Chapter 5
Chapter 5
aureki sai susan yanda zasuyi su hallaka babanki su kwashe dukiyarki, Abu kamar wasa gaba me tsanani ta shiga tsakaninsu ko gaisawa basayi watarana da dare har mun kwanta Bangel yazo yayi sallama da Baffanki ya tashi ya fita bansan me suka tattauna ba nidai naga ya dawo yana huci na tambayesa yake cemin Aishatu don Allah ko bayan raina karki yarda ban aminta Aminatu ta auri Manga ba na haramta hakan idan har hakan ta faru bazanyi farin ciki ba" jikina yayi sanyi ya kwanta ranar kwana yayi yana juyi yana hawaye idan na tambayeshi sai yacemin shidai bai aminta Aminatu ta Auri Manga ba a lkcn inata fama da rashin lfy mukaje gun me magani yace cikine dani amma ya kwanta. Ban wani damu ba duk da cewa Baffanki kullum cikin kawomin magani yake hakan baisa cikin nan ya tashi ba wata biyu tsakani sukayi wani gagarumin rikici daya sanya suka qara kullatar juna ashe a wannan dare sukayi taro suka yanke shawarar tunda yaqi basu hadin kai kawai su kasheshi su huta mana inyaso sai manga ya kada shanun yayi kudu dasu kinga zaace barayin shanh ne suka kasheshi. Maddibo Buba ne yaji wannan shirin nasu a daren kuwa ya kira Haro ya sanar dashi abinda yan'uwansa suke shiryawa yaja fasali tare da murmushi yace “babu komai Allah yafi kowa sanin abindake qarqashin qasa dana ban qasa yafi kowa sanin daidai" daya dawo bai sanar dani ba nidai naga ya tashi cikin dare ya dauko wata qaramar adaka ya bude ya zaro wasu abubuwa masu walwali yabani yacemin Aishatu wannan abin da kike gani ba komai bane face dutsen Lu'ulu'u wanda yan birni suke cewa diamond wannan kuma gwal ne nasan kinsanshi don Allah ki nemi guri kiyi musu mugun boyo asalinsu na Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da wadannan abubuwan" Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su kubce miki kinji" jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa “washegari da safe na damawa Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da zaki fita dashi talle. A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura aurenki da Manga nikuma gashi Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa. *ASALIN LABARI* Jikin Juhud ne ya qara sanyi hawaye na sunturi a kucinta tace “yanzun wadannan sune kadai dalilan da suka sanya Suka kashemin Baffina Amma aka kasa daukar mataki akansu Innatu wannan wacce irin Al'umma muke ciki meson kanta? Shafa nadaddiyar sumarta tayi itama cikin hawaye tace “haka rayuwa ta zama kina gani fah tunda Baffanki ya rasu ko nono sun hanamu tatsa saidai su tatse subawa matansu suje su siyar idan kinga mun samu nono a rugarnan to Moddibo ne ya tatso mana Juhud ya zakayi ne da qaddararka ni yanzu burina a duniya naga kinyi aure kin samu matsugunni saboda wannan rayuwar bata yuwuwa a haka" Fadawa tayi jikin Innatu tana kuka me cin zuciya itakam da Innatu zata amince da sun bar rugar nan tunda baa sonsu amma tasan bazata aminta ba, da wannan tunanin bacci barawo ya saceta. Washegari da wuri ta dauki tallan nononta ta tafi tasha cike da doki yau tayi niyyar idan tayo ciniki har Balangu zata sawowa innatu ko tsiren quli tana tafe tana yan waqoqinta harta isa gari koda taje yan nonon gurin ya cika batada guri dole ta koma gefe ta rakuye tana wasanninta na quruciya dagowar da zatayi taga wani baqin hadari ya gangamo tana juyawa taga Fulanin duk suna hade karensu gashu batayi cinikin kirki ba donma ta datsa yariman ne ta dibarwa wani na dari biyu shiyasa da haka zata koma. Ganin hadarin na gangamowa yasata miqewa jikinta a salube tana juya dari biyun ta gama kasaftata tasai mawa Innatu maganin ciwon jikin hamsin tasai mata balangun dari ta riqe hamsin a hannunta ko batirin fitila sa siya, daukar qoranta tayi ta aza aka ta juya kenan zata tafi taji wata mota tayi horn a bayanta ta juya taga me motar ya zuge glass wani matashin saurayi ne me qwarjinin gaske fuskarsa a daure ya bude bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace “na nawa ne?" Cikin fullanci yayi mgnr tayi saurin Amsawa da cewa na dubu Uku ba dari biyu" dubanta yayi yace “harke?" Kallonss tayi da rashin fahimta ya daganta gira yace “inaso ki juyemin da sauri" daidai lkcn taji gabanta ya yanke yabads wani dam ta dafe qirji da sauri tana waige² yace “ko bakiji ne?" Da qaraji yayi mgnr taja numfashi ta miqa masa har qoran tace banida ledar da zata dauka duka kaje da qoran ka dawo mani dasu wataran" karba yayi yasa a bayan motar ya zaro dubu biyar ya bata yace “gashinan har kudin qoranki bana shigowa garinnan sai idan wani babban uzuri ya taso" karba tayi tayi godiya ta juya da sauri ga mamakinsa kawai yaga ta take a guje ya saki baki yana kallonta a fili yace “lkc guda nutsuwarta ta gushe ko meye yaja hakan?" Tabe baki yayi ya daki kansa yace “kaima Cornel Rasheed da shiga abinda babu ruwanka kake" cikin kasuwar ya shiga yayi siyyayarsa ya juya da motarsa yabi wata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82