Chapter 55
Chapter 55
tana qara tuna masa tun tana budurwa an hanashi sai yanzu data zama saura ragowa sannan ga rashin asali kalma daya yake fada mata Babu komai Addah inasonta a haka ba meenah ce ta qini ba a farko fin qarfinta akayi saboda hska nima bazan qita ba" idan ya Fadi haka Adda ji takeyi kamar ta kasheshi shima gashi Mai Martaba yaqi sauraronta balle yaji kokenta hasali ma fushi yakeyi da ita wannan tasa ta zare hannunta daga lamarin Kareem din ta zubansa ido tare da cin alwashin indai itace ta haifeshi to Meenah ta gama kwanciyar hankali a duniyarta saisun takurata sun azabtar da ita ita da yan'uwanta babban abinda yake daganta hankali Zahrah yar wanta ce ta nemawa Kareem aurenta don huce haushi yanzun Kuma ya samu abinda ransa yakeso bayama ta ita tunkan tafiyar tayi nisa. Wadannan dalilan suka hadu sukayiwa zuciyar Kareem yawa abinka da mara isasshiyar lfy nandanan zazzabi ya rufeshi shi kadai a gda yayita murqususun ciwo yana dafe qirjinsa wayarsa ma ya kasa dauka ya kira wani, baa Ankara ba Saida ya kwana shidda yana fama da ciwo shi kadai a gda sannan ubangiji ya kawo masa sassauci a galabaice ya lalubi wayarsa ya Kira layin Zahrah bugu yafi biyar tana gani taqi dagawa ya hqr ya Kira na Meenah itanma yayi mata misscall yafi goma tana kallon wayar taqi ta daga qarshe ma ta kasheta gabadaya ya jinjina kai cikin azabar ciwo ya Kira layin Mom dan yasan idan ya Kira na Addah ma itanma kamar yanda matansa Basu saurareshi ba itama ba saurararsa zatayi ba. Bugu daya Mom ta daga tace “dan halak kaqi ambato Ina ka shigene inata nemanka bana samunka....." Nishin da taji yanayi ya fadar mata da gaba tace “ya salam kardai bakada lfy ciwon ne ya tashi Kareem....." Cikin rawar murya yace “Mom....ki....ki taimaka ki kawomin Aminatuh don Allah kada ta zamo silar ajalina sonta zai kasheni...." A gigice tace “o.... Ok ganinan don Allah kada ka mutu Kareem mukam mun shiga uku da wannan masifa" kashe wayar tayi ta zari mayafinta ta fice a kidime ta nufi dakin Meenah tana zaune tana koyawa Sarki Homework ta dago ta dubi Mom tace “Lfy Mom?" Sharce gumi tayi tace ”taso ki rakani unguwa" Babu musu ta miqe ta dauki mayafin doguwar rigarta ta sanya ta kama hannun Sarki suka fito ita kejan motar Mom na fada mata inda zasu tana fahimtar gidan Kareem suka nufa hasken fuskarta ya dauke ta hade rai donma Mom tafi qarfin musu ne a gurinta shiyasa tayi shiru har suka isa gdan suka Mai gadi ya bude musu sukayi parking Mom ta fito itakam gyara zamanta tayi Mom ta dakanta tsawa tace “bafa nason sakarci Meenah ki fito mu shiga nace" Tana qunquni ta fito suka shiga cikin tun daga falon taji gabanta na faduwa komai a hargitse tabi falon da kallo taja tsaki Mom ta haura saman tabi bayanta tana kallon tsarin gdan bude wata qofa Mom ta Kuma yi qofofi ne guda biyu suna kallon juna ga mamakinta nan dinma falo ne sai wasu qofofin biyu tsayawa Mom tayi tana tunanin wacce zata bude Sarki yace “Mom ga dakin Uncle nan" Yana mgnr Yana murda qofar suka shiga a tare itakam guri ta samu ta zauna a falon tana hura hanci. Yanayin da Mom ta isheshi yayi mugun tada mata da hankali ta saki wani kuka tace “innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Abdulkareem