Skip to content

Chapter 76

Chapter 76

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

yake gabansa a gaba Rasheed ya koma aikinsa gabadaya sun ajeshi guri guda a Lagos inda kullum tunaninsa zuciyarsa da ruhinsa yake Mali gashi tun a farkon da abubuwa suka lalace da Meenah ta rinqa kiransa yayi block na numberta itama tayi block nasa koya nemeta baya samunta wannan tasa dole ya nemi sabon layi dal saboda zuciyarsa taqi sabawa da rashin sauraro da jin abinda zuciyarsa take muradi saidai rashin saar da yayi daya Kira sai yaji layukan dukka a kashe girman kansa na masifa ya hanashi tambayar wani cikin yan'uwansa layinta yabari akan cewa idan ya koma yasan yanda zaiyi ya sata a wayar Mom. Hakan kuwa akayi bai iya hqrn wata biyun da yayi niyyar yi a Lagos ba ya dauko hanya ya taho Daura bayan ya huta da dare suna hira da Mom a dakinta tanayi masa fadan zamansa haka yayi murmushi yace “mom kamar akanki nake duk kinbi kin damu nayi aure" jinjina kai tayi tace “to ai Rasheed nidai naga cikar kamalar mutum shine hade kansa da iyalansa guri guda kai Kuma na rasa inda kanka yake kunqi ku daidaita da yar'uwarka Meenah Kuma ka kasa samo madadi jiya ma Baffanmu yakirani yake tambayata akan lamarinka da Meenah ance mata aure tace karatu ance ta dawo hannunka tace har abada kaima ya tuntubeka kayi masa shiru wai meye yake faruwa ne" Goge gumi yayi ya gyara zamansa yace “ni bawai Meenah ce bazan dawo da ita cikin rayuwata ba aa Mom abubuwa ne sun kasa gogewa a mind dina Kuma na fahimci kamar itama ba nine a gabanta ba yanzun" murmushi Mom tayi tace “hakane bakai ba aure ne ma bakidaya bashi gabanta so Amma idan kaje zaku iya daidaita kanku" shiru yayi yana nazartar kalaman Mom tace “zanji dadi idan hakan ta faru Rasheed Meenah tanasonka kanason Meenah ga yaranku guda biyu baikamata ku Bari shaidan ya raba kanku ba babu wanda ya isa cikinku ya canza wannan qaddarar kama godewa Allah da rabon Muneefah bai kasheka ba Rasheed rabon ya mace zafi gareshi shiyasa kullum yanada kyau karinqa yima kanka addu'ar Allah ya rabaka da auren mace me yayan wani a cikinta duk son da kake mata idan rabon nan ya yunquro to sai dayan biyun ta faru kodai a rabu ko Kuma a mutu" Jinjina kai yayi jikinsa ya qara sanyi abinda Kareem yayita qoqarin fahimtar dashi kenan ya kasa fahimta yau kam ya gane Kuma ya fahimta wayar Mom ya dauka ya fice daga dakin nata ya shiga mota ya nufi gidansa ya shiga ciki Saida ya dangana da dakin baccinsa ya cire kayansa ya fada bathroom yayi wanka ya dawo ya kwanta gabadaya dakin manyan hotunansa ne shida Meenah saina yaransa Sarki da Muneefah ya zubawa hotunan idanu a fili yace “lkc yayi da yakamata da dawo da farin cikina" wayarsa ya dauka ya Kira Abokinsa Kamil suka gaisa yace masa “cikin satinnan kana free ne?" Amsawa yayi da “eh" yace “ok zamuje Mali ne jibi" bai boye masa komai ba khamil yayi dariya sosai yace “tsohuwar zuma kishin ya gushe kenan?" Ya lura tsiya ya shirya yi masa don haka ya kashe wayar ya dauki ta Mom yanabin contact din ya lalubo number ya danna kira lkcn tana sallar Isha Muneefah ce tana wasa da wayar ta danna tana gwarancinta yayi murmushi yace “daughter bakin yazo kenan?" Nan sukayita shirmensu da yarinyar bayan ta idar ta karbi wayar tunaninta ko Muntaz ne ko Urwat tace “surutu ke gareta Mamana bata rabo da