Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

rayuwarki ta gaba Aminatu a duk halin da zaki samu kanki a ciki ki riqe maraicinki tabbas Allah zai dafa miki inaji a jikina watarana zai wucce, duk abinda kikaga ya samu shamuwa watan bakwai ne yaja mata baffanki bai rabu da yan'uwansa lfy ba duk da yayi bakin qoqari akansu basu gani ba basa sonki basa qaunarki Aminatu dazu naji sanda suke tattaunawa ba domin Allah sukeson hadaki da dan'uwanki Manga aure ba saboda su cinye dukiyarki ne da tayi saura nikam ba damuwata dukiyar ba damuwata tsiranki da mutuncinki idan kikayi aure a wagga ruga tarihi zaita maimaita kansa ubayenku basason halwar Haro bazasu tsaya miki ba a yayin da Uwayenku suke cewa ni mayyah ce......." Kukane ya kwacewa Innatu ta sake riqe hannun yar tata tace “Wallahi billahillazi la'ilaha illahuwa Aminatu niba mayya bace banida nasaba da maita amma uwayenku sun liqamin tun farkon kawoni wagga ruga taku saboda kawai su quntatani su quntata rayuwata kamar yanda suka quntata rayuwar Baffanki Haruna, na dade ina boyenki wani abu da kika dade kina tambayata yau naji a raina ya kamata na sanar miki koda zai kasance itane kalmata ta qarshe nasan zatayi miki amfani a gaba" Idanunta nakan Innatu dake qoqarin tashi zanne ta matsa ta taimaka mata ta tashi suka kalli juna na tsayin lkc kafin daga bisani Innatu taja fasali tace “zan baki labarin asalin abinda ya wargatsa zumuncin gdanku abubuwa sun faru tun farkon kafuwar wannan Ruga taku wanda kamar yanda na sanar dake kakanku Moddibo Wand'u shine asalin wanda ya gadar da wannan boyayyiyar gabar da ba kowane yasan da itaba" fasali taja sannan ta lumshe idonta taci gaba da cewa. *WAIWAYE* Garin Chadi qasace babba me zaman kanta wadda take da shugaban qasa gomna da sarakunan gargajiya qasar tana dauke da lardi lardi mabambamta wanda fulani suke rayuwa a wadannan gurare, Asalin sunan Kakanku Moddibo Wandu ya samo asali ne daga sunan yankinsu tun asalinsu maihaifin moddibo Wandu ke jagorantar wannan yanke bayan shudewarsa ne aka nada Kakanku Ali A matsayin Moddibon wannan lardi sun zauna a wannan guri na shakaru masu tsayi inda Moddibo ke fita fatauci qasashe maqota kama daga Ghana Senigel Niger Nigeria a wannan yawo nasane Allah ya hadashi da wani gawurtacce bafataken me dukiya mai suna Doda wanda a haife ya kusa haifar kakanku ya kama Moddibo ya riqe hannu biyu idan yawon Fataucinsa yakaishi Senigal a gidansa yake sauka wata tafiya ne da Wandu zaiyi Baffa Doda ya kirashi suka kebe yake tambayarsa Matansa nawa? Cikin mamaki yace masa Matarsa daya da yara biyu Abubakar da suke kira Buba Sai Mamuda wanda suke kira Bangel a wannan lkcn gwaggo Lami bata haihi Ribadu ba. Sunyi shiru na wani dan lkc kafin Baffa Doda ya dago ya dubi Wandu yace “ina iya baka Auren diyata Aminatu?" Cikin farin ciki Wandu ya karbi wannan aure batare da Aminatu ta sani ba wadda take ya ta biyu gurin Baffa Doda kuma ta qarshe kasancewar Allah bai azurtashi da haihuwa da yawa ba yaransa Biyu Baffa Habu wanda ya kasance mahaifi a guri na. A wannan rana akayi komai aka gama Batare da sanin Aminatu ba kwanaki uku tsakani Aka shirya masu kayansu da tarin shanayenta garke guda suka dunguma suka nufi Chad tafiya yau kwana anan tashi anan haka Mahaifina da yar'uwarsa da mijinta sukeyinta har Suka isa Chad. Sarkin yankin na wannan lkc amini ne ga Baffa Doda hakan yasa saida aka fara saukar amarya Aminatu a gidansa akayi biki sannan ta tare a rugarsu. Lkcn da akayi