Chapter 58
Chapter 58
zan karba balle Kuma ya kasance dadaddiyar addu'ata ce ubangiji ya amsamin tare da tabbatarmin da ita kamar mafarki so ni a tsarina bana jayayya da duk abinda nasan ba ikona bane, Meenah a baya kema haka kike saboda kedin dalubata ce bansan meye ya sauyaki ba kinga inada maganganu da yawa da nakeso mu tattauna da zasu zame mana mafita Amma farko don girman Allah badon halin Abdulkareem kici abinci muyi sallah wlh ko Isha banyi ba saimu zauna" Yanayin magiyar tasa tasata dole ta dauki Naman takai bakinta yaji dadin hakan sosai ya miqe ya shiga bathroom ya dauro alwala lkcn daya fito ta gama ya tattare ya fita da kayan ya dawo ya isheta a bayi tana brush da alwala, abin sallar ya shimfida yajasu sukayi Isha sukayi nafila raka'a biyu ya sanya hannunsa ya dafa kanta ta zame zata miqe ya miqe ya riqeta tare da matseta a jikin bango ya fara karanto addu'o'insa cikin larabcinsa me Sanyaya jiki sunkai 10 minutes a haka sannan ya saketa yana binta da kallo har zuwa lkcn bata daina dauke hawaye a idonta ba miqewa yayi ya dagata ya zare mata alqyabbar jikinta ya sake ware lafayar jikinta tana tureshi tana komai ta durqushe da sauri yayi dariya wai kunyarsa takeji Meenah da lkcn data fara period shine mutum na farko daya fara sani shima a lambu ya isheta tanata kuka wai taji ciwo daqyar ta fada masa yayi mata bayani. Sautin dariyarsa ce tasata dagowa ya zauna tare da daganta gira yace “ashe kinajin kunyata Meenah yaushe kika farajin kunyana?" Harara ta galla masa yace “ko a jikina ki kwana kinayi yanzun dai Bari na barki ki kwanta ki huta abinki Saida safe" ficewa yayi yaja mata qofa tabisa da kallo tare da miqewa tayiwa dakin key ta haye gadon tayi kwanciyarta badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta damar tunanin abinda yake damunta. Batasan lkcn da bacci ya dauketa ba a sama ta rinqajin ana taba qofar ta miqe tana miqa tare da yin salati tace “wayene?" Cikin sanyin yanayinsa na dabi'a yace “kinyi sallah ne?" Bata bashi Amsa ba ta nufi bathroom ta watsa ruwa ta dauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga ta tayar da sallar bayan ta idar tayi azkhar ta sake zubewa a gurin duk da ba wata hidima tayi a bikin ba tanajin gajiya a jikinta sosai, bacci ne ya sake dauketa bata farka ba sai 10:30pm shima din wayarta ce taji tana ring baqon layine ta Kara a kunnenta yace “barka da safiya ki fito kinyi baqi" Miqewa tayi tasa rigarta ta bude qofar ta fito Sarki ya rugo da mugun gudu ya rungumeta ta dagashi daqyar tana dariya yaron yace “Mom jiya nayita kuka daban ganki ba ashe gdan Uncle kika dawo nima na dawo nan" murmushi tayi tace “surutu dai kazo ka dameni ko" tsuke fuska yayi zaiyi kuka Kareem ya matso ya karbeshi yace “ba tun jiyan nace kazo mu taho ba kace kai bazaka tafi kabar Mom dinka ba to yanzun fah zaka taho ko shima aa?" Da sauri ya daga kai yace “eh" Mom dake tsaye tayi dariya tace “aikam baka isaba yaro muna tare aurena dakai mutu ka raba" kuka ya saka Yana cewa “nin...Ni Mom banasonki kinmin tsufa ni gurin Mom dina da uncle zan dawo" Dariya sukayi dukkansu ta nemi guri ta zauna Hamida tace “jikin yayi sauqi kenan tunda na tafi nakasa sukuni dake na kwana a raina" sunkuyar dakai tayi ya miqe yace Mom me zaa kawo muku gdan namu bai gama tsaruwa ba Hajiyan sai yanzu ta fito" kiransa Mom tayi tace “kazo kayi zamanka