meye hakan kashe kanka zakayi a gda kai kadai" gaban Meenah ya sake faduwa lkcn da Mom ta qwala mata Kira ta miqe a razane ta shiga dakin tare da zaro ido Yana kwance a qasa magashiyan cikin wani mawuyacin yanayi ya bude idonsa ya saukesu akan Juhud tare da sauke ajiyar zuciya ya fara yunqurin miqewa Yana cewa “Am.... Ami...na...tuh zo... matso gareni please...." Janyewa tayi tayi baya idanunta na kansa Mom ta tura ta fada jikinsa ya lumshe idonsa tare da sanya hannunsa ya zagayeta yaja wata ajiyar zuciya me qarfi tana qoqarin qwacewa ya bude bakinsa yace “na...na gode Mom ke kadai kike tausayina a duniya Mom Meenah bata sona...." Juyawa Mom tayi ta fice saboda yanda taga Yana qara matse matarsa a jikinsa abin yabata tausayi da kunya ta lura da Rasheed da Kareem tafiyarsu daya Basu da kunya akan abinda sukeso....... Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/7, 7:18 PM] Oum Hairan: *0031* Da qyar ta samu ta janye daga jikinsa idanunsa suna lumshe hawaye yake zubarwa ya riqe hannunta yace “Nayi tunanin kedin me yarda da qaddara ce da hukuncin ubangiji Meenah ashe ba haka bane Meenah ko bazakiji tausayina ki daina azabtar da ruhina don na cancanta ba ya kamata kiji qaina don qaunar da nakeyi miki inasonki ne Meenah da jinina da rayuwata" Yana mgnr numfashinsa ba kakkatsewa hakanan taji bazata iya jure cigaba da kallonsa a wannan yanayin ba ta miqe zata fice ya Kira sunanta ta tsaya ya dauki wayarsa ya miqa mata yace “idan tafiya zakiyi ki kiramin Amrah ko Urwat ko Muntaz wani cikinsu yazo ya zauna dani Ina cikin yanayin da komai zai iya faruwa dani" Harararsa tayi ta fice a ranta tana cewa “badai ni ka zaba ba wlh saidai ka mutu yanda uwarka da yan'uwanka ke qina haka nima nakeji game daku ban shirya zama da wannan ahlin ba abarni na rayu da zabina koda baya tare dani nasan Ina kwance a zuciyarsa" sauka tayi qasan ta tarar da Mom da Dr Razaq suka dubeta tare sukace “ya me jikin" a gajarce tace “yana ciki" ta juya ta fice ta shige mota shiru dogon lkc ya wucce basu fito ba can taga mota ta shigo Mai Martaba ne da Arman suka shiga suka daukoshi suka fito dashi. A mota suka sanyashi suka fice Mom ta shiga mota Juhud taja suka fita sosai ta qular da Mom da halin ko in kula din data nuna akan mijin nata bata taba tunanin zuciyarta tayi soyewar haka ba. Saida sukaje gda ta juya zata shiga dakinta Momy tace “bantaba tunanin hakan daga gareki ba Meenah mijinki zabinki a baya banga zafin da rayuwa tayi tsakaninki dashi ba da zaki zabi azabtar dashi Meenah koda a yanzu baki zabeshi ba cancanta aka duba aka zabanki shi kada kiyi wasa da damarki inaji a jikina Kareem zai sharenki hawaye don Allah Meenah indai da gaske kin daukeni matsayin uwa a gareki kiyima mijinki biyayya ki rintse idonki ki ninka hqrnki akan wanda kikayi a baya. Tabbas akwai qalubale cikin zamanku to Amma qaddara ta riga fata haka Allah ya shirya mana addu'a Rasheed yake buqata kawai daga gareki" Sunkuyar da kanta tayi tana sauraron Mom harta gama fadar abinda zata fada Ta juya ta fita ta kwanta rigingine zuciyarta na hasaso mata abubuwa da dama da suka faru a baya lkc zuwa lkc tana dauke hawaye a fuskarta itadai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82