rigima" ajiyar zuciya yaja a hankali taji ya sauke numfashi yace “hakan yanada kyau ba lallai tayi kamar na Mom dinta ba" qamewa tayi a gurin jin muryar da batayi zato ba nandanan ta rinqajin zuciya na ayyana mata ta kashe wayar tana Shirin gimtse layin taji yace “ranar juma'a idan Allah ya amince zan shigo qasar ki fara Shirin zama amarya domin bazan kwana a garin nan ba saidake matsayin matata kamar yanda yake rubuce a allon qudura duk wanda yayi karambanin shiga wannan gonar ma saiya fice da kansa ko Kuma dole ta fitar dashi" Murmushi tayi tace “tunaninka ne yake baka hakan nikuma inajin a raina qaddarata tayiwa taka nisa Ya Rasheed so don Allah kada mu wahalar da shari'a kayi zamanka a inda Allah ya ajeka idanma matsuwa akayi nayi auren naji zan fitar da miji tsakanin yau da gobe Amma kaikam nagama aurenka" murmushi yayi yace “au haba da gaske Kuma kikeyi? To ai kin manta da Abu daya ni idan nayi niyyar aiwatarwa yuwuwa yakeyi Meenah badon kanki da kaina ba don rayuwar yaranmu nayi niyyar abinda na furta saboda haka kada ki manta gyarane kawai Amma kedin matata ce domin da igiyar aurena uku akanki aka jingine aka dauranki wani.... Oh God banaso nake tunawa fah ki share kawai sainazo"....... Daga haka ya gimtse wayarsa yabarta da sakin lebe lallai wannan yazo da izala mara gemu dole ta takansa birki don bataji a ranta wannan tatsunniyar zata yuwu ba. Ranar kwana tayi tana jujjuya kalamansa da safe kuwa bata sanar da kowa ba ta shirya nata ya nata ta gudu gidansa Aunty Kharimatu batare da kowa yasan inda ta tafi ba Kumbo Hami ta riga tasan me ta gudarwa saboda sunyi waya da Mom a haukan ma da takeyi tuni magana taje ga kakanta ya Kuma amsa har anyi duk abinda zaayi an wucce gurin da sahalewar Mai Martaba. Tana zuwa gdan Aunty Kharimatu suka lalace da hira har dare tayi kwanciyarta dake mijinta matafiyi ne washegari ma sukaci gaba da harkokinsu har magrib batada niyyar tafiya suna falo suna cin dambum nama sukaji sallamar Jabir gabanta ya Fadi ya shigo yanayi mata dariya yace “girman kujera aunty babba kinada baqi a waje fah" harara ta zabga masa tace “munafuki suwa kak debomin?....." Bata gama rufe bakinta ba sukayi sallama suka shigo idanunsa na kanta ta kuwa hadiye fara'arta ta hade rai ta miqe ta nufi wani daki suka dubi juna shida Khamil sukayi murmushi suka zauna Aunty Kharimatu nata zolayarsa fadi takeyi lallai ango kasha qamshi ashe da gaske kana tafe" Shafa sumarsa yayi Yana cire hularsa yace “wlh Ina tafe nazo na dauke matata mu tafi nagaji da zaman gwaurontaka" harararsa tayi tace “aa kuwa baka isaba wannan abu Babu shiri nifa sai dazun Kumbo ke fadamin Shirin da akayi nace halan ma waccan uwar taurin kan bata sani ba don ko dazun Saida tace batada muradin wani aure" numfashi ya sauke yace “tasan komai ai dama barinta nayi ta huta saboda rayuwar batada tsayi Amma an fuskanci qalubale da suke buqatar dogon hutun brain"........... Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta baney ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/27, 9:03 PM] Oum Hairan: Dariya Aunty Kharimatu tayi tace "ah lallai to ubangiji ya kade fitina ya daidaitaku sai aje ayita hqr koda yake tsohuwar zuma ce Babu wani qalubale qalaunku zaku zauna wuyarta ku daidaita kanku......"

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82