Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

“uhum inajinki" yanda ya kafeta da idone ya hanata tayi masa qarya hakanan tana hawaye tana bashi lbr sosai ya girgiza dajin lbrnta duk da yagaza gasqatawa yanaso ya gano gsky daga gareta ji yakeyi kamar abinda ta Fadi masa bazai taba faruwa a gaske ba. Yanda take kuka kamar ranta zai fitane yasashi jin cewa duk yanda akayi gsky ta sanar dashi Amma kuwa idan har gaskene tabbas wadannan dangi nata sunkai marasa Imani su kashe mata uba bayan dogon lkc su kashe uwarta sannan itama su rinqa farautar rayuwarta? Miqewa yayi Yana zagaya falon Yana kallonta tsayin wani dogon lkc sannan yaja fasali yace “idan na bincika naji qarya cikin abinda kika sanar dani zansa tsinin bindiga na harbeki tashi ki koma daki ki kwanta dare yayi da safe zansan abinyi" miqewa tayi ta koma dakin ta kwanta tana kukanta mikinta ya dawo sabo yanzu ne ma takejin zafi da radadin rashin mahaifiyarta dama ta jima da sabawa da rashin Baffanta. Tana kwance tanata juyi tare da tunanin rayuwarta ta gaba meye Kuma zai zama mafari cikin qaddararta ta baro rugarsu? Da haka bacci ya kwasheta itadai ta farka taganta saman katifa ansa mata net lkcn data tashi ta miqe ta leqa window gari ya jima da wayewa ta bude qofar bayin da aka nuna mata jiya ta shiga daqyar ta bude pampo ta yi alwala shima don taga inda Christy ta kunna jiya ne tazo ta tayar da sallah tana sallar taji an bude qofar an shigo qamshi ya gauraye dakin, batayi tunanin da mutum a dakin ba saida taji ance "Meenah" juyowa tayi da sauri gabanta ns dukan tara² idanunta ya fada cikin nasa yaja fasali tare da shafa kansa yace “nasa jiya an bincikomin komi game dake a daren jiya rayuwarki tabani tausayi kina buqatar kulawa saboda haka ki kula da kanki kafin na kula dake Ni ba yaro bane ko ban haifeki ba zanyi qanwa ta biyar dake saboda haka naji a Raina zan riqeki matsayin yata ki zama ya tagari gareni zakici ribar hakan sannan zan baki kulawa" Tunda ys fara mgnr take kallonsa da lumsassun idanunta da suke dauke da wani sirri me wuyar ganewa tashi yayi ya matso gabanta ya tsugunna ya dora hannunsa akanta yace “kinsan meye sunanki daga yanzu?" Girgiza masa kai tayi yayi mata murmushi abu mafi qololuwar tsada a gurinsa yace “My daughter" batasan me kalmar take nufi ba hakanan taji tayi mata dadi ta yi dariya me sauti tace “turanci ne fah kaima ka iya turanci?" Murmushi ya sakeyi gsbadaya tausayin quruciyarta yasa yaji duk wata isarsa ta zagwanye akanta yace “ya akayi kikasan turanci?" Murmushi tayi da yasa kuncinta lomawa tace “naji arnaku sunayi na tabe cewa da Baffa'am yakaini makarantar arna nima na iya turanci yacemin idan na shiga makarantar arna to bazan shiga aljanna ba yanzu kaima bazaka shiga aljanna ba kenan?" Dariya kalmar ta bashi ya shafa fuskarta yace “zakiso babanki ya shiga wuta?" Girgiza kai tayi da sauri yayi qasa ya zauna yace “yauwa ni nasan bazaki so ba daughter niba arne bane musulmi ne kawai na iya turanci ne a Port-hacourt sannan Kuma da rayuwar makaranta da yanayin aiki" langwabar dakai tayi tace “inason in iya nima" kallonta yayi da sauri yace “ok maza ci abincinki kizo muje muga likita" Miqa mata kayan abincin daya shigo dasu yayi ta karba shayi ne hadadde me kauri sai bread da dankali ta gyara zamanta ta yagi biredin ta tsoma a cikin kofin yayi saurin riqe hannunta yace “ba hakaba Kinga yanda akeyi" gutsurar bread din yayi yakai