Skip to content

Chapter 72

Chapter 72

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

kusan kullum sai ya kirata da farko Yana bata tausayi idan yana fada mata halin da yake ciki so batason yasa mata kokwanto akan qudurinta ta qudurce ko zatasha wuya zata rayu da Baffa'am dinta shi kadai a mind dinta domin yafi kowa cancanta da ragamar zuciyarta. Bata cikason takura ba hakan yasa sometimes tana ganin kiransa takeqin dagawa musamman data fahimci sosai Kumbo Hami ke fushi da ita duk ranar data fahimci sunyi waya da Kareem, Muneefah nata girmanta kwanci tashi har taci wata biyar da haihuwa lkcn tuni Juhud ta hada iddarta hankalinta ya kwanta tayi wani matsiyacin kyau mai rikita isassun mazaje duk inda ta juya ido akanta yake a daidai lkcn ne Kuma kawai Baffa Garbu ya shirya musu tafiya shaqatawa qasashe biyar don sangarta harda wani bata zabi su hudu zasuyi tafiyar shi Kumbo Hami Naila daya cikin jikokinsa sai ita Meenah da yarta Muneefah. Yanayin yanda suka tsara tafiyar ne yasasu dole Saida suka bi ta Nigeria Kuma ma ba yini zasuyi su tashi ba sai sun kwana biyu qusqus taji sunayi wai zasu barsu a masauki suje Katsina su duba Rasheed daya dawo gida shekaran jiya, ai tanajin haka ta tubure musu kuka baji ba gani dole don basusan bacin ranta suka aminta suka shirya tafiyar da ita tanata murna zataje taganshi tare da addu'ar Allah yasa ya warke sosai tunda suka shigo gdan a mota taji gabanta na faduwa sunayin parking ta daga kanta ta ganshi tsaye saman benen part dinsa corridor din daya zame masa tamkar gurin shaqatawa yanajin nishadin tsayawa a wannan guri musamman idan wani abu na damun zuciyarsa. Suna tsayawa ta zame batare da ta jira sun fito ba ta saba Muneefah a kafadarta ta nufi hanyar shiga part din nasa cikin saa a bude yake ta shiga ta nufi inda zai sadata da corridor din ta haura da sauri fadi takeyi “Baffa'am wayyoh Baffa'am dina miss you too....." Tsayawa tayi a bayansa ta dafa kafadarsa tace “ayyah dai ubana yafi na kowa alfaharina a duniya bama haka dakai fah" juyowa yayi ya kafeta da idanunsa dake cikin glass baqi ya cije lebensa har Saida suka fashi ya kama hannunta ya cire daga kafadarsa ya furzar da iska ya juya yabar gurin, binsa tayi cikin muguwar kidima tana Kiran sunansa baiko juyo ba Saida ya dangana da dakinsa [8/21, 8:19 PM] Oum Hairan: Yana shiga tabisa dakin ya tsaya idanunsa na kanta yace “kije kawai banson hayaniya" dubansa takeyi da yanayin rashin fahimta tace “Ya Rasheed nice fah Meenanka" sake daure fuska yayi ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa yayi murmushinsa na isa da indai yayishi tasan ya shiryawa rashin mutunci yace “eh na ganeki fah Juhud Meenah Aminatuh Mom Sarki junior kinsan nasanki nasan wace ke fiye da sanin da kikayiwa kanki? Koda yake ba abin mamaki bane canzawar mutum cikin qaramin taqi Meenah kiyiwa Allah ki ficemin a daki kada kisa ruwa na ya hau wlh banson ganinki...." Idanunta sosai ya ciko da hawaye ya fara tsiyaya a fili tace “meye nayi maka?" Zaburowa yayi kamar Wanda ta bugawa wani abu yace “zanc...." Sai Kuma yayi shiru jikinsa na Bari yace “ki fice nace da gaske ban qaunar ganinki Meenah kinci amanata kin ha'inceni kin yaudareni kin nunamin Babu wanda kikeso samana ashe qarya kikeyi dama ce kika kasa samu lkcn da kikaga Babu idona kika dauko zabinki kika maye gurbina dashi Abu mafi ciwo wai qanina Meenah Ina raye ki auri Kareem Kuma ki dawo ki fadamin me nace meye zaki fadamin....." Ya