Skip to content

Chapter 75

Chapter 75

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

kece bansan ya ake tunani ba Amma idan na zauna kece kikemin gizo da siffofi mabambata" Numfashi ya sauke ya juyo idanunsa na zubar hawaye yace “meye kike tunani ranar da Allah ya Amsa addu'ar masoyana ya dawo dani hayyaci na laluba naga bakinan na tambayi kina Ina akacemin kina matsayin matar wani waninma qanina Meenah taya zan iya yafewa kaina bata lkcn da nayi na nakasa rayuwata saboda ke? Nakasa yafewa kaina kema na kasa yafe miki girman cin amanar da nakeji a Raina kinyimin domin bana mantawa kintaba yimin alqawarin zamu rayu tare zamu mutu tare ya akayi tun Ina raye kika zabi rayuwa da wani bani ba?" Duk da kalamansa sun kashe mata jiki Amma yanayin da take ciki yasata juyowa a fusace tace “qaddara Abdulrasheed dukkanmu akanta muke rayuwa Babu Wanda ya isa ya tayani dakon tawa kamar yanda Babu Wanda ya tayaka Babu Wanda ya taya Ya Kareem Allah madaukakin Sarki ya sardanta ku biyun daka kuna cikin qaddarata kaine kakeja da lamarin ubangiji ni bana jayayya Ya Kareem ma baitaba jayayya ba kullum nunamin yakeyi bayin kansa bane girman rabone da hukuncin Allah saiya Sanya Muneefah tsakaninmu Kuma na dade da sanin tun baya ma shine akan daidai kai kana rayuwa ne a doron son zuciya saboda haka Baffa'am tun da sauran mutuncinka a idanuna ka fice cikin rayuwata kafin na keta alfarmarka na shiga nayi fata² da qimarka Meenah daka sani a baya ba ita bace yanzu yanzun Aminatuh ce a gabanka me taqama da asali kyawun nasaba arziqi da ilimi kada ka manta bayan tafiyarka na samu shahadar zama Barrister Aminah Haroon Moddibo so nasan yancina banason kowa cikin rayuwata ta yanzu" Shigewa tayi daki ta banko qofar ta murda mata key ta haye gado ta zubawa yarta ido tana mata tunanin rayuwarta ta gaba babu bangonta na farko kwanciya tayi bacci ya qauracewa idanunta kamar yanda ya qauracewa idanun Rasheed sosai yake jujjuya kalamanta ya rasa a ma'aunin dazai sanyasu ta fada masa kalamai masu wahalar gogewa a zuciya tabbas shima saida ne daga yanda ta watsar dashi da lamuransa na rayuwa yasan tabbas da gaske ba Meenan daya sani a baya bace, to Amma meye yasa ita ta kasa gane tayi masa laifi me girman daya dace duk hukunci ya dauka akanta? Busar da iska yayi ya gyara kwanciyarsa tare da dauko takardar da Mai Martaba yabashi dazu dazai shigo bayan ya fito daga dakin Meenah yace Kareem ne yabashi yace abashi kafin ya rasu. Tashi yayi ya kunna haske zuciyarsa na bugawa ganin yanda takardar ta bushe da jini ya warwareta ya fara karantawa da larabci yayi rubutun fassararsa kamar haka. _“Assalamu Alaika ya dan'uwa mai albarka na rubuta maka wannan takarda ne a lkcn da Raina yake tafiya ga ubangijin daya halicceshi, badon komai ba saidon inason na qara baka hqr akan laifin da kake tunanin nayi maka na auren matarka Allah yasani ban aureta don cin mutumci ko tozarci a gareka ba, Ni Abdulkareem Mahfuz na zabeka na mallaka maka amanar yata qwaya daya tilo ta zama taka dama nasan takan ce don Allah Abdulrasheed kada kabari Meenah da Muneefah suyi kukan rashina musamman Muneefah ita kadai gareni Kuma na mallaka maka ita halak malak"_ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/23, 7:30 PM] Oum Hairan: Matse takardar yayi a tafin hannunsa jikinsa Yana tsuma zuciyarsa