Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

siririyar hanya. Itakuwa koda ta kwasa a guje duk nisa dake tsakaninta da rugarsu haka ra rinqa cin gudu harta fara hango rugar tasu nesa sosai gabanta ya qara yankewa ya fadi ganin wani baqin hayaqi yana tashi ta sashin da bukkarsu take, da sassarfa ta nufi gurin kawai taji an wafci hanunta da qarfi dagowar da zatayi taga Moddibo Buba ne idanunsa sharkaf da hawaye yana janta yana kallon bukkar tasu dakeci da wuta, Da qarfin gaske ta turje cikin fitar hayyaci tace “Innatuuuu!" Saurin rufe mata baki yayi yaci gaba da janta bai qyaleta ba saida yabar sashin rugar da ita ya tsaya jikin wata itaciya yana sharce hawaye ya dubeta yace “Haka Allah yake ikonsa Aminatu a wannan qarnin babu wani abu dazan iyayi miki face na saki a hanya kibar yankin nan gabadaya Su Bangel basu da Imani Ina zargin sune suka sanyawa dakin Indo wuta suka qoneta ina daji Audi yaje yake fadamin har yana cemin yanzu Hakama Ribadu da Manga sunacan suna nemanki kema sunason kasheki ne tunda uwayenki sunqi amincewa su bawa Manga Aurenki harma suna masa sharrin zai lalataki............ *THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566* *Shares Please* *Oum Hairan* [7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE FOUR 4* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *TUNATARWA* Tabbas gafalalle shine wanda yake take laifinsa yake kallon na waninsa asara da tabewa ta tabbata garesa, kada ka damu da kuskuren wani domin bakasan boyayyen sirrin dake tsakaninsa da Allah ba, yi qoqarin ganin ka samu kusanci da mahaliccinka wannan shine cikar hankali🤏🏼 Dubanshi takeyi da yanayi na gushewar hankali tanason ta bude bakinta tayi magana amma yayi mata nauyi gabbanta gabaki daya rawa sukeyi na tashin hankali zuciyarta tayi matuqar quntata, daqyar ta iya hada kalmar Moddi sun kashemin Innatu me tayi musu kana ina ka bari suka kashemin Innatu na Moddi shin Ina gatana???" Tana mgnr ne cikin gushewar hayyaci inda shikuma yaketa qoqarin janyewa daga gareta har ya samu ya yakice ta ya juya yana tsiyayar da hawaye batare da ya iya bata amsa ba. Saida ya bata tazara sosai tana tsaye kamar sassaqe sannan ya tsaya batare daya juyo ba yace “ki miqe hanyar nan tabbas nasan zasu biyoki koma suna kusa ki tafi Juhud kada su hallakaki burinsu ya cika banason burinsu ya cika nafiso su rinqaji a ransu cewa bayan Haro da Indo akwai wani abu da ya zame musu alaqaqai din da suka rasa samun damar cimma buri akansu tabbas taimakon Allah zai riskeki ta inda baki zata ba....." Daga haka bai kuma cewa komai ba ya tafi yabarta a kan kwanar ta durqushe a gurin ta rushe da wani marayan kuka na tunanin rashin madafa wanda bataji yana bawa zuciyarta sanyi ba saima qarin tafasa da takeyi. Haka tanaji tana gani Moddi ya rinqa ratsa Kalgo da Sabara har ya bacewa ganinta haka ta wanzu a gurin tsayin lkc tana dama ace itama Allah ya aiko abinda zashi dauki rayuwarta ta huta, yanzun idan tabar guringa ina ta nufa....... Tana tsaka da wannan tunanin ta rinqajin qarar yayi alamun tahowa akeyi gareta tayi saurin saita nutsuwarta duk tsoro irin nata yau zuciyarta ta soye mutuwa tafi buqata fiye da rayuwa, ji tayi an tsaya can ta fara hango duhun mutane har uku Muryar Baffa Ribado tajiyo yana cewa “yawwa gata cen...." Ai bata gama jin cewarsa ba ta zabura ta miqe daidai lkcn da suka