qarasa mgnr da ihu ta dago idanunta da tun kafin ya fara mgnr suke tsiyayar da hawaye tace “wlh ba laif....." Dauketa yayi da Mari yace “idan na qara cewa ki fita kikaqi Tabbas gangar jikinki zata riga Rana faduwa Meenah a yanda nakejin tsanarki tsaf ko zaa kasheni zan iya kasheki" juyawa tayi jikinta a mace bata taba tunanin haka daga gareshi ba tayi tunanin kamar yanda take a baya yafi kowa fahimtarta da bata lkc yaji damuwarta ashe yanzun ta canza zani ba haka abin yake ba “to kodai bai gama warkewa ba?" Abinda ta tambayi kanta kenan lkcn da take tafe kamar mahaukaciya zuciyarta na tafasa gabadaya duhu take gani a idanunta batasan inda take jefa qafarta ba. Qara ta saki lkcn data buga kanta jikin bishiya batare data sani ba tayi baya zata Fadi Kareem dayaketa mata mgn tun dazun ya tareta ta fada hannunsa tafi minti biyar komai Yana juya mata kafin duhun ya yaye ta bude idanunta ta zubasu akansa ta janye dasauri tare da gyara riqon yarta tace “tnks" daga haka ta juya taci gaba da tafiya yabita yace “Meenah Ina gurin Aiki akacemin kinzo nazo dominki ki tsaya Mana mu gaisa" hawayenta ta dauke ta juyo ta dubesa kamar zatayi mgn sai yaga ta dago Muneefah ta miqa masa yasa hannu ya karbi yarinyar ya cillata sama yanajin muguwar qaunarta na zaga ruhinsa Wanda ya tabbatar da tasamo asali ne daga qaunar da yakewa mahaifiyarta. Juyowar da zaiyi yaga gurin wayam Meenah har takai qofar falon gdan ya bita da sauri yana kiranta Amma ko juyowa batayi ba ta fada dakin Mom ta zube a jikin Kumbo Hami ta rushe da kuka tace “dama saboda irin wannan ranar nace abarni na rayu ni kadai bazan aure ba aka kasa fahimtata yanzu ga irinta nan Ya Rasheed yaqi saurarona tuhuma yakeyi da naci amanarsa Kumbo wlh banci amanarsa ba ki fahimtar dashi ki zai gane....." Gabadaya hankalin Kumbo Hami ya tashi ta qufula an taba mata zuciyar cikarta daidai lkcn Kareem ya shigo suka kalleshi Meenah ta kawar dakai ya zauna Yana share gumi yace “meye ya faru Kumbo?" Qwafa tayi tace “yo Wagga sakarar yarinya damuwarta tana wucce ta Abdulrasheedu ne komai Rasheed Komai Rasheed aiga irinta nan ga wulaqancin da kika jama kanki nan da kinyi zamanki a Kanon gdan Barrister Kabir aida baisamu damar cin mutumcinki ba" Jinjina kai Kareem yayi yace “ayi hqr Kumbo kinsan halinsa shi dama fahimtarsa ba daidai take data mutane ba ni kaina gaba yakeyi dani a gdannan akan abinda bamu Isa mu canzashi ba Kumbo ya zanyi da rabon Muneefah ne dake tsakanina da Meenah itanma da taqini take kallona a matsayin maci amanar dan'uwa ya zatayi da ita wlh na tabbata inda Mai Martaba bai hada auren nan ba ko ta wacce hanya sai Muneefah ta fita ajikina ta shiga nata Kuma saita haifamin ita tunda haka qaddarar take a rubuce" Shiru ta ratsa ta dogon lkc Kareem ya dago ya dubi Juhud da har yanzu take kwance jikin Kumbo tanata matsar hawaye ya miqe yace “kiyi hqr komai zaizo qarshe Allah shine yasan abinda ke cikin qasa a binne" daga haka ya fice a dakin dauke da Muneefah ya nufi gidansa da ita Zahrah tana ganinsa da yarinyar ta zabura ta miqe ya dubeta ya kawar dakai itama saita waske ya shiga kitchen ya daukowa yarinyar biscuits da yourghut ya zauna Yana bata yana murmushi dadi yakeji a ransa rabonsa da ita tun tana jaririya gata har ta tafi shekara guda ji yake dama ace mahaifiyarta ce a gefensa. Share hawayen daya tsiyayo masa yayi Zahrah na kallonsa tana kada qafa takaici yana qara

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82