Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

inda ya tauyeta ya tsarenta mutumcinta fiye da yanda ma ya tsare nasa, ranar da biki ya watse aka kai amare gdajensu washegari su Kumbo Hami suka shirya tafiya Juhud har tafi Mom shiga damuwa da tafiyar tasu da anyi mata mgn sai hawaye lkcn da taga sun kusan gama shiryawa sulalewa tayi tabar gidan ta koma sashinta tasa Rasheed a gaba da kuka wai ita bataso su tafi. Murmushi yayi ya shafa kanta yace “ke har yanzu yarinya ce Meenah to yanzu Kuma kawai saboda bakison su tafi sai su zauna? Kiyi hqr idan kika haihu zan dauki dogon hutu zan kaiki garinsu nima rabona da Mali nafi shekara ashirin" da haka ya samu ta sake har sun shiga mota Kumbo Hami ta fito ta kama hannunta hakanan takejin yarinyar a jininta tace “kici gaba da hqr mijinki Yana sonki Ni shaida ce Meenah idan Allah yasa watan hsihuwarki ya kama da rai da rayuwa zan dawo ni zanyi miki biqi kinji jikata" dariya tayi itama tayi dariya suka tafi suna dagawa juna hannu tana kwance bisa kafadar mijinta. Taso rakasu airport fir yaqi saboda yasan idan taga tashinsu tsaf zata rikice masa, suna komawa kuwa ya fara hadansu kaya ta dubesa tace “yada hada kaya?" Dubanta yayi yaja numfashi yace “tafiya muma zamuyi" komawa tayi ta kwanta yaci gaba da aikinsa bayan ya gama yazo shima ya kwanta sukaci gaba da soyayyarsu sai biyar na yamma sannan sukabar gidan Muntaz ne yakaisu airport suka daga zuwa Enugu. Sun sauka da dare suka samu motar taxi takaisu masauki suna zuwa ta kwanta zazzabi ya rufeta Saida ta kwana uku tana kwance yana jinyarta har ta samu ta samu sauqi sukaci gaba da rayuwarsu gwanin dadi. Aikam tana ganin qauna da soyayya ririta cikin nan yakeyi kamar me, lkc ya rinqa turawa cikin nata Yana qara girma komai yanayi mata wuya shine yake yi mata komai kafin ya fita hatta abinci daya barta ta girka gara yaje ya siyo musu, October watan haihuwarta ya kama tsakiyarsa suka dungumo suka dawo Daura kwanansu uku kuwa da dawowa Kumbo Hami ta dira a Daura sunyi murna sosai sunata farin ciki kwanansu uku ya tafi ranar daya tafi kuwa cikin dare ciwon naqudar na gaske ya tashi. Wayyoh anci wuya matuqa kwana tayi ta wuni tana naquda har Saida suka yanke shawarar ayi mata aiki sun gama komai sun shiga da ita ubangiji ya kawo mata sauqi cikin taimakon Allah ta sunkuto qaton danta namiji wayyoh farin ciki gurin Mom da Mai Martaba da Ya'isha hatta Muntaz yayi murna da wannan haihuwa kwananta daya a asibitin aka sallameta suka dawo gda Kumbo Hami na kulawa da ita shikam gogan saboda farin ciki har kuka yayi gashi bayada damar dawowa bama ya qasar Yana sauka aka turashi Africa ta kudu. Ba Shiba ita kanta taso ace yana kusa yaga dansa yasa masa albarka hakanan dai akaci gaba da hidindumun haihuwar wani abin mamaki babu wani daga bangaren Addah Abulle daya leqo barkar wannan haihuwa lamarin ya bawa kowa mamaki itako Meenah batasa a ranta ba balle abin ya dameta domin ba iyakar su kadai bane duk Wanda ke gdan sarautar Babu Wanda ya leqo musu barka tasan saboda itane Kuma tariga tayi forget na komai dazai sanyata damuwa dane dai ta haifi abinta Kuma ubansa da shaqiqan danginsa suna murna da zuwansa duniya. Duk wani gata da maijego yar gata take samu Meenah ta samu samansa Babu abinda zatacewa surukarta da Mai Martaba sai gdy domin shima ya taka rawar gani gaya a