ni dakai ba to danme Ni zan nuna masa nidin ba halattaciyar ya bace? Numfashi taja taci gaba da cewa “bari kaji Baffa'am bazan taba canza zabi ba domin ba zabina bane na ubangiji ne saboda haka bana buqatar kalamanka ka adanasu ka fadawa Aunty Zulaihat ita zataji dadinsu Kuma zasuyi mata amfani Amma Banda Aminatuh"....... Qit ta kashe wayar gabadaya ta cillah a wardrobe tana jan tsaki Baffa'am din nata ya fara kai hqrnta qarshe to waima anayin so dolene da zai takura saita qaunaceshi bayan tariga tayi kyautar zuciyarta ga waninsa?. Komawa tayi ta zauna a hankali Kuma take auna kalamanta sai takejin babu dadi duk da cewar gsky ta fada masa, turo qofar akayi aka shigo ta dago ganin Muntaz yasata miqewa ya zubawa qirjinta iso yana murmushi wayarsa tayi ring ya miqa mata yace “kin tara kayan dadi baby Amma na hqr na fahimci babu rabona a wannan gurin gonar manya ce" tsaki tayi ta karbi wayar ganin sunan dake kai yasata miqa masa ya matsa da sauri yace “ai baki isaba yarinya dole ki Amsa wayar nan bazaki jamin masifa ba" jifa tayi da wayar ta shige bathroom bugun duniya taqi budewa Saida taji ya cewa “taqi karba fah tama shige bayi tabarni shanye kamar maratayi" Bata fito daga bathroom dinba Saida taji shigowar su Ya'isha ta fito tana goge idanunta da suka canza kala, da dare ma daya kirata a tata wayar da yasa aka tura masa number tana ganin numbersa ce ta dannata a silent ta koma ta kwanta washegari ta kama idi tun asuba suketa shirye²n tafiya idi sai bakwai suka gama suka fito sunata baza selfie Suna Shirin fita ya shigo sanye da kakinsa hularsa a hannu ya sauke idanunsa akanta tare da kwantar da kansa a jikin qofar yanajan wata wawuyar ajiyar zuciya me qarfin gaske qwarjini yayi mata ta kasa motsawa daga inda take su Amrah sukayi masa barka da zuwa ya dagansu hannu tare da nuna musu hanya suka fice ta daga qafarta daqyar zata bisu ya cafko hannunta ya janyota ya shigar da ita jikinsa ya matseta sosai yanda bazata iya motsawa ba yace “barka da sallah My wife" qoqarin qwacewa taketayi da hannu daya ya hardeta Amma ta kasa qwaqqwaran motsi ya figi hannunta ya nufi sama da ita ta cake a bakin qofar ta riqe qarfen benen ya juyo ya zuba lumsassun fitinannun idanunsa akanta yace “idan Kuma nayi amfani da qarfina nace saikin shiga cikin fah ya zakiyi?" Qasa tayi da kanta ya dagota yace “banson kuka kawai maimaitamin kalamanki na jiya zakiyi" da sauri ta dago yayi mata murmushi yace “zanyi amfani da duk wani abu daidai ko rashin daidai domin naga na hanaki samun abinda kike tunanin shine ya dace dake badon na cutar dake ba saidon sama miki yanci zaifi miki dadi ki rayu da wanda yasan mutumcinki" Dagowa tayi ta zuba idanunta cikin nasa tace “kana nufin Ya Kareem baisan mutumcina ba kai kadaine kasani?" Baitaba tunanin abinda zatace kenan ba ya tsaya cak Yana nazarin me zaice mata ta juya zata fice ya sake riqota yace ki shirya zaki rakani unguwa" hannunta ta janye batare da tace masa komai ba ta fice ta nufi masallacin suna idar da sallar ta zille ta nufi wani bangare na gdan ta zauna tana wayarta da Kareem dinta taji an cire wayar a kunnenta ta juya da sauri yayi wanka ya canza kaya cikin wata brown gezna yayi mata kyau sosai taja fasali yace “zaki?" Kallonsa tayi zatayi mgn yace “bama zabi zan baki ba dolene kizo muje" bata kawo komai ba batayi tunanin komi ba tabisa har inda yayi parking motarsa ya bude mata ta shiga ya sake mata murmushi yaja motar a guje suka fice Muntaz ne kawai yaga lkcn daya dauketa suka fice, Sunyi tafiya me nisa da gidan sarautar ya dauke wata hanya itadai batace masa komai ba wasa kawai takeyi da yatsunta Yana satar kallonta yayi parking jikin wani gda ya fita ya bude ya dawo ya shigar da motar ya sake rufewa ya bude mata qofar ta fito tana qarewa gidan kallo koda bata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82