Chapter 73
Chapter 73
kamata tace “waikai yar wace ka dauko?" Murmushi yayi yace bakisanta ba ko?" Tabe baki tayi tace “ya zaayi nasanta tunda baa cikin ahlinmu ta fito ba" sake kallon Muneefah yayi yace “qwarai kuwa baa cikin ahlinku take ba tunda kinada ikon canzata daga jinina Zahrah na dade da fahimtar Ina kika dosa koma dai meye a ranki kibi a sannu domin Aisha itace ya babba a gurina Kuma ko zaki haifi duniya bayanta zasu biyo abu na qarshe da nakeso ki sani a aurenki ma arziqin Meenah kikeci saboda haka ki taka a sannu" Tashi yayi ya dauki yarsa ya nufi hanyar ficewa daga gdan tayi dariya tace “iska kuwa na wahal dame kayan kara wahalalle Meenah dai tafi qarfinka saidai kaganta ka hanga kayi sake dan zaki ya girma me ita ya dawo son maso wani qoshin wahala" Bai saurareta ya tsaya bata Amsa ba ya fice ya nufi wani shop yayima yarsa siyayya ya juya ya koma gdan sarautar har sun shirya suna zaman jiran dawowarsa domin Alh Garbu yace ba kwana zasuyi ba a ranar zasu koma Kano Meenah bataso haka ba taso ta samu cikakken lkcn fahimtar da Baffa'am dinta gskyr lamari Amma batada wannan damar, tana kallonsa Yana kallonta ya dawo daga yawonsa a mota sukayi sallama da Kumbo Hami da Alh Garbu itakam ko kallo bata isheshi ba wani takaici ya cika mata zuciya abin nasa harda wulaqanci juyawa yayi yayi tafiyarsa tabisa da kallo ta girgiza kai ta shiga motar suka tafi tana waiwayensa hankalinta baimakai ga Kareem da yaketa daga mata hannu ba. Suna tafe tana furzar da iska a haka suka Isa Kano goma na dare suna Isa gdan da suka sauka ta shige daki ta kwantar da Muneefah dake bacci ta zauna zaman karatun wasiqar jaki batada mafita ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta bacci ya gagareta sai juyi kawai da takeyi cikin dare ta lalubi wayarta ta fara neman layinsa ta kasa jurewa Kira biyar tayi baa dagaba ta rubuta masa gajeran saqo na ban haquri, tana qara Kira taji wayar a kashe taja fasali ta kashe tata wayar ta zubawa Muneefah idanu tana sharar kwallah Tabbas duk abinda yasa Rasheed daukan wannan matakin akanta ba qarami bane, da wannan tunanin bacci ya dauketa da asuba ta tashi suka fara shirye²nsu domin tashi zuwa Dubai, Tara suka tashi itadai badon tanajin dadin komai ba donma Naila tana dauke mata hankali da dan karen surutunta. Kumbo Hami ta fahimci abinda yake damun jikar tata koda suka isa dinma bata wani saki jiki ba har suka Isa masauki sukayi sallah sukaci abinci sukayi wanka kowa ya nemi makwanci sai dare suka fice daga masaukinsu, suka shiga gari itadai Meenah yaqe kawai takeyi lkc zuwa lkc tana gwada layin Rasheed Amma har yanzu yaqi dagawa har dole tasa ta saduda ta qyaleshi. Sai asuba suka koma gda sukayi sallar asuba suka kwanta rayuwar taci gaba da gudana a haka baqin naci ya hana Juhud daina kiransa shikuma yaqi dagawa kamar yanda Kareem yake nacin kiranta itama tana jizgashi idan abin ya dameta saidai ta Kira Ya'isha tasa mata kuka tace ta tayata bawa Baffa'am dinta hqr saidai Ya'isha tayi murmushi tace “wlh Meenah baqin kishine yake damun Ya Rasheed Amma Ni shaida ce bai daina sonki ba" da haka take dan kwantar mata da hankali take samun nutsuwa. Satinsu biyu suka daga zuwa Malay daga Malay sukayi India daga can sukayi Saudi sukayi Umarah daga nan sukayi Turkey daga Istanbul suka gangaro Nigeria daga Nigeria suka zarce Mali, watanni hudu suka