Skip to content

Chapter 67

Chapter 67

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

tabe baki ta mayar da hankalinta ga Mom sukaci gaba da hirarsu tanata dariya abinta shirmen da Rasheed yake buga musu ko Sarki bazaiyi ba suna haka Fadila ta fito ta debesu ta watsar Meenah tayi murmushi tace “Allah Sarki wannan fah Mom?" Girgiza kai tayi tace “au Fadila auren ne yaqi dadi mijin neman mata har ksn gadonsu na sunnah shine tayo yaji ya aiko mata da takarda saki daya" dafe qirji tayi tace “ya salam Abin tausayi Allah ya daidaitasu" murmushi Mom tayi tace “kayyah dai itama Amrah jiya ta koma aure mijin ya qara shine zatayi masa haukanta ya korota uwar mijin tace ita dama batason wannan auren daidai ya nace ne daqyar dai aka sasanta ta koma kayy Meenah munga jarabawa dan ritsin nan " jinjina kai tayi tace Allah yasa ta zamo kaffara amsawa tayi da Amin sunata hirarsu ta yaushe gamo Kareem ya shigo suka gaisa da Mom ya dubi Juhud yace “bansan kin fito ba fah Saida na leqa dakinki naga bakinan" murmushi tayi tace “nazo mu gaisa dasu Mom ne" Miqewa yayi ya nufi part din uwarsa yace “ok ku gaisa sosai Amma ki nemamin abinci yau girkinki nakeson ci....." Rasheed dake tura motar wasan yara shida Sarki ya dago yace “lahhh zaka sammin?" Tsayawa Kareem yayi ya juyo ya dubeshi da tausayawa yace “in kanaso ma kullum ka rinqa zuwa kana karba Aminah ta iya girki sosai" tsalle yayi ya dafesa yace “itama sunanta Meenah nima tawa Meenan ta iya girki nifa tunda Meenah ta mutu ban qara cin abinci me dadin nata ba" Tsayawa yayi kamar zai juyo sai Kuma yasakai ya shige ciki sama² suka rinqa jiyo hargowar Addah Abulle basajin dai abinda suke cewa Meenah ta miqe tace “bari na koma Mom duhun magrib ya fara shiga saida safe" ta juya ga Rasheed daya zuba mata ido tace “Baffa'am Saida safe" daga mata hannu yayi yace “zanzo na karbi abincin naki ai" murmushi tayi ta juya ta fice ta nufi sashinta taji an bangajeta taja baya da sauri tare da cewa A'uzubillahi....." Tana duban Wanda ya bangajeta din Fadila ce qanwar mijinta tayi murmushi kawai ta juya taci gaba da tafiyarta a bayanta taji tana cewa “gayyar na ayyah gayyar tsiya an dawo zaaci gaba da dorawa uwarmu ciwon zuciya jarababbiya qalatacciya da wani shegen cikinki a gaba irin masifa irin maita......" Kalamin sun daketa ta cije lebe tare da tsayawa batare data juyo ba tace “hakane saidai kin manta abu daya bani na liqe mawa dan'uwanku ma shine qalatacce jarababben daya liqemin wlh da zaku bashi shawarar ya rabu dani ma ya dauka da dadi nikaji domin zan yar da qwallon mangwaro na huta da qudaje" Tana fadin haka ta shige tabar Fadila sake da baki lallai yarinyar ta riqa wato sune qudaje Kareem ne mangwaro tab yau da tashin hankali a gdannan, fuuuu ta shige ciki ta nufi sashin uwar tasu tana shiga ta fara karanta mata qarya da gaskiya aikuwa ta hau ta zauna ta dauki waya ta Kira Dada Hanne ta zayyane mata abinda ke faruwa Dada Hanne tace “ai Ni wannan jaraba na rasa dame tayi kama yarinya ta zamewa mutane qarfen qafa an kasa kwanceta a yar shima Mahfuz din kwanaki kamar abin arziqi aikin da mukayi ya fara cinsa yanzu Kuma yaqi kullum abubuwa lalacewa sukeyi" Takaici ya cika zuciyar Addah Abulle tace “ni takaicina ma cikin nan da yake jikinta ashe bai fadaman lissafin daidai ba boyemin yayi yanzu kawai Ina ganinta naganta da tsohon ciki haihuwa kusa" wata uwar ashar Dada Hanne