mata baki ta karba ya dauki tea din yakai mata ta kurba yace “yawwa haka akeyi. Ci gaba yayi da bata har Saida yaga ta qoshi sannan ya tashi ya shiga bathroom ya hada mata ruwan wanka ya kirata yace “kiyi wanka Bari naje na zabo miki kayan da zakisa" yana fadin haka ya fice ta tsaya ta zubawa ruwan ido itakam wannan ruwan yayi mata yawa a wanka hakanan ta cire kayanta tayi jiqa jiqarta ta fito Yana tsaye yana jera kaya juyowa yayi ya zubanta ido yanajin gabansa na faduwa miqa mata wasu riga da skirt yayi na English sunyi kyau sosai ta karba har yanzu idanunsa akanta suke yarinya ce qarama sosai iyakar hasashensa yabarta a 15 Amma cikar qirjinta tafi ta wata me 20 din saurin furta A'uzubillah yayi tare da dauke kansa da sauri ya sake maida hankalinsa ga shirya kayan yace “kije bathroom kisa kayan" sakin baki tayi tana kallonsa ya juyo yace “ina nufin bayi” sai yanzun ta gane ta nufi bayin tasa skirt din ya zaunawa qugunta dass kamar dama don ita aka haliccesu tasa rigar ta fito tana nade gashinta daya warware. Bata isheshi a ciki ba ta dauki hijjab tasa ta fito falon suna zaune sunacin abinci da Christy da gefen ido Christy take kallonta yace “zan kai daughter gyaran gashi daganan zan kaita taga likita" da sauri Christy tace “kamar kasan nima inason zuwa" Ficewa yayi Yana yiwa Juhud magana da fullanci ta bisa da sauri itama Christy tabisu suks fice daga gdan Juhud ke baya su kuma suna gaba suna yar hirarsu jefi² yayi parking gaban wani babban Shagon gyaran gashi suka fito suka shiga itadai banda kallo babu abinda takeyi zama sukayi yayima madam din bayani wata qatuwar mata ta dauko coump ta nufota tasa hannu zata cire mata hula tayi saurin riqewa ta miqe da sauri tace “kambu tabdi wlh bazaki budemin kaina shedan yayimin fitsari ba" dafe kansa yayi da ace Ya'isha ce ko Amrah da sai ya kifansu mari. Takaici ne fal cikinsa ya dubeta yace “ki Bari tayi miki abinda zatayi miki mu tafi inada abinyi Meenah" yanda yayi mgnr a hassale ya qarasheta da tausasawa yasata sakin hular dogon gashinta baqi data nade tayi acuci dashi ya ware dama ba kitson arziqi bane tufka ce guda daya ba Christy ba da sauran matan dake gurin shi kansa saida tsayin gashinta ya firgitashi tunda yake baitaba gani ba a zahiri gashin har ya wucce duwawunta sai rashin gyara ana fara wareshi qarnin manshanu ya cika Shagon shikam miqewa yayi ya fice don basa ga maciji da manshanu ko kadan. Mota ya koma ranar an kwashi yan kallo duk bala'in Rasheed sai qyaleta sukayi tace bazata shiga dryer ba gutsure mata kai zatayi har wata ce ta shiga ciki a gabanta Amma fir taqi dole sai rabuwa sukayi da ita aka gyara mata farcenta Christy qin yarda tayi ta bude kanta saboda yau ta raina kanta gashin yarinyar ya firgitata saikace Aljana. Bayan an gama musu ya biya kudin suka fito suka nufi gda Saida suka biya aka duba dinkin qirjinta aka tabbatar da lfyrsa sannan suka wucce gida. Suna zuwa ta shige dakinta ta tsaya gaban mirrow tana kallon kanta an gyara gashin nan sai sheqi yakeyi dama abinka da me santsin suma tuke mata sukayi suka nade mata abinta. A iyakar haukan Juhud ta zaci Christy matar Rasheed ce itadai taga kullum suna tare da wasa bata taba kawo wani abuba to tayaya ma zata kawo tunda batasan anayi ba,itadai abu daya data sani Christy bata qaunarta batada aiki sai harararta da kyararta shikuma mijin nata komai

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82