Chapter 64
Chapter 64
nan saiya rikice mata rayuwarsu a qasa mai tsarki ta zame mata wata rayuwa da take bata nishadi tanajin Kareem a ranta fiye da tunani Amma har gobe takasa canza gurbin Rasheed kullum shine cikin tunaninta mafarkinta da dukkan wani motsinta hatta addu'arta ya kwashe kaso mafi rinjaye shidin bashi da tamka cikin rayuwarta bazatayi masa madadi ba. Watansu biyar a Saudi aka dauki azumin watan Ramadhan a lkcn Juhud lfy tayi mata qaranci ita ba ma'abociyar bacci bace Amma baccinta yayi yawa Kareem shine ya fara lura da yanayinta suna kwance da dare ya janyota jikinsa Yana shafa mararta ta riqe hannunsa ya daganta gira ta turo baki tace “nikam Allah ya Kareem zaka sani guduwa waikai baka gajiya da abinga ne?" Murmushi yayi ya zubanta ido Yana lasar lips dinsa yace “kintaba ganin inda mutum ya gaji da dadi ai kullum qari kake nema kinma san me?" Girgiza masa kai tayi ya shafa cikinta yace “baki tunanin komai game da sauyin yanayinki?" Dariya tayi tace “yanzu fah sai kace ciki ne dani ko?" Hade rai yayi kama kunnenta ya murde ta saki qara yayi dariya yace “wato kin mayar dani abin tsokanarki ko naga Sarki junior shekara daya da aurenki kika haifesa nikuma kina neman kaini biyu duk qoqarina" murmushi tayi tace “to abinda bazaka yima kanka ba Ya Kareem meye na damuwa kafa taba aihuwar nan balle kace tsoro kakeji" numfashi ya sauke yace “kawai inason naga yayanmu ne Meenah zanji dadi zanyi farin ciki sosai inasonki shiyasa nakeson zuri'a ta wanzu tsakaninmu nasan ko bana raye bazan goge a mind dinki ba" Shiru tayi masa ya kama kunkuminta yayi mata cakuli tayi dariya ta qanqameshi da haka bacci ya daukesu da asuba ya tashi taba jikinta kawai yayi yaji jikinta zafi zau ya tasheta tayi miqa yace “jikinki zafi" numfashi ta sauke tace “na kwana zazzabi Ya Kareem" wanka yayi itama tayi sukayi sallah suka fita asibiti suka shiga aka bata magunguna tare da yimata gwaje² labari me dadi ga Kareem abinda yake zargine itadai jikinta ya mutu batasan meye dalili ba babu farin ciki Babu baqi a ranta saima hawaye da batasan sanda ya zubo mata ba. Tasbihi da taslimi yayima ubangiji Sarki daya me ikon zartar da komai a lkcn da yaso ya juya gareta ganin yanda take sharar hawaye duk sai ta Sanyaya masa jiki ya kama hannunta suka tafi suna zuwa gda ya dubeta idanunsa sun kada sunyi jawur yace “bakyaso ko?" Girgiza kai tayi da sauri tace “ba haka ban...." Katseta yayi da cewa to mene?" Kuka ta saka ta fada jikinsa tace “babu fah kawai Ina jinjina girma da buwayar ubangiji Ya Kareem meye kayimin da zanqi jininka" ajiyar zuciya ya sauke yajata suka zube ya share mata hawayen yace “ki daina kina sani a tunani kinji" dagansa kai tayi yace “me zakici?" Kallonsa tayi tace “azumin fah" kallon magungunan yayi yace “ok idan bazaki iyaba ki hqr Allah yayi muku uzuri fah Dagansa kai tayi yini sukayi yanata tattalinta da riritata wannan ciki Yana ganin boni komai yagani ya rakito mata kayan baby kuwa abin har yazama hauka abinda ya bata mamaki Mom ce kadai tasan da cikin har yakai watanni biyar a lkcn ne Kuma wani baqon al'amari ya sakosu a gaba hakanan sai taga Kareem yayi tagumi ya tsunduma duniyar tunani idan ta tambayeshi dalili sai yace mata Babu komi Tasha zuwa ta tarar dashi Yana kuka a daki shi daya tambayar duniya sai yace mata Babu komi dole ta zubansa ido a dan ritsin ne Kuma ya kama rashin lfy sosai itadai Saida ta Kira Mai Martaba ta sanar dashi domin an bashi gado baisan