Chapter 54
Chapter 54
a pillow kuka me ciwo ya qwace mata daya Sanya Mom dake shigowa nufota da sauri tace “Subhanallahi waike yanzu Aminatuh bazaki daina Sanya damuwar nan a ranki ba kenan kullum ke kenan cikin jinya" wata ajiyar zuciya me qarfi Kareem ya sauke ya nemi guri ya zauna gumi na karyo masa Yana sharcewa Ya'isha dake shigowa tace “ya Kareem motar taka baka rufeta ba ka barota" shafa sumarsa yayi yace “wlh hankali nane baa jikina ba ince kin rufe" dagansa kai tayi ta nufi gadon da Meenah ke kwance ta riqo hannunta tace “amaryar Ya Kareem sunqi Allah yaso meye yayi zafi da doguwar jinya haka?" Zame hannunta tayi a na Ya'isha ta sake gyara kwanciyarta taci gaba da jan zuciya abubuwan da suka sabbaba mata ciwon suna dawo mata a fili tace “Aure, Ni Mai Martaba Ya Kareem Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati wlh banaso don Allah ku taimakeni ku rabani dash......... _Nasani wannan page din ba kowa zatayima dadi ba so Amma a babin qaddara wannan daidai ne shi ubangiji Yana zartar da hukuncin da yake daidai batare da la'akari da abinda Wanda ya zartar da hukuncin akansa zai nazartawa zuciyarsa ba kada ku manta matar mutum kabarinsa Kuma shi rabo ajali ne yakanyi kisa ma idan qarfinsa yakai._ _So kada kuga laifin alqalamina haka abin yake kamar yanda kuka ganshi a rubuce kada ki manta 50% is true life story._ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/6, 9:00 PM] Oum Hairan: *0030* Miqewa Kareem yayi ya fice daga dakin ya koma waje ya rafsa tagumi jikinsa sai tsuma yakeyi Yana tausayin kansa Amma yafi tausayin Meenah saboda tafisa shiga damuwa ya jima zaune a gurin kafin likitan ya iso suka shiga tare likitan ya dubata ya sake bata kulawa ya fice daga dakin ya dubi Juhud datake zaune take shan tea yace mata “sannu" bata ko dubesa ba ya nemi guri ya zauna Suna taba hira lkc zuwa lkc suna taba hira da Ya'isha Mom tana Sanya musu baki itako ko kallo bai isheta ba hasali ma tunda ya zauna takejin wani qunci aranta ji takeyi kamar ta fice daga dakin bata son ganinsa. Kwanciya tayi taci gaba da saqa da warwara a ranta sai yamma Ya'isha tace zata tafi mijinta yazo daukanta sukayi sallama suka tafi Mom ta tafi rakasu ya taso ya matso jikin gadon yace “duk da nasan ni mai laifine a gurinki Meenah Allah ya sani inasonki tun kafin yanzu Amma bantaba yimiki fatan ki dawo gareni ba Allah shine ya tsara hakan saboda haka na karba Kuma nayi masa gdy kema inaso ki karba kiyi masa gdy......" Miqewa tayi zaune zuciyarta na tafasa tace “akanme zanyi gdy akan abinda ba zabina ba bankuma nema ba? Why da zakace dole saina karbeka? Kareem da zaka manta dani ka fice cikin rayuwata da mun taimaki kanmu wlh banyi farin ciki da samunka matsayin miji ba kada kaji a ranka na karbeka bazan taba karbarka ba Rasheed shine zabina shine rayuwata......" Hannunsa ya dora bakinta yace “stop Meenah ya isheki don Allah kada ki fasamin zuciya da kalamanki kiji a ranki wannan bayin kaina bane yin Allah ne..... Wayarsa ce tayi ring ya zaro a aljihunsa number Zahrah ce yayi kamar ya kashe saidai zuciyarsa ta raya masa ya daga qila wani abune Important yasata kiransa danna wayar yayi ya Kara a kunnensa