Chapter 59
Chapter 59
ya zaba ko ita ko ke shikuma yace ya zabi zabin dansa aikuwa tace saiya saketa anso hanashi yaqi ji qarshe yayi mata daya me kyau sannan yace da Kareem yabashi damar rabuwa da Zahrah tunda abin nasu iskanci ne aikuwa tuni ya yankawa Zahrah ticket itama Kinga sai tafi samun sukunin zaman gida" Zuciyar Imani ta Meenah duk sai jikinta yayi sanyi tace “Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Ya'isha wannan ba labarin badawa bane Allah fa shine ya halatta saki Amma bayasonsa nikam banji dadi ba idan Addah bataci arziqin komai ba yakamata taci na yayanta wlh wannan sakin bala'i Mai Martaba ya qara jefani sannan ita Zahrah meye laifinta a ciki najifa ance iyayenta ne suka dauketa bataso tanason mijinta Kuma ko jiya da yazo dakina naga ta kikkirashi bai dagaba haba don girman Allah wannan ba adalci bane bai kamata ba" Tabe baki Ya'isha tayi tace “saiki fada mawa Mai Martaban tunda kinfishi hangen nesa nikam naji dadin hakan ko banza sayi hankali susan ba ko Ina ake shimfida a zauna ba" kashe wayar tayi ta zabga tagumi wannan wacce irin masifa ce daga wannan sai wannan? Bataji tsayuwar motarsa ba saiji tayi ya zare hannunta a kuncinta ya tsugunna a gabanta ya shafa habarta ya dago kanta taja numfashi tace “Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Babu alamun bacin rai a tattare dashi yace “meye kuma?" Kafin ya rufe bakinsa yaga ta balle da kuka tayo qasa ta dora hannunta a cinyarsa gwiwarta na gugar nasa tace “kayimin wannan alfarmar ko ita daya ce a rayuwa don Allah Ya Kareem" da rashin fahimta ya dubeta tayi qasa da kanta tace “ka dawo da matarka dakinta domin Allah. Miqewa yayi yace “ok kinyi sallar Isha?" Girgiza masa kai tayi yace “ki dafamin coffee ki kawomin dakina" ficewa yayi daga dakin ta bishi da kallo wani takaici ya tokareta waishi miji gashi babu damar yin musu yau izzar yakeji sosai batada zabi sai nufar kitchen din da tayi ta fara hada masa coffee din ta gama ta nufi dakinta tayi wanka ta Sanya kayan baccinta ta zura hijjab ta nufi dakin nasa ta qwanqwasa yabata izinin shiga ta bude ta shiga gabanta na faduwa ta kawar dakai tunda take bata taba ganinsa a tube ba sai yau cikar zatinsa kawai abin ka tsaya ka nazarta ne qirarsa ta hutun gaske fatarsa lufluf su ta lura kamar sign na Fam dinsu ne gargasar jiki daga mazansu har matansu. Sunkuyawa tayi ta aje masa ta miqe zata fice ya Kira sunanta ya nuna mata guri ta zauna Saida ya gama abinda yakeyi sannan ya miqe ya nufi wardrobe ya dauki riga yasa yajasu sukayi sallar ya dauki coffee din yanasha Yana kallonta ita Kuma na kallon qasa ganin yanda duk ta takura yasashi cewa “jeki Saida safe" kamar me jiran umarni ta miqe tayi zuruf ta fice ya girgiza kai yana murmushi yace “Meenah kenan" Ya jima zaune Yana tunanin hanyar da zaibi ya samo kanta bai kwanta ba sai 12:00am koda ya kwanta din baiyi bacci ba yanason kasancewa da matarsa Yana tsoron takurawa rayuwarta ko kadan baison shiga rayuwar dan' Adam balle Meenah da take da muhimmaci cikin rayuwarsa hakanan ya kwana Yana juyi shikam bacci me sunan bacci baiyishi ba da safe ta rigasa fitowa ta gyara part din nata ta sauka qasa ta gyara ta koma ciki tayi kwanciyarta fitowa yayi cikin shirinsa na fita yaga ta