ta qunduma tace “au ke yanzu kina zaune sakarai kika bari tayi ciki kema zaa jorner miki tsiyar?" Da muryar takaici tace “to ya zanyi kefa kika sani na rinqa rabar da kudi tsakanin gurin malamanki dana Hajiya Bilki nidai banga wata nasara ba saita dawowa ta gdannan" Qwafa Dada Hanne tayi tace “ai shegiyar gantalalliyar yarinyar ce masifar taurin kaine da ita bansan wanne irin shiri ne a jikinta ba Amma bari intasan wata batasan wata ba" sun jima suna saqarsu a mugun zare sannan sukayi sallama da shirinsu na cimma matsaya. Meenah kam tana shiga part dinta idanunta ya sauka qasan tiles din taga wani garin magani duk an barbadar dashi kiyayewar Allah ce kawai tasa taga maganin saboda shima arsh ne kalar tiles din, taja baya da sauri tana a'uziyya a fili ta fara dube dube bataga Wanda zata Kira ba ta koma gefe ta tsaya tsam jikinta na tsuma tsoro ya cikata tana nan tsaye Allah ya jefo mata Kareem taja ajiyar zuciya, qarasowa yayi da sauri yace “meye kikeyi anan Kuma?" Dubansa tayi jikinta na tsuma tace “naje zan shiga naga wannan abun" idanunsa ya zuba a tiles din ya na kallon abin ya girgiza kai yace “ki shigo da Bismillah babu abinda zai sameki sai abinda Allah ya hukunta kiji haka aranki".......... Kama hannunta yayi suka shiga cikin gdan ya janyota jikinsa yana sunsunar qamshin gashinta yace “kin wahalar da zuciyata yau" dagowa tayi ta kalleshi yayi mata murmushi yace “kiyi komai ba komai ya lfyr babyna" ajiyar zuciya tayi tace “nima nasani" dariya yayi yace “kuma kina tare dashi?" Kautar da kanta tayi sukaji ana buga qofar suka kalli qofar tare ji sukayi anyi sallama gabanta ya Fadi ta janye yace “ina zaki?" Kallonsa tayi tace “Baffa'am ne ke buga qofar nan fah...." Janyota yayi yace “to me zaki bashi?" Tsayawa tayi tayi sororo sai Kuma ta juya da sauri tace “zan bashi hqr ne yace yau bazaici abincin kowa ba sai nawa" Zama yayi ta bude qofar tana budewa ya shigo yace “ina abincin nawa?" Yana mgnr yana kalle kalle ta kalli Kareem tace “yanzu zan girka maka me kakeson ci?" Kallon kitchen din yayi yace “nima fah na iya girki muje na tayaki nawa ma sai yafi naki dadi" zaro ido tayi tayi dariya tace “habadai aiko Ya Kareem bazan sa girki ba balle kai da girmanka da matsayinka" nuna mata hanya yayi yace “ok aje abani abincina naci na kwanta sallar ma yau bazanyi ba" kitchen din ta nufa Kareem ya tashi yabi bayanta taliya ta dauka ta girkata fara ta tace ta dauko kayan miya ta soya ta zuba kifinta bushasshe data gyara ta dauki hantarta ta zuba ta soya sannan ta zuba kayan dandano ta juye taliyarta ta cakuda a cikin man nan da kayan miya ta barsu suka dahu daidai buqatarta ta sauke. Bata tsaya hada lemo ba ta dauko na kwali ta dora akai ta zuba mawa Baffa'am dinta nasa sannan ta zuba nasu ta fita yana zaune har yanzu Yana karkada qafa ta ajiye masa a gabansa ya dauka ya miqe yace “yawwa na gde" ficewa yayi ta girgiza kai ta dauko nasu ta jera a dinning ta nufi dakinta tayi wanka ta fito ba kwalliya take ba ita dama doguwar riga kawai tasa ta fito ta qwanqwasa dakin na Kareem tajishi yana karatun qur'ani ta bude ta shiga, Saida yakai simuni sannan ya juyo ya dubeta yaja ajiyar zuciya tace “barka da hutawa" jinjina mata kai yayi tace “na kammala" murmushi yayi yace “kin bawa Ya Rasheed din?" Dagansa kai tayi yace “ya tafi?" Ta qara daga masa kai yace “ok

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82