Chapter 50
Chapter 50
yayi shafa'i da wuturi ya haye gadon ya kwanta tare da daukan yaron ya dora a qirjinsa yanajin qaunar gudar tsokar tasa har cikin bargonsa, zubawa p.o.p idanu yayi yana nazarin kalaman Meenah tabbas lamarin yau me girma ne Meenah da bakinta ta furta masa gara rabuwa dashi akan rayuwa dashi wannan abu yanayi masa ciwo duk wata matsala ta gidansa bata zuwan musu a kankin kansu saida wasu su qirqireta idan yace zai dauki mataki a hanasa wannan wacce irin rayuwa ce ne?" Miqewa yayi ya dauki Mahfuz daya farka a bacci yake neman uwarsa ya fita ya nufi dakinta ya bude ya shiga ga mamakinsa ya isketa zaune can qarshen gadon ta zuba uban tagumi ya zubanta ido tausayinta da qaunarsa na qara nunkuwa a zuciyarsa ya haura gadon ya kwantar da Mahfuz ya sanya hannunsa ya janye mata tagumin ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunsunar sumarta yanajin wata natsuwa na kwararo masa yace “idan na rasa gatan kowa a duniya baikamata na rasa naki ba Meenah bai kamata na zamo mara galihun nunawa duniya a gurinki ba bayan kin kasance mace daya tal dake mulkin zuciyata please na roqeki ki daina jin a ranki akwai abinda zai rabamu qaddarar mutum Babu me tayashi dakonta ni kece qaddarata nima nine qaddararki bazan hanaki kuka ba akan abubuwan da suke faruwa Amma dai ki rinqaji a ranki iyakar rintsin rayuwar duniya ni nakine ke kadai Babu wani tsanani da zaisa na rabu dake saidai qaddarar mutuwa idan ta gifta saboda haka banson sakejin wadannan kalaman naki don Allah kinji?" Zamewa tayi a jikinsa ta miqa hannu ta dauki Mahfuz tayi Bismillah ta Sanya masa nonon ya kama yanasha shikuma yana aikin kallonsu. Kwanciya tayi badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta hutu shima kwanciya yayi a bayanta ya maqaleta da haka sukayi bacci washegari da wuri ya fice daga gdan duk cika ta gidan sarautar idan ka shiga barayin Rasheed bazaka taba cewa sabuwar haihuwa akayi ba saboda yanda gdan yake a yashe daga ita sai Kumbo Hami suketa harkokinsu Rasheed bai dawo ba sai bayan Isha lkcn har sun kwanta ya shigo ya kirata ta miqe ta nufi dakin nasa yana safa da marwa ta samu guri ta zauna shima ya zauna a gabanta ya dubeta sosai yace “nasa anzo an kama Hajiya Bilki da Dada Hanne....." Dafe qirji tayi da sauri tace “na shiga uku Baffa'am me sukayi maka?" Share zufa yayi ya miqe yace “saboda a koya musu hankali su fita daga harkata da iyalina" yana mgnr yana hada kayansa ta miqe ta Isa gabansa jikinta na rawa ta durqushe tace “wlh wannan abin baikai ka dauki wannan matakin ba Abban Sarki ana barin halal ko don kunya please kada kayimin haka wani bala'in zaka qara jefani a ciki kasa a sakosu wlh ni na yafe musu...." Rufe mata baki yayi yace “ke zaki iya yafewa saboda bakisan ciwon kanki ba nikam ban yafe ba Yana fadin haka ya shige bathroom yabarta sake da baki wannan mutumin kwai dan neman jarfa anason kashe wata yana neman zunguro sama da kara Tananan zaune ya fito daga wankan Yana tsane ruwa ta sake dubansa zatayi mgn ya nuna mata hanya yace “jeki ma hadu da safe inason zanyi yan nazarce nazarce" miqewa tayi jikinta a mace ta koma dakinta ta ishe Kumbo Hami tana sallar Isha ta zauna bayan ta idar ne take tambayarta meye yake faruwa ta kuwa zayyane mata komai