waye akansa ba wani abin mamaki daya razana duniyarta ranar da Mai Martaba yazo tana tsaye jikin gadon da Kareem yake riqe da hannunsa tanayi masa addu'a taji sallamar Mai Martaba ta dago da sauri cak ta tsaya komanta ya tsaya hatta da numfashinta lkcn da tayi arba da wanda yake takewa Mai Martaba baya cikin bugawar zuciya tace “Baffa'am!" Kallonta yakeyi da alamun rashin fahimta ta nufesa da sauri tana cewa “Ya Allah Mai Martaba yaushe akaga Baffa'am dina Amma aka boyemin meye yasa akayimin haka ashe akwai abinda zaa iya boyemin game da Baffana....." Tana mgnr tana nufarsa shikam ya saki baki ne Yana kallonta zuciyarsa na wani irin bugawa da mugun qarfi qara waro idanunsa yakeyi yanason ya ganeta ya kasa tana Shirin kai hannunta jikinsa taji yace da Mai Martaba “mai Martaba itan wacece?!" Ba itaba shi kansa Mai Martaba Saida tambayar ta dakeshi ya dubeta yaga tayi mutuwar tsaye hawaye nabin kuncinta bakinta yana rawa alama ta magana takeson yi ta kasa kama hannun Meenah Mai Martaba yayi yace “ki nutsu Meenah Rasheed fah ba qalau yakeba duk duniya Babu wanda yake ganewa" zubawa Mai Martaba ido tayi tace “meyesa aka boyemin bayyanarsa?" Murmushi Mai Martaba yayi yace “akwai hikima cikin hakan yanzun ma banso kikasan da bayyanarsa ba so dandai ya matsa ne saiya biyoni" Zubewa tayi ta rushe da kuka tace “Allah na gde maka daka bayyanamin shi a raye Mai Martaba Amma ya gane Sarki junior ko?" Murmushi yayi yace “ni kaina da zan fita na dawo saiya tambayeki waye ni" zubawa Rasheed ido tayi da yake bin dakin da kallo yace “Mai Martaba shima wannan dakin bansanshi ba shikuma wannan da bashi da lfy waye?" Yana mgnr yanakai hannunsa ga Kareem dake kwance kamar gawa riqe hannunsa Mai Martaba yayi yace “bakasanshi ba?" Daga kai yayi yayi murmushi yace “wani qaninka ne Kareem ja tunasa?" Dafe kansa yayi kamar zai tuno ya dago yace “ok shine wannan wanda mukayi yaqin tare dashi aka sacemu tare aka kaimu Sudan kace sunan gurin ko?" Murmushi Mai Martaba yayi ya dubi Juhud data kwantar da kanta a jikin gadon tana kallon ikon Allah. Likitan ne ya shigo suka gaisa da Mai Martaba suka fita suka barta ita da Rasheed abin yana tsuma jikinta da ruhinta wai gata ga Baffa'am dinta Amma baiko kallonta harkar gabansa kawai yakeyi ta miqe tanajan tsohon cikinta me watanni takwas ta matsa bayansa ta sassauta muryarta tace “Abdulrasheed" juyowa yayi ya zubanta ido tare da dibanta ya watsar hawaye ya sake tsiyayo mata tace “wai da gaske baka ganeni ba?" Daina latsa wayar yayi ya sunkuya ya ciro takalminsa duka biyun ya miqa mata yace “nasan sune sukayi miki kyau to gasunan na baki" noqewa tayi taqi karba tace “meyesa zaka mantani tsayin shekara shidda nakasa cireka a Raina na kasa karbar kowa bayan kai Rasheed ni ban cancanci ka mantani ba....." Saurin ja baya tayi lkcn daya fara kwance tazugen wandonsa gabanta ya fadi tana kallonsa tanajin ninkin faduwar gaba gani tayi ya zare wandon ya kuma cire rigar ya rage dagashi sai singlet da boxes ya nufeta Yana murmushi yace “nifa kinganni banida rowa idan kinason wadannan dinma zan iya baki wlh Meenah ta tafimin duk abinda na mallaka a duniya Kuma kinsan Meenah ta mutu Ina zuwa kogin maliya zan fada ciki na tsunduma tsundum na mutu nima kowa ya huta yawwa ai kema kinsan zan hadu da Meenah acan ko?" Tashin hankali Yana matsarta tana matsawa ya damqo hannunta ta rintse idonta ya damqa mata kayan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82