Skip to content

Chapter 69

Chapter 69

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

kece akwai yayarta data dade tana nema a 9ja tabi rugage ds dama domin gano inda zata sameta hakan ya faskara ta tabbatar bayan dogon bincike d ruwan da akakai Rana baffaninki da sukazo suka sanar damu kedin Mayyace sun kwatanta mata inda zata same kakanki harma da bata tsoffin hotunan Kati guda biyu na kakarki wacce ta haifi mahaifinki Aminatuh wadda kikaci sunanta da Kuma na mahaifiyarki, a jikin wannan hoton ne ta fara fuskntar wani abu" Shiru Amrah tayi kana ta dago ta kama hannun Meenah tace “ganin kamanni da yanayi na jininta jikin wadannan hotuna yasata bin duk wata hanya ta roqi alfarmar wadannan baudaddun Fulani su rakata inda zata samo miki danginki ke Saida ta hada musu da qaryar cewa kin cinye mata yayanta biyu ne jin ba abin arziqine zai kaita ba yasasu yarjemata Amma da sharadin zata biyasu ladan bata lkc hakan kuwa akayi suka dunguma ta biya musu kudin jirgi sai Senegal ga mamakin Mom sai taga sun nufi gidan sarkin birnin da suka sauka Wanda yake kakane a gurinta shine ya haifi mahaifinta itadai bata tofa ba har suka isa ciki sunata karbar gaisuwa suka Isa sashin kakarta wadda itace uwargida a gidan ta tsufa sosai tana ganinta tace “yar qaniya ashe kina tunawa da mutane" nandanan labarin isowarta ya cika gdan ta sallami Manga ya tafi masauki bayan anci ansha an huta komai ya lafa mom ta fito da hotunan nan ta miqawa Attajiri Dodda ya karba Yana ganin dayan ya tashi zaune yace “Aminatuh Aishatu Ina kika samo hoton babarki Aminatuh?" Hawaye ne ya zubo masa yace “Aminatuh ta mutu tun baa haifeku ba dama su biyu ns Haifa daga mahaifinki Garbu sai Aminatuh naso riqe dan Aminatuh wato Haruna Amma Ina sun hanani banason zumunci ya mutu na sake Basu auren Aishatu yayarki nidai tun daga auren nan ban sake sanin labarinta ba sunbar inda nasansu sun hanata nemanmu duk da hakan shi Haro yakan kawo mamu ziyara daga baya kuma mukajishi shiru shima bayan yan watanni na tashi yaje ya ganomin ko qalau Haro shekara uku an tafi hudu baizo ya ganni ba shima mukaji lbrn mutuwarsa nayi kukan rashin Haro, babban tashin hankalin sun sake tashi a inda mukasansu Babu Indo Babu dalilinta babu yarsu guda daya tun daga lkcn na baza koma ta a Nigeria neman wannan yarinya saboda naji lbrn baqin fentin da akayi masu ta dalilin kakarta data haifi uwarta Hamida sun zama abin tsangwama ababen kyara wai ana musu kallon mayu"........ Dakatawa tayi ta dago ta zubawa Juhud da jikinta keta rawa ido tace tana Shirin mgn ta miqe da mugun gudu ta nufi cikin gdan Kareem dake nufo sashin ya rufa mata baya tana shiga ta fada jikin Mom ta qanqameta ta rushe da kuka me sauti Mom ta dora hannunta akanta tana Shirin mgn Meenah tace “Ashe kin nemomin asalina Mom kikaqi fadamin kika barni cikin zullumin tunanin ta Ina zan fara nemansu Mom meyesa kikeson boyemin duk abinda ya kamata na sani" Murmushi Mom tayi tace “wato Dana Hana a fada miki Saida aka samu Wanda ya gumtsa miki Meenah tawa yata ta kaina Ni dama bantaba jinki daban da jinina ba kiyi hqr bawai na boye miki don banaso ki sani bane aa na boye miki ne don inason idan kin haihu sai kisan komai na daukeki nakaiki har Senegal da Mali kiga dangin mahaifiyarki ke yar gata ce mu goma ne