Chapter 53
Chapter 53
Meenah bata zama mallakin Kareem a farko ba hakan bazai zama hujja ta cin mutumcinta ba wlh tallahi Zainab duk ranar da wani abu makamancin wannan ya Kuma faruwa zakisha mamaki na Kuma babu wanda ya isa hanani zartar da abinda nayi niyyah a gobe juma'a zan yanke abinda nayi niyyah kai nama fasa yau dinnan idan da Wanda ya isa ya Hana" Bata fahimci komai ba Amma sosai taji wata faduwar gaba ta darsar mata ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta damuwa tasa zazzabinta na qa'ida ya dirar mata wanda likitoci sukayi ittifaqin zai iya haifar mata da ciwon zuciya saboda Yana yawan kumbura zuciyar tata. Bacci ne ya dan dauketa sama sama kasantuwar ba sallah zatayi ba tanaji ana Kiran sallar Isha a masallacin Fada ta sake gyara kwanciyarta bacci me nauyi ya dauketa batasan meye yake faruwa ba sai ji tayi ana yiwa qofar bugu na hauka ta miqe zunbur tana son tantance dalilin bugun taji muryar Addah Abulle tana cewa “billahil lazi la'ilaha illahuwa indai nice na haifi Kareem bazai taba zama da wannan tsinanniyar yarinyar ba matsayin mata wlh Allah saidai idan na kasheta nima a kasheni" Muryar Mai Martaba taji Yana cewa “bazama takai ga kisan ba kizo ke ki fita a gdannan ki tafi gdan naki uban aure ne na daurashi Babu dalilin fasashi" bude qofar taji anyi ta sake zabura ta zubawa me shigowar ido Kareem ne ya shigo idanunsa akanta itanma shi take kallo ido cikin ido ya mayar da qofar ya rufe ya nufota taja baya da sauri yaja ya tsaya Yana kallonta ya dan saki fuskarsa batare data tsammata ba taga wasu hawaye sun kwaranyo daga idanunsa ya daga hannu sama yace “Alhmdllh Meenah duk da banyi tsammanin zuwan wannan lkc da wuri ba Ina tayamu murnar samun kanmu a sabuwar rayuwa matsayin da naso samunsa a farko ubangiji bai amince ba wato ma'aurata.........." Ai bai rufe bakinsa ba ya tsinceta a qasa warwas yayi kukan kura ya isa gareta Yana jijjigata Addah Abulle ta danno qofar tayo kansu da wuqa tsirara a hannunta ya miqe da sauri ya tareta Mai Martaba da Muntaz suka tayashi riqeta ya damqe kaifin wuqar da hannunsa tana wani kuka me cin zuciya tana cewa “wlh saina kasheta mayya cikin zuri'a ta bazan taba lamunta ba......" Abinda Mai Martaba baitaba yiba yau shine yayi mata allurar yan maza ta motsa abinka da tsohon soja baisan sanda ya saketa ba yayi bal da ita taje ta daki gini ta dawo qasa tana qoqarin tashi ya sake nufarta Kareem da hannunsa keta zubar jini saboda riqon da yayima wuqar ya nufeshi da sauri shida Muntaz suka riqeshi daidai lkcn da Arman ya shigo shima yayi kan Mai Martaba Mom ce da Salman sukayi ta Juhud suka kimkimeta Kareem ya saki Mai Martaba har yanzu kuka yakeyi yace “don Allah Mai Martaba kada kayi abinda kayi niyya ka qyaleta tayi duk abinda da tayi niyya aurena da Meenah ne Allah ya riga ya daurashi babu abinda zai kwanceshi saidai mutuwa ko qaddarar data raba auren Rasheed da ita" Fita yayi da sauri ya shiga motarsa yabi bayan tasu Mom suka nufi asibiti sukayi emergency da ita likitoci suka rufu akanta numfashinta suketa qoqarin saqalowa abin ya gagara faduwar da tayi taja mata shiga doguwar suma, ranar daga Kareem harsu mom Babu Wanda ya koma gda anan suka kwana gurinta gabadaya ya rude hankalinsa yaqi kwanciya Yama manta da lissafin yar jaririyar yarsa da take asibitin itama ta Juhud din kawai yakeyi Muntaz ya tafi gda suka dawo da Hamida da Mai Martaba Addah Abulle bata