Skip to content

Chapter 47

Chapter 47

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Sanya kayan a mota Mai Martaba ya iso gurin yace “ya subhanallah meye Kuma hakan Ina zaka?" Juyowa yayi idanunsa sun kada sunyi jawur ya dubeshi ya kawar dakai Alh Aminu ne ya matso shima lkcn Rasheed din ya koma cikin gdan ya figo hannun Meenah ko dankwali Babu akanta Mai Martaba daya fahimci barin gidan yake niyyar yi yace “wai ba mgn nakeyi maka bane" a fusace ya juyo yace “banaji Mai Martaba banji abinda kaceba ka kauce kabani guri yau kam ko baku koreni ba na gama zaman gdan sarautar nan akan matata zan iya hqr da komai....." Muryarsa ce ta sarqe ya jefata a mota ya kulle har yanzu kuka takeyi yama kasa rarrashinta ya sake kallon Alh Aminu ya nunasa da yatsa yace “ka sanar da munafukar matarka ni Abdulrasheed nafi qarfin yayanta a aure kun bani Zulaihat banaso na karba Allah ya dubeni ya kasheta kun bani Hidaya na sakar muku kayarku shine yanzu zaku liqamin bazawara kwancen wasu saboda kun Mai dani jani talau waima ni kadaine da namiji ne a gidannan Ina Salman Ina Arman Ina Kareem Ina Muntaz hatta Urwat kukayiwa aure zama zaiyi da matarsa saini akanme zaku sanyawa rayuwata idanu ne banaso na fada muku banaso wlh tallahi zanci mutumcin duk ubanda ya qara tunkarata da mgnr aure auren banza auren wofi da har zaku sanyawa matata tsura akansa aiba ita ta hanani ba nine naga batada tamka bare mahadi, Abu na qarshe ka fadawa Bilki ta kiyayi dawowata gdannan Kuma ta shirya Amsa Kira kotu saita fadamin uban wa matata ta kashe da take fadawa duniya cewa in mutum ya cika rabar Meenah saidai yajishi a Ramin kabari?....." Sosai Mai Martaba ya girgiza da yanayin Rasheed din yasan tabbas yau yakai qarshe akwai gagarumar matsala idan yabarshi yabar gidan dama Meenah ce zatake kawoshi tunda shi dama asalinsa bayada ra'ayin zaman gdan sarautar to ya dauke abarsa meye Kuma zaisa suganshi? Mai martaba na Shirin mgn Mom ta iso gurin ita da wasu mata su uku dole tasashi yin shiru ta kama hannun Rasheed tajashi gefe sun jima suna bugawa kafin ta shawo kan kayanta Yana kuka kamar wani yaron goye daqyar ta lallabashi ya yarda zaibar Meenah a gidan sarautar Amma da angama biki da ita zai tafi. Zuwa tayi ta fito da ita a mota ta janye mata sumar data rufe mata fuska tana ganin Mom din ta fada jikinta ta sake rushewa da kuka itama hawaye ta share tana tausayawa rayuwar Meenah Babu uwa Babu uba babu shaqiqin dan'uwan da zata zanta dashi taji dadi ga rayuwar taqi mata dadi wata murya taji ta bayansu tace “kiyi hqr Aminatuh komai yayi tsanani sauqi na zuwa hakanan Allah yake jarabta bayinsa zababbu domin ya gwada imaninsu ba sonki ne bayayi ba qaunace ta kawo miki hakan bantaba ganin Wanda akayiwa irin wannan qazafin ya qare rayuwa a wulaqance ba ko baizama wani ba zai samu yardar Allah" Juyawa tayi ta zubawa matar idanu gabanta ya yanke yabada wani rass ta janye jikin Mom da sauri tana qara kallon matar tare da langwabar dakai a rayuwarta nata taba ganin kamar tsagin Kara irin wannan ba kama haske da jiki inda kasan innatun ta a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace “mom wannan fah?" Dadine ya cika mom ganin ta fara warewa tace “Wannan Kharimatu kenan qanwata ce babanmu daya daga Mali suke ita da Mamanta Hamida kinganta can" juyawa tayi ta kalli