bama buqatar komai tun jiya da sukaje suka sanar dani halin da ake ciki na kasa sukuni shiyasa nazo naganku yanayin Alhmdllh komai zai wucce insha Allahu Meenah hqr zakiyi da abinda Allah ya hukunta, Aminatuh nice na haifi Rasheed Amma bazanyi shaidarsa kamar yanda zanbada shaida akan Kareem ba kin samu miji na nunawa saa daya tamkar da dubu idan kin kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo qarshe ita rayuwa kowa da irin tasa jarrabawar Babu me taya wani dakon kayan da ubangiji ya qulla masa dole shine zaiyi dakon kayansa rabon dake tsakaninku me qarfine Allah ne kawai yasan adadinsa saboda haka kuyi hqr da jarrabawarku" Kallon kallo sukeyi kowa da abinda keyi masa yawo a ransa Mom ta miqe tace “Inason mgn dake Meenah miqewa tayi tabita suka haura saman dakin baccinta suka shiga Mom ta zauna a gefen gadon ta kama kunnenta tace “ki kiyayi shiga haqqin Kareem kawaicinsa da kararsa ta game kowa zai iya zubanki ido akan duk abinda yaga baki da raayi koda kuwa shi zai cutu hqrnsa abin jinjinawa ne shiyasa yake wahala idan ciwo ya ganshi don Allah kada ki zama silar wargatsa masa rayuwa kinji" Kwantar da kanta tayi a cinyar Mom tana shassheqar kuka ta dauko wasu turaruka masu qamshin gaske na humra da na wuta tace muje a jerasu a show glass din fita sukayi suka jera ta fito da wani garin magani ta dauko danyen nonon raqumi ta barbada a ciki ta miqa mata tace “shine yayi saura da jiya kikaqi sha duk yanda kike tunanin fitinar Rasheed Kareem yafisa saboda akan hakan har so akayi a raba aurensa da Zahrah kwanakinsa bai qare ba yanzu Kuma gashi zaki zauna ke daya da sunyi hqr ma sun barta ta dawo da kin samu sauqin wani abun don Allah banda rowa Meenah shidai abinnan in kin hanashi ma ba ado zakiyi dashi ba Kuma ba kwanaki zaa qara masa ba idan wa'adinki yayi shima nasa yayi please a kula don Allah" sosai Mom ta rinqa bata shawari a fakaice saida taga ta dan sake sannan sukayi musu sallama suka tafi shima ya fice a gdan ta shiga bathroom tana wanka ta jiyo wayarta tana ring batabi takanta ba Saida ta gama shirinta tsaf sannan ta dauka number Ya'isha ce tabi suka gaisa tace “ya amarci jiya tsohuwar zuma ta motsa Ya Kareem an kwana ana zikiri" dariya mgnr tabata tace “waiku don Allah meye yasa kuka bawa abinnan muhimmaci ne haka" Dariya Ya'isha tayi tace “mahadin rayuwa kenan gulma nazo yi miki" gyara zama tayi tace “aike dama indai anga kiranki to gulma ke cinki meye zaki fadamin" gwauron numfashi ta sauke tace “wato bantaba sanin Addah Abulle jahila bace sai jiya iliminta baya mata jagora kamar yanda yakeyiwa danta jiya Mai Martaba Yana zagaye bayan an taho kawoki ya nufi bayan gda ya isheta ita da Dada Hanne suna qusqus Dada Hanne nabata shawarar kawai tunda duk bugunsu yaqi tasiri akanki to su dora miki jinya yanda shi Kareem din zai gaji ya koreki sannan su sanyawa kowa qiyayyar ki a zuciyarsa ta yanda ko kin dawo gdannan Babu me karbarki Ina kaiki sun gama tattaunawar nan suna daga ido sukaga Mai Martaba da Ya Muntaz shine Mai Martaba yayi musu wani warning mai kama da daukar rai har yana fada musu daganan zuwa shekara goma idan kikayi ciwon kai saiya hanasu kwanciyar hankali ke sosai fah akayi rikici qarshe dai Addah Abulle tace da Mai Martaba tunda har ya nuna mata ita ba kowa bace akan danta to saidai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82