gurin mahaifinmu biyu sun mutu mahaifiyarki Indo da Abdulrasheed babbanmu Wanda shine yasa mukasa sunan yayanki dan'uwanki Rasheed yanzu saura mu takwas maza hudu mata hudu zakiga kowa zakisan kowa Kakarki mahaifiyar Ummanki Kumbo Hami tace tana tafe cikin satin nan zatazo tayi aikinta tamayi na gayyar sodi balle me dalili"....... Sosai yinin ranar Juhud ta yini da damuwa me gauraye da farin ciki yanzu hankalinta ya tattaru guri daya a baya Baffa'am dinta sunan mataimaki ya Amsa a gareta ya rasa mahadi ya rasa madadi yanzu Kuma matsayinsa ya nunku yayanta ne dan qanwar babarta shin meye sakayyar daya dace tayima wadannan mutane?" Ta rasa mafita ta rasa mahanga amfanin abokin shawara kenan yanzu da ace tanada mashawarci da ya bata mafita. Yini tayi tana safa da marwa a falonta zuciyarta tayi baqi Rasheed kawai ke haskata shine keyi mata yawo a cikinta shaidan Yana raya mata abubuwa da yawa saidai tayi a'uziyya ta kawar da tunanin kawai da haka Kareem ya shigo ya sameta da kula a hannunsa ya zubanta ido yayi murmushi yace “duk kinbi kin takura kanki kwana biyun nan akan abinda baki isa canzashi ba am bama wannan ba wainar fulawa naga Fadila nayi nace Bari na taho miki da ita" zama tayi don tun shigarta da taji Fadilan na cewa tanason yin wainar taji tanaso nutsuwa ta kasa samu da tuni tayi aikuwa ta bude kular sai tiriri takeyi ta mangyada taji lawashin albasa da attaruhu ta hadiyi yawu ta gutsura zatakai bakinta tayi Bismillah kenan taji an tankwabe hannunta tana dagawa taga Amrah cikin hawaye tace “Karka barta taci wannan wainar sun zubanta guba ne don su kashe dan dake cikinta Ya Kareem nayi tunanin lkcn da Addah ta tabbatar da cewa Meenah ba mayyah bace zata sauko ta dawo hanya Amma abin mamaki sai naga dawa ta qara shiga su Hajiya Bilki da Dada Hanne suna zugata, Ya Kareem meye ribarsu idan sun kashe dan dake cikin Meenah sunada tabbacin zaka qara samun wani ne kaida Meenah waye yafi asara tunda ita ko ba komai tanada Sarki junior kaifah?" Tunda ta fara mgnr gumi ke karyowa Kareem tana kaiwa nan bata Ida rufe bakinta ba taji an daki hancinta Addah Abulle tana huci tace “shegiya munafuka nayi danasanin Bari Mom ta shayar dake dana sani Madara na dura miki qila da bakiyi sakaryar zuciyar nan ba ni dama nasan haka zata faru to bari kaji na riga na tsani Meenah tun daga lkcn da tabarka ta auri Rasheed bakuma zan taba sonta ba ban qaunarta ban qaunar jininta Abdulkareem zabi biyu zan baka kodai ka saki Meenah ko Kuma ka dawo da Zahrah idan kaki zabar daya cikin biyun nan zan dagsnka nono nabarka da duniya da macen daka zaba akaina ka gani idan zaka qare qalau kanadai kallon yanda qarshen Rasheed ya qare daya zabeta yabar uwarsa da ubansa shima da takeso kenan bakai dan karere ba da ake maleji dakai a rashin uwa akai uwar daki dakai"................. Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/16, 8:25 PM] Oum Hairan: Tunda ta fara mgnr Juhud ta zubanta ido tana murmushi har Saida ta ida kaiwa qarshe sannan ta tabe baki tace “dama zabi daki kika bashi na rabuwa dani da yafi muku Alkhairi dukkanku dama neman gaba nakeyi banji a Raina zan iya rayuwa ta har abada da danki ba saboda haka ki kwantar da hankalinki saura kadan lkc yazo....." Daganta

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82