ta cikin wayar Meenah take jiyo gunjin kukanta tana cewa “Allah ya isa tsakanina dakai Kareem ka cutar dani kaine wlh kaine sila tunda kaine ka rakitomin ita cikin rayuwata harta cutar dani, na dauki ciki watanni tara na Haifa matarka ta kashemin yata wlh bazan yarda ba kaji na rantse maka wayyoh Allah na Zainab ta mutu Aminah ta lashemin yata......" Qit ya kashe wayar idanunsa ya ciko da hawaye ya dubi Juhud data zubawa TV idanu a zahirinta ba TV take kallo ba kalaman na Zahrah ne sukeyi mata yawo a kwanya yace “kinji sauqi likita yace zaki iya komawa gida zanyiwa Mom mgn ta shirya mu tafi Zainab ce ta rasu...." Bata ko kallesa ba taci gaba da wasa da yatsunta yaja numfashi ya fice a dakin suka hade da Mom a reception ya tsaya Yana dubanta da jajayen idanunsa da damuwa biyu tasa suka kada tace “yanzu ake fadamin Zainab ta rasu ya kamata kazo ka tafi kaima tunda jikin nata da sauqi" girgiza kai yayi yace “ban yarda da hankalin Meenah ba Mom zata iyayin komai Ina tsoron kada na tafi tayi tunanin guduwa tabarni wlh mutuwa zanyi a wannan karon Mom ke shaida ce na wahala a karon farko dana rasata don Allah ki tausheta ta soni koda kwatan Wanda nakeyi matane ni basai yakai rabi ba inasonta a haka" Murmushi Mom tayi me dauke da hawaye ta dafa kansa tace “Abdulkareem to Banda abinka Meenah yanzu ai taka ce kasan dai ba cikakkiyar lfy gareka ba don Allah ka rage damuwa da duk abinda zatayi zai hucce kasan kaima dole zaa fuskanci wannan qalubalen tunda ba ita taga damar auren nan ba Ni kaina Meenah fushi takeyi dani ban damuwa domin nasan gata Mai Martaba yayi mata kaidin dama kaine ka dace da ita Hukuncin Allah ne yabawa Rasheed da Kuma rabon Sarki junior Kuma ma ai tanasonka tun a baya kawai yanayin da take cikine yasa zakaga kamar batasonka" Murmushi yayi yace “hakane Mom na gde am Dr yace zamu iya tafiya gda nikam zanfi samun nutsuwa tana tare dani" batason jayayya dashi shiyasa ta aminta su tafi din ta shiga dakin ta fara hada musu kayansu Meenah na kallonta harta gama ta dubeta tace “mu tafi mijinki ya matsa saidai mu tafi gabadaya" daqyar Mom tasha kanta ta miqe suka tafi baya ta shiga yana kallonta yayi murmushi sai Mom ce ta shiga gaba suka nufi Katsina da suka isa Daura ta samu ta fita a mota tayi wuf ta shige dakin da take ta fada gado ta rushe da sabon kuka tana tuna wai yau ita ce matar Kareem bata Rasheed ba meyesa qaddararta kullum ita baibai ce a fili tace “lkc yayi da zan nemawa kaina gata dole na nemi su Baffa Ribado ko zasu kasheni su fitomin da dangin mahaifiyata" Qwanqwasa qofar taji anayi ta miqe ta bude qofar ganin Kareem ne tayi saurin mayarwa ta datse yaja baya da sauri tare da cije lebe ya juya a kasalce ya fice daga gdan ya nufi gdansa babu kowa kamar yanda ya tsammata yayi murmushi ya nufi gdansu Zahrah acan ya tarar da yan karbar gaisuwar bai wani zauna ya dade ba ya nufi gidansa ya kwanta a gado Yana saqawa da warwarewa akwai aiki a gabansa. Meenah batashi takeyi ba baya a lissafinta ga Addah Abulle ta takura masa da Kira har takai baya daga wayarta saboda yariga yasan mgnrta bata wucce akan qiyayyar aurensa da Meenah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82