Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

Babu amo Babu labari. Qa'idar aikin nasu yace watanni shiddan ne gashi sun wucce nan fa Mai Martaba ya tashi takanas yaje barikinsu inda ya dawo cikin matsanancin tashin hankali suna ganinshi Meenah dake zaune ta dora kanta saman cinyar Mom tana aikin kuka ta miqe tana cewa “Mai Martaba kaganoshi Yana cikin qoshin lfy?" Sunkuyar dakai Mai Martaba yayi yana kwance rawaninsa yace “lamarin akwai daure kai fah naje barikinsu duk sojojin da aka tura Togo sun dawo tsiraru ne suka mutu Amma shi bai dawo ba dana matsa da bincike ma a data na aikinsa tun sunada wata biyu da tafiya wani mugun ciwon kai ya sarqeshi shine dalilin da yasa aka bashi hutu da zummar zai dawo gda tsayin watannin nan bai dawo ba....." Yanke jiki Meenah tayi ta fadi qasa sumammiya gabadaya sukayi kanta Mom ta dauko ruwa ta fara yayyafa mata daqyar ta dawo hayyacinta ta miqe zaune ta dubi Mai Martaba cikin gushewar hayyaci tace. “Me kakeso kacemin Mai Martaba mijina ya taho gda daga filin daga Kuma baizo gidaba to Ina ya tsaya Kuma wayoyinsa basa shiga tun satin daya tafi?" Gumi Mai Martaba ya sharce yace “shine abinda nima nake tambaya kada ki tashi hankalinki na sanar da duk Wanda ya kamata na sanarwa wannan isue din Kuma sun fara bincike daga yau insha Allahu komai zaizo da sauqi...." Cikin kuka tace “ta yaya zan kwantar da hankalina bayan rayuwata tana cikin garari nikam don Allah ku fitomin da mijina wlh inason kayana" daqyar suka samu suka lallasheta shima ba shiru tayi da kukan ba kawai surutan ta daina hakanan aka duqufa babu ji Babu gani nemansa ta kafofin sadarwa na Internet da duk wasu hanyoyi da zaa samu bayaninsa Amma shiru Babu amo Babu labarinsa. Gabadaya hankalin gdan sarautar Babu na kwance wannan baqon alkaba'i daya fado musu Babu zato ya girgiza zuciyar kowa a gdan daga yara har manya hatta wadanda ke nuna adawarsu irinsu Hajiya Bilki a zahiri suna nuna alhininsu tare da jefar da maganganu na zargi a fakaice suna alaqanta batan nasa da Juhud da take kwance cikin halin jinya bata kwana uku da lfy saboda tashin hankalin da take ciki duk ta qare sai qasusuwa gashi kullum lkc qara tafiya yake babu wani amon labari tun daga sama ga manyan sojojin da suka baza idanunsu a kowanne lungu na Africa domin ganoshi zuwa gwamnati da itama take hobbasa wajen ganin an samo bakin zaren saidai kullum labarin daya ne baya canzawa daga inda yake. Malamai kuwa da suke aiki da addu'ar Allah ya fito dashi sunfi dari suma kullum amsar daya ce a qara hqr lamarin daya Sanya Juhud a wani hali ga shayarwa gashi ko abincin bata iyaci dole tasa sarki yanada shekara daya da wata hudu Mom tayi masa yayen dole aka dorashi akan abinci aka qyaleta da damuwa daya gabadaya ta quntata kanta kullum bata da aiki daga sallah karatun qur'ani sai kuka Mai Martaba da yayansa maza musamman Kareem daya dawo daga Saudia ya gama karatunsa kullum basa Kano basa Abuja basa Lagos Basu kotono Basu Togo Basu Burkinafaso tafiya kullum qara miqawa takeyi Abu ya tafi shekara guda, watarana suna falo suna zaune Meenah na rungume da Sarki junior Amrah da Fadila suka shigo suka zauna aka gaisa suka jajantawa juna Dada Hanne dake zaune ta rafsa tagumi ta dago tana kallon Juhud tace “lamarin nan da ban mamaki Mahfuz batan Abdulrasheed kamar batan toka a ruwa gsky abinnan da lauje cikin nadi Anya ba mutuwa yaronnan yayi ba" Duk Wanda ke falon Saida ya