Chapter 4
Chapter 4
Bangel buba yanada Sha tara bangel yanada Sha bakwai akayi musu aure Buba aka aura masa Jumme shikuma Bangel Asubi Jumme mace ce me kawaici da hqr itakam Asubi irin mijinta ce sai ya kasance Haro ya tare a gdan Buba komansu tare sukeyi ko shawara buba zaiyi baya shawara da yan uwansa da suke ciki daya saidai Haro saboda nutsuwarsa tasa tunanin manya yakeyi. Rayuwar ta farayi mawa Haro dadi ya saki jiki da Jumme sosai duk abinda ya samo daga Jumme sai Suwai lkcn da shekarunsu suka kai ne aka daura masu aure Lariya itace matar da aka bawa Rubado shikuma Haro aka aura masa ni nima kamar yanda aka dauko Aminatu daga Senegal haka nima aka daukoni aka kawoni jumme ce tayi murna da zuwana ita da Suwai sune suka karbenu hannu biyu surukarmu kam ko kallo ban isheta ba mijina kuma dan'uwana dan qanwar mahaifina Haro ya qaunace ya nunamin kulawa dayake dama ba qarama sosai aka kawoni banyi wannan bambadancin da amare sukeyi ba muka zauna lafiya da mijina a hakanne Jumme ta Haihu haihuwar farko ta haifi Abdullahi wanda kuke kira da Hammah Audi shekaru biyu kuma Asubi ta haifi Rubado basa jana nima bana shiga cikinsu daga asubi har lariya Jumme ce kawai muke mutunci matuqa ana haka na samu cikina na farko nasha wahala sosai da yakai haihuwa Na haifi namiji Umaru ya fara girma sosai yakai kusan shekara uku ya kama qyanda wannan qyanda bata barshi ba saida ta tafi dashi munji mutuwar yaron sosai, bayan rasuwarsa ne harin barayin shanu ya addabi Lardin Wandu babu shiri Moddibo ya debo halwarsa muka dungumo Niger daga niger muka tsallako Nigeria muka samu matsugunni a Wannan guri da ya zama sabuwar Wandunmu" Bamu jima da dawowa ba ciwon Ajali ya kama Moddibo ansha jinya sosai a lkcn da ajalinsa ya rigaya ne yasa aka kira masa yayansa yayi musu nasiha akan zumunci sannan ne ya ware wani kaso me yawa a cikin shanunsa yace wadannan na gadon mahaifiyarsa ne Aminatu daya rinqa kula masa dasu sune sukayi yawa haka, nanfah Bangel da Rubado suka kalli juna sukayi qwafa suka tashi suka fice daga dakin bayan fitarsu ne yake sanar dashi cewa akwai wasu shanun da ya bayar aka tafi dasu kudu kiwo da Buba da Haro ne sukaci gaba da jinyar mahaifinsu har kwana ya qare ya tafi yabar baya da qura qurar da itane kema kikazo kika tadda burbushinta. Maitar da suke iqirari ta fara ne daga lkcn da nake haihuwa yarana suna mutuwa Asubi ce ta fara cewa wai ni nake cinye kayana saida na haifi yara takwas duk suna mutuwa sannan ne Allah ya bamu ke kika tsaya wai ashe duk yaran dana rinqa haifa maza suna mutuwa Ubayenku ne suka sanya hannu kawai saboda tunanin idan Haro ya mutu yanada da Namiji bazasu samu komai ba kedin ma sunso hallakaki Allah yaqi basu dama kika rayu da tsangwamarsu saboda kyawun da ubangiji yayi miki tun kina qanqanuwa dumurmur dake kamar kazar gidan gona saurin girmanki yafi komai bawa mutane mamaki Hasiya da Adama da Baraka duk sa'anninki ne amma duk kinfisu girma ko tallan nono muka tafi kafin akulasu an kulaki sau dari wannan tasa uwayensu sukejin hasaadar hakan akwai wani furuci da Gwaggo Lami tayi kafin mutuwarta watarana mun dawo daga tallen Nono wani Alhajin birni yabaki kyautar Yar dolin wasa (yar tsana) kinzo gda kuka fara fada da yan uwanki akanta har kika fasawa Baraka baki, ina daki ta kamaki ta zaneki sannan tace indai su baraka jininta ne to saita lalataki