gyara ko Ina ya girgiza kai ya bude dakin nata tana kwance tana chat ta kallesa ta kawar dakai yace mata “barka da safiya" aje wayar tayi ta miqe tace “ina kwana" shafa sumarsa yayi yace “na tashi lfy Visa dinmu zan karbo gobe da safe zamu tafi nayima Sarki passport Mai Martaba ya hanani shi bansan meye yasa ba" itadai batace masa komai ba ya miqe yace “kina burgeni salonki yana sanyani nishadi nabarki kiyi iyakar abinda zaki iya kafin ki shigo hannuna" Ficewa yayi ta tabe baki ta koma tayi kwance abinta bata tashi ba sai azahar da yunwa ta fafaketa ta shiga kitchen ta samawa kanta abinci ta dawo ta zauna a falon qasa tana zaune taji an bude qofar an shigo ta daga kanta suka hada idanu da Amrah da Zahrah ta miqe tana cewa dasu “Lahh Amrah sannunku da zuwa ku iso mana" wani mugun kallo suka watsa mata Zahrah tace “tun Ranar dana fara ganinki matsayin tsohuwar budurwar mijina naji zuciyata bata karbeki ba ashe kedin masifa ce Kuma bala'i cikin rayuwata Aminah kin kashemin Zainab nikuma nayi alqawarin kashe taki rayuwar sai kinyi nadamar shigo da kanki cikin rayuwar gidana"..........…... Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/9, 7:14 PM] Oum Hairan: Sun jima suna zazzaga mata rashin mutumci banda kallonsu da hawaye Babu abinda takeyi ita qwarin gwiwar ayi mata ta rama ma ba ko yaushe takedashi ba tana tsaye suka juya suka fice Amrah tana cewa banza liqaqqiya ai baki fara kuka ba tunda kika nace Saida kika auri yayanmu muna murna Allah yarabamu da qaya ashe kina manne zaki gane bakida wayo shashasha dake kawai" suna fita ta koma ta zauna ta zuba uban tagumi tana kukanta me cin rai bata ganin laifinsu kanta take dorawa laifi data maqale musu da tayi wani yunquri na samawa kanta yanci da yanzu ba wannan zancen akeyi ba itadai batasan tsayin lkcn data bata ba kawai dai taji tsayuwar motarsa ne ta miqe ta dauke abincin data faraci dazun ta nufi kitchen din ya shigo yabi bayanta da kallo bata juyo ba hakanan yaji ransa bai kwanta da shirun nata a kitchen ba yabi bayanta. Tsaye ya tarar da ita ta kifa kanta a cabinet tanata kukanta me karya zuciya gabansa ya fadi ya fita yabarta qlau ya dawo ya tarar da ita cikin damuwa, matsawa yayi bayanta ya hade tazarar dake tsakaninsu qamshin turarensa ya daki hancinta taja ajiyar zuciya ya sanya hannunsa biyu ya dagota ya juyota ta sunkuyar da kanta ya matsa sosai kanta ya hade da qirjinsa yaja numfashi ya dafa kanta yace “meye ya faru bayan fitata naji a jikina wani yazo gdannan" dagowa tayi ta dubeshi ko fushi Kareem yake fuskarsa a washe take yace “fadamin waye don Allah" kawar dakai tayi ta tureshi ta juya zata fita ya riqo hannunta ya janyota ta shige qirjinsa ya Sanya hannunsa ya matseta Yana sauke ajiyar zuciya me sanyi yace “kiyi hqr don Allah duk da kinqi fadamin meye ya kawo kukan" Sake janyewa tayi zata bar gurin ya riqota ya dagata cak bai direta ko inaba sai dakinsa ya sauketa a gadon ya kulle qofar ya shige bathroom ya jima ya fito daure da towel yana tsane jikinsa har zuwa lkcn kanta na qasa tana wasa da yatsunta bayan ya gama shiryawa ya zauna a gefenta ya riqo hannunta Yana qarewa lallen hannunta kallo yace “yayimin kyau sosai am su Amrah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82