Chapter 27
Chapter 27
ta kafesa da idanunta da yake tsiyayar da hawayen tashin hankali tasowa yayi ya matso gabanta ya miqar da ita yace “idan ya kasance kin kasa saka wancan Alkhairin da abu mafi daraja wato qaunar da wannan mutumin yake nema a gurinki to tabbas ke ba yar halak bace domin dan halak shine yake jiran gabar saka Alkhairi da komansa koda kuwa gurin bai cancanci sakayya ba shidai burinsa yaji a ransa babu bashi tsakaninsa da wannan mutumin" Sakinta yayi ya juya zai shiga bathroom har ya bude ya juyo yayi mata murmushi yace “kije kiyi tunani akan kalamai na" a mugum kasalce ta bude qofar ta fito ta nufi cikin gdan zuciyarta na kai kawo akan kalamansa tana shiga dakinsu ta zube a bakin qofar tana mayar da numfashi Amrah dake fitowa daga bathroom taja ta tsaya sake da baki ganin yanda ta cure jikinta tanata rera kuka takaici yasa Ya'isha miqewa tace “dallah malama ke baki rabo da kukane meye Kuma akayi miki" dagowa tayi ta kwantar da kanta jikin Amrah tace “nikam Ina ganin rayuwa Amrah don Allah meye wadannan kalaman suke nufi......" Zayyane musu komai tayi ta qarashe da cewa “bansan meye yasa qwaqwalwata bata gane abubuwa ba" numfashi Amrah da Ya'isha suka saki tare Amrah tace “kan ubancan lallai akwai qura a gdannan Juhud bafa wani abu Big Cele yake nufi ba kece yakeso kece Aminan da yake baki lbr ke kadai ce me wannan siffar daya suffanta" Ya'isha ce tayi murmushi tace “ke saiyau kika fahimta ai dake da Aminah dukkanku kallonku nakeyi Amma wlh batun yanzu ba na fahimci Big Cele son Juhud yakeyi tsabar miskilanci ne da girman kai ya hanashi bayyanawa yake wani bada fadi da hura hanci kamar kyankyaso aikin banza na dade da gano damuwarsa kekam ta bakin naki kina ganin rayuwa ga Mai Martaba yayima Ya Kareem alqawarin aurenki" cikin mutuwar jiki ta dago tace “nikam ya zanyi wlh da gaske bantaba daukar wannan gundumemen lamarin zai fadomin ba banyi masa muhalli a bangarena ba bantabajin Baffa'am zaice yanasona ba kai bama abinda yake nufi ba kenan babu abinda zaiyi dani" Dariya sukayi dukkansu ta zubansu idanu Amrah tace “waima to shi ya gani wlh yarinya tun wuri ki takansa birki inba hakaba zakisha wahala Big Cele bashida mutumci gashi da ganinsa zaiyi wuta babban tashin hankalin ma mgnr aurensa da Zulaihat tayi mugun nisa harma fah ankai kudin tambaya sa rana kawai zaayi anasa rana Kuma raqashewa zamuyi Kinga kenan bakida gurbi kawai batankin gomanki zaiyi dayanki bata gyaru ba" Tagaji dajin wadannan kalaman hakanne yasata miqewa ta shiga bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta fito taji ana kiran magrib ta dauki dabino ta tauna ta fita ta dauko ruwa tana dawowa Amrah ta miqa mata waya ta Amsa ganin number Kareem ta Kara a kunnenta tace “nasha ruwa lfy Habiby kaifa?" Murmushi yayi yace “yanda kikasha Luv ya exams?" Kwanciya tayi tana lumshe ido tace “inajin dadin exams din da taimakonka" hirarsu sukaci gaba dayi tama manta da batun Shan ruwa saida yace “kije kisha ruwanki zan kiraki anjima" ta aje wayar ta tayar da sallah tayi buda bakin. Tun daga wannan ranar salon rayuwar gdan ta canza musamman tsakanin Juhud da Rasheed duk inda tasan zasu hadu gujewa gurin takeyi saboda ita har cikin zuciyarta bataji a ranta zata iya soyayya dashi ba bayan haka ma sannu a hankali Kareem ya gama siye zuciyarta da salon qaunarsa me tsayawa a rai da wuyar gogewa kullum idan sunyi waya kalmarsa daya itace don Allah Aminah ki kulamin da kanki nayi miki tanadin kaina na tsare kaina tsayin