Skip to content

Chapter 56

Chapter 56

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

batasan sanda bacci ya dauketa ba wajen biyun dare ta farka tayi alwala ta tayar da nafila tana roqon Allah ya shiga lamuran Rasheed a duk inda yake ya tsareshi da tsarewarsa ya bayyana shi cikin aminci da salama bayan ta idar ta zauna tana lazumi taji wayarta tana ring takai hannu ta dauka lambar Kareem ce taja tsaki ta katse wayar ya Kuma Kira ta dauka zata kashe maganganun Mom suka rinqa dawo mata tayi qarfin halin dorawa a kunnenta Ajiyar zuciya ya sauke lkcn da tayi masa sallama ya Amsa cikin wata irin murya me tsananin sanyi shiru taci gaba da wanzuwa wadda harta sabbaba mata tunanin kashe wayar can taji ya sake jan zuciya yace “nayiwa Mai Martaba mgn game da tariyarki yace nayi miki mgn shiyasa na kiraki a wannan lkcn me kike shiryawa meye plan dinki?" Shiru tayi kamar bazata ce komi ba shikuma yayi kasaqe Yana jiran jin cewarta alamar da yaga na ba mgnr zatayi ba yasashi cewa “ok bakida wani tsari ga dukkan alamu ni inadashi yau Litinin na baki zuwa juma'a ki gama komanki zaki tare a gdanki kici gaba da ibada kamar kowacce mace, ki duba account dinki na tura miki wasu yan canjika Basu da yawa kiyi hqr dasu idan basu isheki shirye²nki ba zanyi qoqarin qara miki insha Allahu" Katse wayar yayi daga haka tabi wayar da kallo cikin mamaki lallai ma Kareem dinnan yana fama da kansa yana fama da bala'i shikam dama ya hqr ya barta anan inda take da yafi musu kwanciyar hankali dukkansu. Qwafa taja ta duba alerting din da akayi mata dazun ta zare ido tare da cewa “wht? Me zanyi da kudaden nan ni Aminatuh 2 millions ta meye ce?" Komawa tayi ta kwanta baccin da bata koma ba kenan washegare wayewar Litinin ta fara shiri don komawa makarata Mom na kallonta batace mata komai ba harta gama shiryawa ta dauki jakarta ta saba tace “mom zan koma school" murmushi tayi tace “da izinin wa?" Kallon Mom tayi da sauri tace “izini Kuma?" Daganta kai tayi tace “mijinki ya kirani da asuba yace kada ki koma makaranta kiyi shirye²nki juma'a zaki tare a gdanki Litinin me zuwa zaku tafi Saudi zai koma can da zama abinda yayi saura na karatunki yayiwa H.O.D na department dinku mgn zaayi bakin qoqari" zama tayi dabar a gurin gumi na karyo mata tace “ni Kuma Mom in bisa Saudi haba Mom don Allah kice masa aa inada abubuwan da sukafi binnasa muhimmaci anan Mom inason in nemi dangina su hadani da dangin mahaifiyata idan naci gaba da zama a haka akwai matsala please Mom kisa baki don girman Allah" Murmushi Mom tayi tace “wannan duk me sauqi ne ni na daukar miki alqawarin bibiyarsu har zuwa lkcn da zaa dace kibani address nasu" sunkuyar da kanta tayi hawaye wani nabin wani itadai bataso ba taso tayi komanta da kanta miqewa tayi ta koma dakinta ta kishingida zuciyarta na zafi haka yinin ya kusan qarewa kiran duniya da yakeyi mata taqi dagawa itafa bayan zafin tsanarsa saboda mahaifiyarsa da tayi harma da ganin rashin dacewar wannan auren nasu duk da tasan ba haramci a ciki Amma wata halal din ta cancanci bari don kunya. Da la'asar tana kwance Mom ta turo qofar ta shigo da sallamarta ita da wata mata Meenah dake kwance ta miqe suka gaisa da matar Mom tace “wannan itace nakeyi miki mgn aurenta na farko yazo a wani yanayi baayi mata komai ba so data haihu an gyarata Amma anja shekaru kusan shekara antafi biyar shine yanzun nake buqatar ki qure