nayi masa wani zugi ya miqe a gadon ya rinqa zagaye dakin nasa a tsarinsa na gaskiya ji yakeyi kamar bazai iya sake zama da Meenah ba yanajin ciwon abubuwan da suka faru a baya so yanzu ya zaiyi da wannan nauyin da Kareem ya dora masa a halin yana gargarar mutuwa? Tambaya ce da yakasa amsawa kansa ita dole akwai sarqaqiya cikin wannan al'amari komawa yayi ya kwanta ya kasa bama kansa mafita sai zafi da zuciyarsa takeyi kawai. Abu daya da yasan ya zame masa dole shine daukar amanar Muneefah da Kareem ya damqa masa to Amma ta yaya zai karbeta a gurin mahaifiyarta bayan yasani yanajin yanda shaquwa take tsakaninsu ko giyar wake Meenah tasha bazata bashi yarta ba, da wannan tunanin ya samu bacci ya dan daukesa da safe yana fita falo ya ishe kowa suka gaisa yanata raba idanun ganin Meenah Babu alamarta hakan ya tabbatar masa tana dakin daya isheta jiya yaja fasali ya dubi Amrah yace “shiga ki daukomin Muneefah" miqewa tayi ta nufi cikin dakin ta tarar Meenah tayima yarta wanka tanayi mata kwalliya ta zauna suka gaisa tace “Big Cele yace akawo masa Muneefah" Bataso ba saidai batada ikon hanawa ta gama shiryata Amrah ta riqema yarinyar hanu suka fito ya dauketa suka fice daga falon Mom tana kallonsa batace masa komai ba, kwanaki bakwai din da Meenah sukayi suna karbar gaisuwa ta fahimci abubuwa da yawa sosai Addah Abulle tayi laushi batada aiki sai kuka tunda ta haifi Muneefah bazata iya cewa ga ranar da Addah ta dauki yarinyar ba sai cikin kwanakin nan da taketa nan nan da ita danma Rasheed ya hanata sakat akan yarinyar duk wani motsin da Muneefah zatayi tana gareshi. Kwanaki goma da rasuwar su Kareem bayan komai ya fara nutsawa Meenah da Kumbo Hami suka fara Shirin tafiya Rasheed baisan me akeyi ba sai a daren da zasu tashi Mom ta kirasa lkcn bai dawo daga yawonsa ba kasancewar har yanzun bai koma bakin aiki ba yana hutune take sanar dashi su Muneefah zasu tafi, Saida yaji wata faduwar gaba yace “tafiya Kuma Mom na zaci sun dawo kenan?" Murmushi Mom tayi tace “basu dawo ba to yanzu haka ma Shirin kaisu airport mukeyi" tana Fadi masa haka ta kashe wayar ta dubi Meenah da hankalinta take kan Sarki junior da yaketa kukan sai yabita itama hawaye ta share tace “makarantarka junior kabari idan akayi hutu zanzo ko na turo a daukarmin kai kaji" daqyar ta rarrasheshi ta samu ta sulale ta shiga mota suka tafi abin mamaki wai harda Addah ayi musu rakiya ashe dama tunda suka rabu da Mai Martaba tayi aure batafi wata biyu ba ta kasoshi tanason Mai Martaba ya dawo da ita dakinta shikuma yaqi. Ko a airport din daqyar aka karbi Muneefah a hannunta tanata kuka so take ta roqi alfarmar abata yarinyar take gani ko ta rinqa samun sauqi Amma tsoro ya hanata furtawa saboda ta fahimci suma dangin uwarta sunason kayarsu da hakadai jirgin su Meenah ya daga sukuma suka juya domin komawa inda sukafi wayo cike da kewar juna. Wannan tafiya ta zamewa Rasheed tamkar famin tsohon miki a cikin zuciyarsa abubuwa sun fara dawo masa sabbi duk da cewa izza da dagawar da Meenah ta rinqayi masa ta girgizashi baitaba tunanin akwai juyin da duniya zatayi Meenah ta rinqa kallonsa watsi dashi kamar tunda Allah yayita batasan anyi ruwansa ba. Wata biyu abubuwa suka zama tarihi akaci gaba da cudawa kamar yanda aka saba kowa yasa abinda

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82