Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

shiyasa na zabeta matsayin ranar da zan fara fayyace miki sirrin zuciyata, kafin hakan ki karbi wannan furen ki shaqi qamshinsa nasan zaiyi miki dadi" hannu tasa ta karbi furen tayi jifa dashi tace “na shiga ukuna ni Aminatuh don Allah Ya Muntaz kar kace kanasona wlh Baffa'am kasheni zaiyi dazun saboda Ya Kareem yace yanasona daqyar aka kwaceni a hannunsa...." Batayi aune ba taji ya banqarata baya ya hade bakinsa da nata numfashinta ya dauke ta rintse idanunta ta hada qarfinta ta tureshi daqyar ta miqe tana rarraba idanu yayi murmushi Yana shafa sumarsa yace “nop Ni ba irin baqauyiyar soyayyar nan zamuyi ba sai kinso kosu Ya'isha zasusan halin da muke ciki kawai zan baki damane mu rinqa ware guri muna haduwa har zuwa lkcn da Mai Martaba zaibamu damar yin aure Kinga saimu bayyana kanmu matsayin masoya lkcn babu abinda Big Cele ya isa yayi, to waima da kike wani tsoronsa shidin ubanki ne naga shima aure yake Shirin yi kekuma saiya hanaki jin dadinki akan me?" Wani mugun kallo da takeyi masa yasashi cewa “kinga nifa ba dole zanyi miki ba Amma dai yakamata kisan yancinki a matsayinki na macen da kowa zaiyi burin mallaka....." Tsaki taja ta nufi wajen park din tana fita ta samu napep ta hau ta fada masa inda zai kaita yaja suka tafi sun rigata zuwa gdan suna kallo harda Rasheed ta shigo da sallamarta su Mom ne kawai da Mai Martaba suka Amsa mata shikam Rasheed wani kallo yakeyi mata na tuhuma inda Kareem yakeyi mata kallon tausayi Muntaz kuwa da shine ya shirya komai miqewa yayi zaibar gurin ya iso gabanta yayi mata murmushi ya fice daga falon Ya'isha da Amrah ma miqewa sukayi Amrah ta riqe hannunta suka juya zasu tafi Rasheed da taka musu wata uwar tsawa da saida fitsari ya kusa qwacewa Juhud ya taso a haukace ya zare belt dinsa batare dasun lura ba ya rufesu da duka bai damu da kowa bama kamar Juhud tafi kowa dakuwa tana ihu tana tambayar meye tayi masa Yana cewa tayi masa shiru Kareem ne ya miqe a guje ganin Yana neman illatata ya angajeshi ya dagata ya nunashi da yatsa yace “kar Kuma ka qara dukanta wlh rama mata zanyi wannan ai zalumci ne duk abinma da Aminah zatayi su waye suka koya mata bagasu ba zaka wani zage qwanjinka akanta ita kadai saboda taqamar kanada iko da ita halittarta kayi?" Tana kuka ta qwace a hannun Kareem ta rarrafa ta riqe qafafun Rasheed tace “indai dukan nawa zaisa zuciyarka tayi sanyi Baffa'am ka kasheni don Allah......" Daqyar takai qarshen zancen numfashinta ya kama rirriqewa gabadaya falon sukayo kanta kafin su iso gareta ma tuni ta suma, Kareem ya sunkuceta a guje sukayi waje asibitin dake cikin gdan ya nufa da ita suka karbeta suka shigar da ita wani daki gabadaya jikinta ya farfashe da dukan da yayi mata ruwa suka fara daura mata da Allurai. Mai Martaba ya iso ya tarar da Kareem zaune ya rafsa uban tagumi ya Kira sunansa ya dago idanunsa sun kada sunyi ja Mai Martaba yace “ya jikin nata?" Bai bashi Amsa ba yace “waini meye laifina don nace inason Aminatuh ko Kuma ita meye laifinta da wannan azzalumin zai nemi illatata shiga fah kaga yanda ya farfasa mata jiki Mai Martaba shikenan Kuma don ya kasance uba a gareta saiya takura rayuwarta ya hanata rayuwa da farin ciki ko kuwa laifinta ne qin dawowa da wurin daga mkrnta ita Ina ta sani a garin nan balle ace ita tajasu yawo"........ Jinjina kai Mai Martaba yayi yace “babu komai qarami Yayanku Ni yakejin haushi saboda nace sai yayi aure Kuma na kawo masa Zulaihat nace ita zai aura bazai iya dukana ba shiyasa yake hucce haushinsa akan Aminah zaici qaniyarsa su gama karatun badai cikin satin nan zasu fara jarabawar ba dukkansu inada yanda zanyi dasu kaikuma kaje ka fara shirye²nka na tafiya Saudi na gama maka komai" Gumi ne ya keto masa ya dago duk jarumtarsa Saida hawaye ya ciko idanunsa yace “Auren fah Mai Martaba?" Murmushi Mai Martaba yayi yace qarami kenan kaje kayi karatun rabon mutum baya taba wucceshi indai Nike da ikon badawa nabaka Aminatuh Amma suma karatu zan turasu Kano sai sun gama zanyi musu aure kasan wannan tsarin na gdannan ba baqonka bane don ko yayyanku Fadila da Hamida Saida suka gama degree dinsu sannan na auraddasu" Shigewa yayi ciki yaga yanayin jikin nata ya fito ya nufi motarsa ya shiga ya fice daga gdan. Juhud bata farka ba sai dare sosai Addah Abulle ke jinyarta tayi mata sannu ta daga kai cikin yanayi na jin jiki tace “Addah Ina Baffa'am dina?" Ba Addah ba Ya'isha ma saida ta kalleta taja tsaki tace “uwar me zaiyi miki banza dake kema?" Sunkuyar dakai tayi tace “hqr zan bashi" tsaki Ya'isha da Amrah sukayi Addah tace “bai jima da barin nan ba" bata Kuma cewa komai ba Addah ta taimaka mata ta miqe ta shiga bathroom tayi brush ta fito dake ba sallah takeyi ba suka bata abinci taci ta kishingida Amrah ce ta matso tace “wato Ya Muntaz ba qaramin dan sharri bane muna dawowa Big Cele yace kina Ina shine ya karkace yace ai dayaje makarantar ma bai samemu acan ba muna Dikko Park da samarinmu muna bikin ranar masoya mu da yayi Mana mgn muka biyosa muka taho kekam cewa kikayi saurayinki zai kawoki qiri² ya kitsa Mana sharri zamuyi mgn Big Cele yace duk wacce tayi masa mgn saiya dagargaza kanta"............. *Oum Hairan* [7/19, 9:05 PM] Oum Hairan: *JH013 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki* *Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566* *Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde* Hadiye wani abu tayi me daci a fili tace “Allah yanaji yana gani" daga haka bata Kuma cewa komai ba ta miqe taje ta kwanta ba bacci takeyi ba tunanin sauyin yanayin Baffa'am din nata ne kawai yake addabarta itakam zataje ta sameshi ya fada mata laifinta don ta kiyaye yimasa irinsa a gaba. Da wannan tunanin bacci ya dauketa da safe kafin kowa yazo Kareem yazo tanajinsa tayi likimo kamar me bacci ya qaraci mgnrsa ya fita bayan fitarsa kadan Rasheed din ya shigo daga sallama miskilin baice da kowa komai ba ya gama kalle kallenshi ya juya ya fice Ya'isha ta tabe baki tace “miskili kafi mahaukaci ban haushi" dagowa Amrah tayi tace “wato daga jiya zuwa yau gabadaya Big Cele baya cikin nutsuwa na fahimci ba iyakar Juhud yakejin haushi ba kowa ma fushi yakeyi dashi Kuma kinsan dalili?" Girgiza kai Ya'isha tayi tace “akan mgnr auren da Mai Martaba ya matsa masa yayi ne Kuma yace ya zaba masa Zulaihat kinsan tun da can ma Big Cele ya tsani yarinyar nan kamar masifa Ni bansan azal din data haushi ba da Zabin Mai Martaba ya qare akanta" Tunda suka fara mgnr

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82