sai kinyi abin kunya a rayuwarki ko tana raye ko bata raye, badai kyaune yasa kowa yake nannan dake ba to kyawun saiya zame miki fitinar da zata addabi rayuwarki............. *THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566* *Shares Please* *Oum Hairan* [7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* *( Pure love sex nd romantic)* *FP THREE* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *TUNATARWA* Kowa yakanyi maka jaje a lkcn da wani abunqi ya same idan abin farin ciki ya sameka qalilanne sukeyi maka dariya har zuci, kada kasa dariyar mutane a ranka harta rudeka kaji cewa kowa sonka yake masoyin gaskiya shine wanda yake tare dakai a kowanne irin yanayi farin ciki ko akasinsa.🤏🏼 *CIGABA* Inajin ciwon abinda Gwaggo Lami take fada akanki amma ban isa nayi magana ba abu daya na sani shine inayi miki addu'a ki kasance ya ta gari abar Alfaharin iyaye, kwanci tashi girma ya fara zuwar miki komanki abin mamaki ne gabbanki sunada saurin nuna girma hakan yasa tun kina qarama na sabar miki da saka hijjab irin na kanawa, sosai kike ganin tsangwama qyama cikin Yan'uwanki Hasiya Adama da Baraka Amma baki damuwa kodan kin taso kinganmu a cikin wannan qangin ne oho. Wata rana Naje tallan Nono birni na dawo na tarar dake kina kuka na shige daki kika biyoni nake tambayarki meye yake faruwa sai kike fadamin Asubi ce ta bugeki saboda kunyi fada da Baraka tace miki kilakin birni kin bugeta hakanan na hqr bance komai ba ashe mgnr nan har gurin iyayenku maza taje da dare Baffanki yazo yake tuhuma ta wai waye yake zuwa yake siyan nono a gurina a sulluwa (mota) daga birni?" Dagowa nayi na dubesa nace yaron Alh Idi ne da ka hadamu dashi a kasuwa yake zuwa karbar masa nono" numfashi Baffanki ya sauke ya kira sunana na amsa yace “shin Indo kinasa ido akan Aminatu kuwa?" Sake ware injin idona nayi akansa nace “Wai mekake tunanine Haro nikam bangane inda zantukanka suka dosa ba" sake gyara zamansa yayi ya dafe kansa yace “dazu na dawo daga kiwo na Ishe Ribado da Bangel suna tattaunawa naqarasa domin mu gaisa shine suke cemin wai dazun sunga wani me Sulluwa yazo ya dauki Aminatu a mota sunyi hanyar birni" dafe qirji nayi cikin kidima da gigita nace “aa Haro wlh zancene Juhud yau babu inda taje tallanma nice na fita saboda tacemin batajin dadi" jinjina kai yayi yace “shikenan adai qara kulawa" ashe wasan baa fara ba. Tun daga wannan lkcn suka dora mamu qahon zuqa babu dama mutum yazo siyan nono gurinmu sai suce iskanci yazo ba keba nima a haka nake a gurinsu duk da cewa Baffanki baya bawa abin muhimmanci, tsaka da haka Hammanku Manga ya dawo daga neman kudi yaganki ya nuna yana sonki da murna baffanku yazo min da mgnr domin a lkcn duk anyiwa su baraka aure saura ke kadai kin rasa ko matayi a rugarmu dama maqota saboda sharrin maitar da suka liqa mana. Duk da zuciyata bataso ba amma banja ba saboda bansan raayinki ba hakanan baffanki ya nemoki ya tambayeki game da Manga domin shi yace ma kun gama daidaitawa nan kikayi tsalle kikace bakiso naso na matsanki ki karbeshi amma sai baffanki yace tunda bakiso babu meyi miki dole ko bayan ransa hakanan naja bakina na tsuke babu kunya yaje yace da yan'uwansa kince bakison Manga nan suka qara sanya masa tsura ashe dama asali ba manga ne yace yanasonki ba sune suka kitsa masa ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82