dattijuwar matar da tayi tsufan jin dadi fatar nan kamar a matsa a tatsi jini tana sanye ds farin tabarau tayi mata murmushi ta bude mata hannu ta fada jikin matar hakanan takejin wata nutsuwa na ratsata da kwanciya a jikin Kumbo Hami Kumbo Hami ta shafa kanta tace “kiyi hqr jikata zakiga ribatai a gaba munci wannan baqin cikin nida babbar yata Aysho tana jaririya a tsumman goyo aka koremu daga gdan babansu Aishatu surukarki......" Kuka ne ya qwacewa Kumbo Hami ta share qwallarta tace “saboda qin jini da yanayin qabila wannan abu yake bibiyarmu kamar garin Bodde wani babban garine da yake cikin Qasar Mali So garin yazamo kamar Biddah a Nigeria sunyi qaurin sunan asiri da maita Wanda ba dukkan garinne suke da wannan hali ba su masu yinma sune kaso mafi qanqanta. Baffana attajiri ne a garinmu a zahiri bama maita bama tsafi Amma saboda dukiyarsa yasa ake cewa shine shugaban mayun garinmu Baffa Garbu wato babansu Aishatu surukarki yaron babana ne hakan yasa yabashi aurena tunda nazo garin lkcn baa auro uwayen su Aishatu ba matan gidan suka tsangwamin Kuma Allah dabawa mugu dama haka akayita rashe rashe a gabar tun baa yarda har suka amince da gaske ni mayyace hakanan na haifi Aysho ranar dana haifeta Garbu bayanan uwarsa tasa aka daukemu akaje bayan gari aka yasar damu daqyar na iya komawa Mali daga Senegal naci gaba da rainon Aysho Garbu nasona Amma bashida ikon dawo dani domin babana ya fusata hakan yasa Aysho nada shekara goma ya karbeta a gurina sai labari naji ya auradda ita ga dan qanwarsa ya taho da ita Nigeria tun daga wannan Rana nakebi akaini inganta nakasa samun dama dakaina nazo Nigeria neman Ayshatu na ban dace ba a qarshe dai nama hqr domin jikina na bani Ayshatu bata raye don da tana raye inni ban nemeta ba ita zata nemeni, bayan na rasa Ayshatu ne qulafucina da son naganta yasa na komawa Alh Garbu shine har na sake haihuwar Kharimatu, Aminatuh yanzun komai ya wucce bayan ansha wuya kema idan kikayi hqr watarana zai wucce"........... Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/2, 6:36 PM] Oum Hairan: *0026* Jinjina kai Juhud takeyi da jin wannan rikitaccen al'amari tabbas duniya ta cika da mutane marasa tsoron Allah saidai kayi fatan Allah ya dada maka Imani kawai, dubanta Mom tayi tace “Kumbo Hami itace ta riqeni tun bayan rasuwar mahaifiyata banida uwar data fita a duniya Meenah" sosai Meenah taji dadi da ganin dangin surukar tata hakanan taji tanayi musu wata qauna me game jini suma sosai suke nuna mata qauna da kulawa sun jima sosai a sashin nata sunata hirarsu gabadaya su anan suka qarashe bikinsu basajin Hausa sosai hatta Rasheed fullanci yakeyi musu wannan tasa Juhud sajewa dasu. Kwana uku aka dauka ana bikin qofar falo Rasheed hana Juhud zuwa yayi da sunan biki to itama bata matsa ba ganin Mom ta goya masa baya a gdanta tayi nata bikin saidai tasa ta cire kawai idan yaga garara mutane sunwa bangaren sauqi yasata a corner yayita hadanta aiki ta rasa a wanne bigire zata aje Rasheed irin mazan nan ne masu jarabar nacin masifa shi indai zaki dagansa qafa to bakida matsala dashi idan har kaga Yana ciccin mazu to ya nema anyi masa rowa ne. Tunda ta fahimci haka itakuma taci alwashin kozata wahala indai ya nemi haqqinsa zata bashi domin shima Babu ta

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82