zagayeta kowa da makami a hannunsa jikinta ya dauki tsuma ta dubi fuskokinsu zatayi mgn kawai Manga yakai mata sara ta goce ta fadi qasa warwas. Ya sake daga Addar Hannunsa ya saita qirjinta ta rintse idonta tanajin saukar saran daya sanyata sakin wata razananniyar qara data cika dajin. Ya sake daga Addar zai qara mata suka ga wani haske me dogon zango ya haskesu tuni suka saki makaman suka juya da sauri suka tsuke suka shige cikin duhun dare domin a lkcn magaruba ta jima da wuccewa. Hasken yaci gaba da kusantota har ya iso daf da ita cambala qafarsa da yayi a cikin jini ne yasashi saurin haska qasa yaga jinine yake malala a qasa kamar ruwa, da sauri ya saita fitilarsa a wajen da yaga jinin yana gangarowa ya matsa da sauri ya zubawa yar fulanin ido tare da russunawa ya haske fuskarta da fitilarsa sosai yaji faduwar gaba daidai lkcn da ruwan saman ya kece da qarfin gaske, yace “Cornel Rasheed yar fillon da kasai nono a gurinta ne dazun" Safa ya zaro cikin jakar dake goye a bayansa yasa a hannunsa ya daga rigarta tare da zaro ido waje saran ya shiga sosai, jinjina kai yayi tare da zaro wata qatuwar waya a aljihunsa ya danna wasu numbers ring biyu aka daga bai jira cewar me mgnr ba yace “ku tsare dukkan qofofin dajin nan guda hudu akwai yan ta'adda a cikinsa yanzu na tsinci wata sabuwar gawar bafulatana da alamun sun kasheta ne sukaji motsina suka gudu...." Qit ya kashe wayar ya sanya hannu ya sake gyara mata rigarta ya miqe ya debo ganyen bishiya ya rufa mata ya tsallake ya tafi. Ajiyar zuciyar da yaji ta saki ne yasashi tsayawa cik tare da juyowa ya haske fuskarta da wannan dalleliyar fitila tasa yaga ta bude idanunta ta sake mayarwa ta lumshe hakan ya tabbatar masa da sauran rayuwarta, raba daya biyu zuciyarsa keyi akan ya taimaka mata ko yayi tafiyarsa? Ji yayi zuciyarsa ta karye tabbas Dan'adam daraja ce dashi maybe idan ya taimaketa Allah ya qadarta tashinta idan kuma ya tafi yabarta wasu halittun na daji zasu iya zuwa su qarasa ta, da wannan tunanin ya tsugunna ya sanya hannunsa ya dagota cak ya sabata a kafadarsa ya miqe ya nufi Camp dinsu da ita, tafiya ce me tsayi sosai tsakanin gurin daya tsinci Juhud da camp dinsu haka yayita kurdawa cikin wannan duhuwa har ya fito sarari ya fara hango Camp din nasu kuratan sojojin da suke basu fita duty ba suna zazzaune cikin ruwan sunata hirarsu da iface²nsu. Duk inda ya gifta kallonsa akeyi da fuskar mamaki idan ya wucce su kalli juna su gimtse saboda sanin tsagwaron rashin imaninsa yanzu ne zai sabawa mutum halitta ko yabaka gwale²n da sai kayi sati kana ruwan dumi, kai tsaye clinic din Camp din ya nufa ya wucce kowa ya shiga har dakin duba marasa lfyr ya kwantar da ita saman gado ya juya zai fita Likitan dake kan aiki yayi qundunbalar cewa “Tnks Sir" jinjina masa kai yayi yace “kayi aikinka akan wannan yarinyar banason a samu matsala ka bari ta mutu kaima saika mutu domin alamu sun nuna zamu samu wani haske game da yan ta'addan nan da suka damemu" sake sara masa yayi cikin ladabi ya sanya kai ya fice wani Soldier ya dafashi yace “A tsarin aikinmu babu dauko petiant mu kawoshi garemu domin magani Cornel Rasheed meye yasa kayi hakan shin baka tunanin matsala zata iya afkuwa?" Fuskarnan kamar hadari yace “nayi ne don inada ra'ayin hakan kuma hakan nakeson yi saboda haka ayi hakan

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82