shekaru burina ya kasance a halali na na fara shuka inason gonata tayi kyakkyawan yadon da yabanyarta zata burge kowa idan amfanin ya nuna ya isa moro ya morawa duniya baki daya Aminah samawa yayana uwa ta qwarai shine abinda na dade Ina addu'a nasani bazan taba danasani ba idan kin kasance mata a gurina zaki bani farin cikin da zanyi alfahari dake a duniyata da lahirata" Idan ya fada mata haka Yana kashenta jiki matuqa takanji kamar ya daureta da jijiyarta ne duk saitaji wani shauqin qaunarsa Yana qara mamaye ruhinta wannan dalilin yasa ta qara qaimi wajen tsare kanta tunda me bata kariyar bayanan gashi ya Daura mata nauyi Mai girma na amanarkai. Kwanci tashi lkc ya rinqa tafiya cike da matsaltsalu Rasheed mugun miskili da baa gane matsalarsa Amma yanzu kusan kowa ya fahimci yanada damuwa gashi da baqin zurfin ciki ya kasa furtawa kowa damuwarsa saidai yaje Garden yayi tagumi ko ya tusa waya a gaba yayita kallo. Ranar da sukayi Candy suka hada qwarya²r party a gidan sarautar Juhud batada qawaye su Ya'isha ne suka gayyato samarinsu da qawayensu Mai Martaba shine ya daure gindin partyn harda dauko musu Dan Hausa yazo don qarawa abin armashi qarfe hudu suka fara caskalewa samarinsu duk sunzo itace kadai saurayinta baizo ba baya qasar ma Amma yayi mata fatan Alkhairi sun dauki wanka na tashin hankali sunyi kyau na bam mamaki dama dukkansu ba baya ba wajen kyau Amma sukansu Saida suka sallamawa Juhud tayi kyau kamar wata amarya suka fito daga gdan ana take musu baya suka fara hotuna anyi mata hoto yafi kati dari da shiga daban² ta karbi wayar Ya'isha ta zagaya baya ta Kira layin Ya Kareem bugu daya ya daga tayi ajiyar zuciya tace “rayuwata tana cike da kewar masoyi banajin komai yana tafiyar min daidai" dariya yayi yace “kinajin abinda nakeji kuwa Aminah nifa inajin kamar zanyiwa Mai Martaba mgn ne zanzo hutun azumi kawai a hada bikinmu dana Big Cele ayi a bani ke mu taho nan" Juyowar da zatayi suka hada ido da Rasheed dake tsaye jikin swimming pool kallon da yake mata ne yasata kama in...inar qarfi da yaji tace “am...in...." Ji tayi ya warce wayar ya duba yaga number qanin nasa yana mgn Yana cewa “hello..... Luv....." Qit ya kashe wayar ya jefa a aljihunsa ya juya yabar gurin daga Ya'isha dake qarasowa ta dafata tace “wai me kikeyi ne anata nemanki" juyowa tayi idanunta ya ciko da qwallah tace “ya qwace wayar Amrah...." Binsa sukayi da kallo Ya'isha tace “hmmm wannan mutumin dan rainin hankalin mutumin wlh bashi da mutumci yanzu duk hotunan da mukayi sun tashi a banza kenan?" Qwafa Amrah tayi tace “kuma duk baqin cikinsa bazamu fass shagalinmu ba Allah yasa ba layina bane akai daya cuceni" janta sukayi suka shiga filin itadai yaqe kawai takeyiwa mutane har takwas taron ya tashi suka shiga gda ta shige daki ta kwanta tana mayar da numfashi. Da wayar Ya'isha Kareem ya sake kiranta yake tambayarta Ina wayarta ne yanata Kira a kashe taja fasali tace “Baffa'am ya qwace tawa ta Amrah ce nakesa layin itanma dazun ya qwaceta" wata iska ya furzar yace “ina Gsky abin nasa ya fara yawa fah banason shigarmin hanci da qudundunen nan da yakeyi Ina ganin girmansa kada azo ayi babu dadi zan fadawa Mai Martaba ya dakatar dashi gsky na gaji duk yabi ya takuraki to ko hsihuwarki yayi kikakai yanzu ai ya qyaleki balle a sama yaganki" itadai batace komai ba saboda itanma duk kawaicinta da kararta Baffa'am din nata ya fara duba juriyarta. ************* Satinsu biyu da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82