fasaharki wajen gyarata ko nawa ne mijinta yace zai biya" suna hirarsu wannan Hajiyan na fito da saiwoyi da magunguna tana yima mom bayani tare da turaruka itadai tabe baki kawai takeyi bata yarda abin gaske ne ba Saida taga an dauki wani qoqo an zuba wani ruwan tsumi an dauko wasu barbade barbade anyi an gwamutsa da danyan madarar shanu wai sun miqo mata tasha. Ta dubi Mom da idanunta daya kawo ruwa zatayi mgn ta kuwa daure fuska tace “aini dama nasan ban isa dakeba Aminatuh nunamin bani na haifeki b...." Da sauri ta karbi qoqon maganin jikinta na rawa ta kafa bakinta ta shanye daqyar tana kakarin amai matar tayi murmushi tace “wannan shi kadai ma idan Tasha na kwana biyar ya wadatar bare zaa hada da wasu tun daga wannan rana Juhud ta bani ta lalace da magunguna wasu tsarki wasu Sha wasu dafawa itadai bakinta har daina tantance dandano yayi cikin kwanakin batada aikin daya wucce kuka. Wayar ma da Kareem ke kiranta ta jefashi a blacklist ko ya Kira baya samunta hakan tasa dole ya qyaleta yasan duk inda yau takai da jimawa gobe tana tafe yanaji a jikinsa wataran wannan qiyayyar zata shude tunda da babu ita daga baya ta wanzu to watarana itanma zaa nemeta a rasa, da wannan tunanin ya tattarata ya zubanta ido akayita shirye²n tariyar tata shine da Mom da Ya'isha da Aunty Hamida suketa digiminsu dakin uwar ango da yan'uwansa Babu me ko lale da bikin hasali ma ko bangaren da ake shagalin basuyi itama amaryar haka saidai idan Mom tayi mata dole sannan take dan motsawa hakana aketa kaiwa da komowa su Ya'isha sune yan jeran amarya har zuwa lkcn Zahrah bata dawo ba aka gyarawa Juhud dayan bangaren kamar yasan zaiyi mata biyu dama tsarin mace biyu yayiwa gidansa bayan sun gama gyarawa sun zubanta duk wasu kayan alatun rayuwa suka kullo suka taho gda sunata yabawa da kudin da Kareem ya narkar a furniture dinta lallai ba qaramin so yakeyiwa Meenah ba. Ta dauki gyaran jiki na ban mamaki abinka da farar fata har wani yellow takeyi yanda Mom ke rawar jiki a wannan bikin ko Rasheed ne ya dawo ba lallai tayi ba ko lalle da akayi mata dishi² ya kama jikinta saboda tsabar gyara hatta gyaran gashi a gda akayishi yin duniya suje gurin gyaran taqi tana maqale a daki kamar wata mara gsky ko yaushe cikin kukan rashin mijinta take da anbarta da wannan damuwar ma da tafi mata fiye da wannan da aka qara mata Ranar juma'ar Mom taga ikon Allah yini Meenah tayi tana kuka tana kiran Rasheed duk dauriyar da Mom takeyi a wannan karon Saida ta kebe itama taci kuka ta gode Allah Mom bata qara tsinkewa da lamarin Aminah ba Saida magrib da Kareem ya turo da motocin daukar masa amarya tunda ta fice a sashin su Mom din aka nemeta aka rasa babu wanda hankalinsa bai tashi ba amarya ta bace da aka fadawa Kareem neman zaucewa yayi ya nufo gdan afujajan suka shiga nemanta lungu da saqo domin sun tabbatar da cewa tana cikin gdan kasancewar masu tsaron qofofin gdan sunce Babu wacce ta fita gabadaya sun gama karade gdan babu dalilinta sai a qarshe Mom tace aje bangaren Rasheed ko can tayi haka Kareem da Mai Martaba suka nufi part din ga mamakinsu suka tarar dashi a bude suka kalli juna babu furuci suka kutsa ciki yayi qura sosai part din haka suka rinqa dubawa can cikin wani daki suka rinqa jiyo shassheqarta har rige² sukeyi wajen shiga dakin sukaja sukayi turus dukkansu ganinta zaune gefen

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82