wannan aure Aminatu bata wucce 14 ba hakan yasa sukayita wasan buya da Wandu har tsayin shekaru inda zama yaqi dadi tsakanin Aminatu da Gwaggo Lami, ita Gwaggo Lami batada shanu saita tatsi na mijinsu sannan takai kasuwa ta siyar ta samu na cefane ita kuma Aminatu yawan shanunta yasa bata fita tallen nono yarane da ita da suke dauka mata suke saidawa su kawo mata kudin. Wannan abu yana ciwa Gwaggo Lami tuwo aqwarya gashi ta rasa yanda zatayi da Aminatu ga wata kulawa da Maddibo Wandu ke bawa Aminatu ta musamman kinsan abinka da lamarin maza idan suka auro yarinya wannan abu ya taru ya hadu ya haifarwa da Aminatu baqin a gabadaya rugar domin kowa Bayan Lami yakebi sai ya kasance shikuma Moddibo ya koma bayan Aminatu, kwatsam ana haka sai aminatu ta fara rashin lafiya ana shawara ce basir ne ashe cikine da Aminatu a haka dai ba tare da kowa ya ankara ba har cikin Aminatu ya isa haihuwa cikin dare ciwo ya turnuketa gashi Maddibo bayanan a lkcn ya tafi Nigeria sawo wasu shanaye. Gwaggo Lami tanajin Aminatu tanata nishin ciwo amma taqi ko leqota saida Buba ya fito fitsari yajiyo ya nufi dakin da sauri ya isheta cikin mawuyacin hali a lkcn ta gama jigata kan da ya sawo kai amma yaqi qarasa fitowa aikuwa ya ruga da gudu yaje ya taso wata dattijuwa me suna Suwai suka taho tare kafin kace wannan dakin Aminatu ya cika da mutane amma ko qeyar Gwaggo Lami Cikin ikon Allah ana kiran Assalatu aka samu Aka ciro yaron daqyar Amma Aminatu batasan wake akanta ba gashi jini yaqi tsayawa Suwai tayi iyakar qoqarinta zamani bana asibiti ba amma ina saida ubangiji yayi ikonsa Aminatu bata ko kalli fuskar danta ba Allah ya karbi rayuwarta......... Mutuwar Aminatu ta girgiza duk wani mutum dake rayuwa a wannan ruga hakana aka tashi Manzo ya tafi Senegal ya sanarwa da iyayenta suka taso suka taho tare, tabbas Baffa Dodah ya tausayawa Moddibo matuqa da irin halin dimuwar daya riskeshi a ciki daqyar da qarfin Addu'a ya dawo daidai amma duk da haka daya kalli Jaririn da Aminatu ta tafi tabar masa sai ya kama hawaye kwana sittin da haihuwar jaririn aka rada masa Suna Haruna su Baffa Doda sunso tafiya da Haruna amma Moddibo yaqi yasa musu kuka yana roqonsu idan sun barshi zaike dauke masa kewar Aminatu. Badon ransu naso ba suka tafi sukabar masa wannan jariri hakanan Wannan yaro yaci gaba da rayuwa tun yana tsumman goyo cikin rashin kulawa da qyara indai kinga anyiwa Haro wanka to Dattijuwa Suwai ce ta daukeshi a qarshe ma dole Maddibo barmata shi yayi itake kula dashi da komansa duk da cewa kwana Saba'in da rasuwar Aminatu Gwaggo Lami ta haihu hakan baisa taji tausayin maraici ta bawa wannan yaro nono ba watsin da tayi da wannan jariri yasa shikuma Maddibo ya dauki qaunar duniya ya dora masa komai ya samo na Haro ne Buba dake yarone me hankali kuma ya dan fara tasawa bai damuwa da wannan fifikon hasali ma tausayin Haro yakeji inda Bangel ya taso da qiyayyar haro shima Rubado daya tashi qarami da wannan aqida da uwarsu ta koya musu ya tashi Haro ba mutunne me hayaniya ba wannan tasa ko fita sukayi kiwo sai su kamashi su zaneshi da zarar sunga Buba ya kauce haka zai dawo gda yanata kuka Suwai da Moddibo suyita rarrashinsa. Rayuwa tayita tafiya a haka har suka tasa sukakai munzalin girma Al'adarmu ta fulani yaro yana kaiwa sha takwas akeyi masa aure suyita tsalle tsallensu da matarsa har hankali ya iso musu su rungumi junansu wannan ce ta faru da Buba da

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82