tayi shiru na dan lkc sanna ta dago tace “banji dadin kaisu qara da yayi ba shima hakan qarin wata fitinar ce daya qyalesu watarana sai lbr" Miqewa tayi ta Sanya Sarki junior a gadonsa tana cewa “nima abinda naso ya fahimta kenan yaqi bani hadin kai koroni ma yayi Kuma tunda yayi niyya Babu me hanashi" da wannan tayi addu'a ta kwanta sukayi baccinsu itadai da zullimi ta kwana aikam abinda take gudun ne ya faru da safe Yana fita Hidaya da Khadija sukayiwa gdan tsinke suka rinqa zaginta sunacin mutumcinta Meenah babu baki sai hawaye kawai da takeyi suna tsaka da wannan tujarar ne Kareem yazo musu barka don shi sai ranar ma yakejin lbrn haihuwar gurin Fadila aikuwa ranar Khadija da Hidaya sunji a jikinsu domin dukan mutuwa yayi musu kamar shine sojan daqyar Mai Martaba ya qwacesu barkar da baiyi ba kenan ya fice daga gdan rashin mutuncin gdan ya fara girmewa tunaninsa ace Babu Wanda ya isa ya fada aji anbi an tsangwami yarinya akan abinda bashida tushe balle makama aikam ranar hatta Addah Abulle Saida taji kunyar irin rashin albarkar da Kareem yazo ya zazzage mata a gdan akan rashin zuwa taga Dan da aka haifawa Rasheed yan uwansa kuwa gda gda ya rinqa binsu yana ci musu mutumci Yana fada musu ai ba Meenah suke qi ba Rasheed suke qi tunda shine ya dauko Meenah Kuma yakeson kayarsa sannan ba Meenah kadai ta haifi Mahfuz ba Rasheed shine silar zuwansa duniya saboda haka shine basaso" Basu wani dauki mgnr da muhimmaci ba ba Kuma su risuna ba sukaci gaba da dabdalarsu rikici yaqi qarewa cikin wannan family har ranar suna akayi sunan babu wani armashi kamar abin arziqi dangi suka hadu ranar Meenah Saida ta gwammace ita dama mutuwa tayi da wannan baqin cikin data riska wannan Rana a qarshe baa gama sunan da ita lfy ba sai a gadon asibiti ta qarashe sunan jininta yayi mugun hawa hawan da Rasheed bai taba tsammani ba ya shiga tashin hankali matuqa da yanayin da yaga matar tasa a ciki, da dare aka sallamesu suka dawo gda kanta na ciwo sosai da Rasheed da Mom da Kumbo Hami sunata rarrashinta da kalami na kwantar da hankali bacci ya dauketa washegari badon yaso ba ya shirya yabar garin ya koma wajen aiki yabarsu cike da kewar juna................ _Kuyi hqr da wannan_ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/4, 8:56 PM] Oum Hairan: *0028* Kwananta sittin da haihuwa Kumbo Hami ta koma Mali inda ita Kuma taci gaba da rainon danta cikin kulawa da tattali a hankali lkc yaketa tafiya qaunarta da Rasheed tanata qara gaba inda aiki ya riqeshi kusan watanni biyar sannan ya waiwayosu ranar anyi qara'in rayuwa kamar bazaakai gobe ba yayi musu sati biyu ya shirya domin tafiya wani aikin hadin gwiwar qasa da qasa zuwa Togo yaso tafiya da ita Mom tace gara yaje yaga yanayin gurin tukunna inyaso sai yazo ko ya aiko tabisa. Hakanan suka rabu bason ransu ba wani abin almara tunda ya tafi wayarsa bata shiga da farko sun dauka yanayin aiki ne tafi tafi da tafiyarsa ya dauki wata biyu babu waya babu aike, sosai hankalin Juhud yaqi kwanciya hakanan wata faduwar gaba ta aureta Mom ma tana cikin damuwar rashin jin labarin dannata hakanan take daurewa tana kwantarwa da Meenah hankali, tafiya na qara tsayi har aka tafi wata shidda Babu waya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82