wannan haihuwa, duk abinda uba yakeyi shine ya dauki nauyi donma komai na buqata Rasheed ya tanadi abinsa sai dan abinda baa rasa ba Kuma ya zuba mata kudi masu kauri a account dinta ko zata buqaci wani abu. Ranar kwanaki uku ne suna zaune da Mom da Ya'isha da Aunty Hamida a falo Juhud na feeding din babynta ya kafeta da ido qurr yana qare mata kallo suna dariya Kumbo Hami tana cewa “wannan ja'irin yaron quiya zaiyi tun yanzun Yana qarewa uwarshi kallo da shegen wayonsa aka haifesa" itadai saidai tayi dariya kawai. Sallama akayi a bakin qofar suka daga kai suka kalli me shigowar Hajiya Bilki ce ta shigo ita da Dada Hanne babbar yayarsu Mai Martaba Mom ta taresu fuska a washe tana musu sannu da zuwa ta basu gurin zama Dada Hanne ta tabe baki tace “ashe an haihu?" Da yanayin rashin jin dadin tambayar Mom tace “eh wlh yau kwana uku" tabe baki sukayi Dada Hanne tace “eh tun ranar aka fadamin shine dai yau na daure nace Bari nazo Ke Bilki bani ruwan qanzon nan" dukkansu kallonta sukayi ta miqa hannu ta dauki yaron a cinyar Juhud tana harararta kawai ta bude bakin yaron ta dauki ruwan zata dura masa Meenah ta miqe da sauri tayi kukan kura ta warce danta Dada Hanne ta kuwa dauketa da mari tace “kutmar ubancen ke dan uwarki ni zaki qwacewa yaro a hannu koda yake ba banza ba dama anfada ance indai da abar a jikinki bazaki Bari a karyawa danki ba gashi kuwa munga alama to wlh baki Isa ki bata Mana zuri'a ba dolene abawa yaron nan ruwan qanzon nan Kuma daga yau an daina bashi wannan baqin nonon na tsiya a nema masa Madara ko abawa Fadila ta shayar dashi shidai Rasheedun da kwadayin farar fata da kyauwun banza yakaishi ya dauko to ta qare masa akansa...." Tana qoqarin fusgar jaririn Juhud ta qara qanqame abinta ta saki wani kuka me sauti tace “wlh bazaku kashemin daba duk abinda zakuyi saidai kuyi....." Mom ce ta karbe da cewa “Dada Ina ganin mutumcinki ki fita daga lamarin halwata kafin na hada dake na tsince muku zarafi yaran nan daga ita har mijinta basu damu da lamarin kowa ba ku kun damu dasu to waima Ina ruwanku da abinda ta Haifa ne ince dai nasu ne su suka Samar da abinsu ke yanzu bakiji kunya ba gotai gotai dake kizo kina yada girma gaban jikarki" Hayayyaqo mata Dada Hanne tayi tana cewa eh dama Mana dole kice haka Aisha ai kinci kin qoshi mun kaiki matsayin da baki takaba a baya to dake da Mahfuz da Rasheedu da duk wani Wanda yake yaruwa a gidannan a qarqashin darajata yake balle wannan yar galaulawar da kuka kwaso kuka manna Mana saboda haka wlh muddin Ina raye Kuma Rasheedu daga tsatson sarki Waziri ya fito to dole ne a bani dannan mu karya masa maita takanas nayi tattaki har Kankia na karbo wannan maganin don tseratar da ahllinmu daga gurbacewa irin maita ai bala'i ne bazamu sake a lalata Mana halwa da son zuciya ba" Hajiya Bilki ce ta cafe da cewa “yo Dada Hanne da kike wannan mgnr jinki zasuyi ne ko zaa barsu su gane me kike nufi da gatan da kikeson yi musu ne ai anriga an lashe kurwas basuda katabus hatta Mai Martaban bashi da fuss indai akan wannan tsintacciyar magen ala qaqai dince kina gani fah saboda a samu a ceto yaron nan nabawa Alh Aminu shawarar yafadawa Mai Martaba tunda yaqi Hidaya ga Dijenan babu makusa in batafi ba bazaa fita ba ya aurawa Rasheed Amma yaron nan ya debemin albarka ta

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82