Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

qirjin Juhud yake dukan tara² aure Baffa'am dinta zaiyi?" Maimakon taji tana farin ciki sai taji ta cika da tausayin kanta a hankali tasa hannu ta share hawayen daya gangaro mata ta yunqura ta tashi zaune cikin dakiya da nuna jarumta tace “a tunanina uba kamar Mai Martaba bazai taba yima dansa Zabin dabai dace dashi ba banga aibin Aunty Zulaihat ba da kuketa mgn akanta ni sainaga ma ta dace da mijin nata zasu dauki kala sosai Ina ganin muyi musu fatan Alkhairi yafi tsayawa wannan surutun da kukeyi Kuma ma Ni banji araina don wannan Baffa'am yake fushinsa ba kawai dai nice na bata masa" Qwafa Amrah tayi ta fahimci duk yanda zakaso daka ganar da Juhud bata ganewa garama ks qyaleta a cikin duhun da take, Addah ce ta shigo musu da abin karyawa suka karya aka sallamesu suka tafi gda ranar bataje makaranta ba yini tayi a kwance da tsamin jiki bata da aiki sai murdo ruwan zahi a hitter ta gasa jikinta da yayi rudu² abinka da jar fata, abinda yake bata mamaki tun ranar da Rasheed yayi mata duksn mutuwar baya yarda su zauna guri daya da yaga ta fito yake tashi yabar gurin itakuma tsoro ya hanata ta tunkareshi ta fahimci neman abokin mutuwa yake shiko Kareem kullum qara fito mata da salon qaunarsa gareta yake baya boye soyayyarsa a gaban kowa sai gaban Rasheed shima don ya fahimci baya happy da lamarin ne. Sun shiga jarabawa gadan² kawunansu sun dauki chargi matuqa musamman Juhud data Hana kanta sakewa da farko sunci gaba da zama suna lesson da Kareem tunda ta fahimci duk lkcn da suka zauna Baffa'am din nata zaita zagaye a gurin Yana qwafa yasa dole ta hqr ta janye ta koma yiwa kanta lesson da kanta tanashan wahala Amma saboda baqin nacinta taqi ta hqr hakanan take tursasa kanta, ganin hakan yasa Mai Martaba ya siyo mata tamfatsetsiyar waya Infinix hot 10 yabata tare dayo mata download na manhajoji na bincike da zasu taimakawa brain dinta taji dadi sosai ranar yini tayi da farin ciki a ranta tanajin itama ta faso gari su Ya'isha sa daina daga mata kai. Da magrib Mom da tayi tafiya zuwa qasar Mali garin babanta ta dawo tana falo anata kwasar gaisuwa Juhud ta fito sanye da wata baqar doguwar riga me matuqar kyau da daukar idanu tana danna wayar da aketa Kira tun dazun ta qarasa gaban Mom tayi kissing hannunta tace “wlcm Mom munyi missing naki long time kin manta damu" murmushi Mom tayi tace “me sunan Yaya kina burgeni jarabawar nan da alamun bata baki kashi dadi tayi miki kinyi wani fresh dake kamar auduga sabon toho" da murnarta tace “alhmdllh Mom dama rashin lesson ne yake wahalar ni Kuma Mai Martaba ya sharemin hawaye ya siyamin sabuwar waya ya saukemin manhajoji ina samu Ina karatuns cikin kwanciyar hankali raba dare nakeyi Ina karatu sai biyun dare nake nafila na kwanta da asuba da Dora da karatu kafin kowa ya tashi ns tsinci abinda na tsinta. Jinjina kai Mom tayi tace “lallai Mai Martaba yanaji daku sosai kuna sha'aninku muga wayar taki" miqa mata tayi ta fara dubawa tana dariya tace “aa kaga barrister Aminatu Haroon Moddibo wadannan zafafan hotuna haka" rufe idonta tayi tana dariyarta me daukar hankali Rasheed dake zaune ya miqe saboda hakanan idan ya cika kusanci da yarinyar yanzu yake rasa nutsuwarsa har ya taka step na farko ya juyo yace “Meenah" gabanta yabada wani rass ta dago da in....Ina tace “na...am Baffa'am" hadiye wani yawu yayi yace “ki kawomin wayar nan zan duba