kwashe a yawon nasu suna dawowa suka shiga bikin Naila da Hameen dake abin duka na family ne yayi armashi sosai. Mom ita da Ya'isha da Aunty Hamida duka sunzo tunda sukazo take maqale da Mom tanata zubanta shaqwaba washegari suna gurin dinner Rasheed ya dira a qasar Basu dawo gida ba sai wajen 12:30am suna kowa baccine akansa tana shigowa tana cewa “ni Allah Mom badon kin takura ba bazanje wannan dinner ba gara na kwanta nayi chat....." Mgnr ce ta maqale mata lkcn da idanunsu ya sarqe ana juna ya wani maze tunaninsa zatayi masa mgn ga mamakinsa sai yaga taba banza ajiyarsa ta Kara wayarta a kunne tana cewa “double sorry na shiga yanayine wayar na jakka bansa ka kiraba sai yanz...." Iyakar nan Rasheed yaji ta shige daki yaji gabansa na mugun faduwa ya dubi su Mom da suketa faman dariya ita da yan'uwanta ya miqe zuciyarsa na tafasa yace. “Gobe da wuri zan wucce Ghana ba lallai mu samu haduwa ba" bai jira amsar Mom ba ya fita ya ishe Alh Garbu da fadawansa sunata hira gda kamar kasuwa ya lura suma dabi'ar qasar kamar basa bacci sosai da dare, daquwa Alh Garbu yayi masa yace “dan boko dan qaniyarka shine ka shige cikin mata ga qannenka da yayyaenka da iyayenka duka bazakazo cikinsu ba" yaqe kawai Rasheed yakeyi ya isa garesu ya gaishesu wasunsu da yawa yasansu qannen Mom ne wasu Kuma jikokin gdanne nan aka baje sabuwar hira Nan Alh Sulaiman babban yayan su Mom ya kaikaice yace “Alh dama tun kusan sati uku nakeson yi maka mgn wai ya mgnr yaran nan Najeeb da Ameenah....." Tunda ya Fadi haka Rasheed ya zubansa ido duk da baisan wacce Aminan ake nufi ba Amma yaji saukar saqon faduwar gaba. Zubansa idanu Alh Garbu yayi Yana nazarinsa can yayi murmushi yace “to ai lamarin Aminah ne akwai rikitarwa kaga mijinta na farko ko igiya daya bai yanke mata ba nemansa akayi aka rasa shari'a tabata damar aure ta auri qaninsa shikuma qaddara ta rabasu da saki daya to mijinta na farko din ya bayyana Kuma tanasonsa shima na shaida yanasonta wani dalili ne ya hanashi magantuwa saboda haka indai sunason juna to sunfi dacewa da juna wannan dalilin yasa nace da Najeeb ya hqr wannan abu duk na gidane dashi da Rasheed duk jikokin gdannan ne rashin zumincinsu yasa basusan juna ba" Tunda Alh Garbu ya fara mgnr gumi ke karyowa Rasheed baqin kishinsa ya motsa ya dago idanun nan kamar gauta Yana Shirin yin mgn wayarsa tayi ring ya zaro ya duba aqogo daya na dare harta gota ganin number Ya Arman yasashi tunanin akwai dai wani abu daya faru daga wayar yayi ya Kara a kunnensa numfashi ya sauke me nauyi yace “ina Kareem din?" Huci ya furzar yace “Har matarsa aka kashe ko iya shi kadai ne?" Sake jan numfashi yayi yace “ok zan dawo gobe" daga haka ya kashe wayarsa. Ya miqe ya nufi makwancinsa ya soma safa da marwa Yan fashi sun shiga gdan Kareem sun kasheshi shida matarsa? To akanme?" Tambayar da ya rinqa yima kansa kenan mara Amsa a hankali yaji wasu hawaye sun zubo masa ya nemi guri ya zauna Yana tuno haduwarsu ta qarshe da kalmar qarshe ta Kareem ya fada masa, “Kai dan uwana ne na jini Ya Rasheed a tunanina murna ya kamata kayi da ya kasance nine na kula maka da iyalanka a halin bakanan ba gaba yakamata kayi dani ba! Ya Kareem har gobe inason Meenah bazan taba daina sonta ba har fitar numfashina na qarshe na hqr da Meenah ne badon zuciyata ta hqr ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82