dago karma Juhud taji labari da kaduwa tasata zamewa daga kujerar ta sauko qasa tayi dabar tana kallon Dada Hanne. Harara ta watsa mata tace “eh Mana biri yayi kama da mutum to nidai tunda abinnan ya faru nake biyar malamai da yan bori idan suka hau bori suka jirge sai suce ai saqale kurwarsa akayi akayi bandarsa" gabadaya hankalin kowa sai ya dawo kan Juhud da itama take jujjuya mgnr a kwakwalwarta Dada Hanne tace “kuma fah cewa sukeyi makusancinsa ne yayi masa wannan abin kawai saboda yanason cin gado to nidai naga kaidai Mahfuz bazakayi wannan abu ba itama Mom din yara bazatayi ba saura da me dama Kuma ku hudune magadan nasa....." Miqewa Kareem yayi yace “don Allah dakata Dada kada kizo Mana da surkullen hauka cikin wannan lamari ke Ina kika taba ganin anyi bandar mutum banda sakarcinku na mata? Kuma ma meye Rasheed ya Tara da har zaayi tunanin kasheshi don gadonsa haba dallah ku rinqa auna mgn kafin kuyita Mana" Yana fadin haka ya miqe zumbur ya dubi Addansa daketa harararsa ya dubi Mai Martaba da Mom yace “wlh daukan alhakin Meenah zakuyi indai kuka zargeta yarinyar nan batada wani abu da ta sani game da batan mijinta haba ai abinda zai yuwu ma dagaji ansanshi" ficewa yayi daga gdan idanunsa nakan Meenah da keta jan zuciya tunda mijin nata ya bata take cikin masifa komai Yana neman koma mata baya gdan an qara tsangwamarta da Mom kawai takejin dadi sai Kareem daya mayewa Sarki junior madadin bsbansa komai ya tarkato Sarki. Ana haka Mai Martaba yaga zaman ya fara tsayi Abu ya tafi shekara biyu ya Sanya Kareem ya nema mata admission bayan sun biya mata an zana mats jamb lkcn da sukayi mata mgnr karatun fir qi tayi tace ita bataso daqyar Mom da Kareem sukasha kanta ta yarda ta fara zuwa Alqalam University Katsina bata jima da fara zuwa ba abubuwa suka fara canzawa Dada Hanne da Alh Aminu suna zuga Mai Martaba baiyi furuci ba Amma gabadaya ya janyewa Meenah tallafi babu Wanda yasan dalili Mom ce taci gaba da dawainiya da karatun nata ita da Kareem. A hakadai da dadi babu dadi take gurgura karatun cike da samatsi da qalubalen rayuwa kullum addu'a takeyi Allah ya bayyana mijinta itama ko ta samu hasken zuciya. Yau da gobe ce tasa Kareem bawa Mom shawarar kama mata hostel saboda karatun nata na Law yanajan kudi sosai hakan kuwa akayi suka kama mata hostel ta koma can da zama Sarki junior na gurin Mom yanata girmansa inda a lkcn Ya'isha ta ta haihu Zahran Kareem ma ta haihu taso zuwa daidai lkcn suna exam hakanan ta hqr sai bayan Exam akayi hutu ta shirya domin zuwa tayi barkar ta nufi Daura cike da kewar gudan jininta da sallamarta ta shiga falon Sarki ya taso da gudu ya rungumeta ta dagashi tana juyashi suna dariya tayi kissing nasa tace “miss you love inata kewarku" Lakace mata hanci yaran me shekaru hudu yayi yace “yaushe zaki dawo?" Narkar dakei tayi tace “saura semester guda Son ka matsu na dawo ne?" Turo baki yayi yace “Addah Fadila ce tacemin na daina zuwar mata gidanta kada na cinye mata su Jabir Momy wai tace kece kika cinye Dad Ina ya bata....." Gwabe bakinsa Mom tayi tace “ba nace maka idan na qarajin mgnr nan a bakinka saina yankaka ba" riqe bakinsa yayi alamun yayi shiru ta daukeshi jikinta a mace ta nemi guri ta zauna suka gaisa da Mom ta miqe tace “zanje nagano babyn Ya'isha" miqewa itama tayi tace “nima abinda ya kawoni kenan hutunmu na sati daya ne Kuma tun

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82