wani abu ki hadomin da abinci" Babu wanda ya kawo komai tace “to Baffa'am" ta miqe ta shiga kitchen ta dauka abincin nasa ta dawo ta karbi wayar ta nufi saman a bude ta tarar da qofar hakan ya bata damar sakai tare da sallama yana tsaye yanata kaiwa da komowa shigowar tata yasashi tsayawa ya harde hannunsa a qirjinsa ya zubanta ido tayi saurin kawar da kanta saboda baqin kwarjininsa baya bata damar Sanya idanunta a cikin nasa. Tsugunawa tayi ta aje abincin cikin ladabi ta dago ta miqa masa wayar ta miqe zata fita har ta murda handle din taji ya Kira sunanta da wata irin murya data sanya tsigar jikinta tashi taja ta tsaya ta kasa motsawa daga inda take qirjinta yana duksn Sha hurhudu, bai tsammaci juyowarta ba hakan yasashi takawa a hankali ya isa bayanta ya zubawa mazaunanta da faffadan qugunta idanu yanajin sautin bugun zuciyarsa da ya zame masa jiki game da ita yana qaruwa. Hannu yasa ya murda key din qofar ya zare tare da hadawa da kyawawan dogayen yatsunta data qawata da baqin lalle me ratsin ja ya riqe a cikin nasa ya juyo da ita ya hadata da qofar yana qara rage girman idanunsa akanta a hankali yace. “Haqiqa ko a tarihi bantabajin lbrn yar da take neman zabar duniya fiye da babanta ba Meenah abubuwa da dama suna bani mamaki na yanda sama da wata guda kikayi watsi Dani a gdannan ko arziqin gaisuwa bana samu daga gareki kawai saboda Ina qoqarin karenki mutumcinki ko?" Hawaye yafi komai arha a rayuwarta nandanan idanunta ya ciko da qwallah yasa hannu ya dago kanta yace “bance kiyimin kuka ba Meenah ai kin girma na gama aikina saura naki gashinan Kuma kin fara babu abinda na isa na sani game dake saidai najishi a gari kamar yanda barori da bayin gdannan zasuji babu abinda na isa kizo ki sanar dani matsalarki yanzun ta zama ba tawa ba kin fifita matsayin kowa saman nawa duk Ina kallonki" Da sauri ta dago bakinta Yana rawa tace “wlh ba haka bane Baffa'am tsoronka nakeji banason na sake bata maka rai shiyasa kaga Ina gujewa kusantarka....." Zubawa bakinta idanu yayi yana ayyana abubuwa da yawa kafin ya furzar da iska ya janye daga gareta daqyar ya koma ya zauna yace “rabona da cin abinci na qoshi tun Ina Benin shima din ba qoshi nakeyi ba Meenah kawai hqr nakeyi saboda tunaninki yafimin cin abincin dadi komai nawa kece nakasa samun sukuni sabodake hatta abokan aikina sunsan idan ba Meenah sukace min ba basa ganin walwalata meye yasa ke kika kasa sanya Rasheed aranki kika kasa bashi matsugunnin da bazai goge ba a ruhinki abin baqin cikin wai kewarki ta hanani sakewa na taho domin ganinki Ina murna yata ta girma kawai ki rasa da labarin da zaki tareni saina samarinki haba Meenah alqawari yace haka?" Duk da babu abinda ta tsinta cikin kalamansa wadanda ta gane Basu taka Kara sun karya ba Amma taji jikinta yayi sanyi a haukanta ta yarda batayi masa adalcin ba tace “kayi hqr bazan qara ba" murmushi yayi dama abinda yakeso kenan a duniyarsa yanason abashi hqr koda kuwa shine me laifi, fara zubansa abincin tayi ta dauka ta miqa masa ya lumshe idonsa tare da budewa yace “hannuna ciwo yake ya kamata a fara ramawa kura aniyarta" yanda yayi mgnr ya bata dariya tayi murmushinta me kashe masa jiki ta miqe ta zauna a gefen gadon ta rinqa bashi abincin da hannunta yanaci Saida ya qoshi ya kawar dakai ta turo baki tace “kuma ai baka cinye albarkar ba" murmushi yayi ya miqe yace “inason

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82