gdan hankali ma baya kanta balle asan Ina ta nufa. Mom da Hamida ke jinyarta tsayin kwanakin biyar batasan waye akanta ba Kareem ya canza mata asibiti yakai uku qarshe Asibitin Mal Aminu Kano ya mayar da ita acanne suka samu ta fara motsa gabbanta sai lkcn ya samu nutsuwar tunawa da iyalinsa har zuciyarsa nutsuwarsa ta rabasa da tunanin komai sai lfyr Meenah babban tashin hankalinsa da likita yace masa zuciyarta ce take barazanar daina aiki saboda ta cunkusa mata damuwar da tafi qarfinta tunaninsa ta yanda zai fara nasa aikin ya goge mata duk wata damuwa dake buwayar rayuwarta ya sanyata farin ciki kamar yanda ya shirya yi a farko Allah bai amince masa ba burinsa bai wucce Meenah ba cikin duniyarsa gata ya sameta Amma Kuma wasu abubuwan sun danni soyayyarta gareshi tsabar qin da takeyi masa ne yasata shiga wannan yanayin dajin cewa shine matsayin mijinta ko meye dalili? Wadannan tunane²n sune suka sanyashi ramewa cikin kwanaki biyar din. Ranar kwana biyar din ranar ta kama sunan Matarsa hakanan ya nufi Katsinan bashi da wani kuzari dake yasan dama ba taron sunan akeyi ba har zuwa lkcn Zainab sunan yarinyar kenan sunan mahaifiyarsa yasa mata tana asibiti ciwon gendis yayi mata kamun gaske anyi mata juyen jini Amma duk da haka taqi lfy inda likitoci suka tabbatar da a cikin mahaifiyarta ta samu matsala Amma su sun dauki alhakin ciwon kacokan sun dorawa Meenah musamman su Dada Hanne da dangin Zahrah da sukayi tsalle suka dire suka dauke yarsu cewa bazata zauna da Meenah ba shidai daya yakabo yaje ta qare masa, Bai damu ba koda yaje gdan nasa ya tarar dashi a kulle domin ya riga ya shiryawa zuwan wannan Rana a baqin kishi irin na Zahrah ba Meenah data tsans fiye da kowa a duniya ba ko wacce mace ya auro sai anyi wannan rikicin shiyasa baisa abin a ransa ba taje tayita zamanta a gdannasu idan ta gaji ta dawo. Kwanan Meenah bakwai a Kano ta bude idanunta tana kallon kowa daidai a lkcn tunaninta bai dawo ba bama kowa take ganewa ba hakanan ta rinqa rarraba ido kan mutane. Mom sai sannu take jera mata tana binta da kallo da la'asar Kareem ya iso asibitin shida Ya'isha tun daga harabar asibitin ya hadu da Lado drivern Mai Martaba yayi masa albishir din Juhud wani farin ciki da murna daya dade baiyi irinsu ba suka cika zuciyarsa har gudun motarsa ya qara don ya isa gareta yayi parking baikai ga rufe motar ba ya nufi ciki sai Ya'isha ce ta rufe masa motar cikin tausayinsa ko lkcn da Meenah take matsayin matar Rasheed Kareem baya zama cikin nutsuwa muddin tana guri Allah ya jarabceshi da qaunarta gashi Kuma yanzu tasan ba qaramin rikici ya saukowa kansa ba don tabbas Meenan da ba itace yanzu ba batajin zai samu kanta da sauqi duk wannan rawar qafar da yakeyi akanta ba gani zatayi ba tunda bashine a zuciyarta ba hasali ma ita a lissafinta ma Babu aure. Yana shiga bai saurari kowa ba ya nufi gadon da take kwance idanunta a lumshe yaja wata ajiyar zuciya tare da binta da kallo me nuna tsantsar qauna da kulawa yace “Aminatuh" jin saukar muryarsa tayi kamar muryar Rasheed ta kuwa juyo da sauri tare da bude idanunta ta saukesu akansa yanayi mata gizo cancanzawa yakeyi daga Kareem ya koma Rasheed ta kasa gane taqamaiman waye a gabanta. Tun farkawarta bata iyayin furuci ba sai yanzu da bakinta ya bude da furta “Abdulrasheed....." Daga haka ta sake lumshe idanunta ta kwantar da kanta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82