Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Juhud Book One 1 Complete Hausa Novels 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

gado rungume da wani hoto a qirjinta sai kuka takeyi me ban tausayi. Wani abu me nauyi ne yazo ya tokarewa Kareem maqoshi ya furzar da iska me zafi ya juya ya fice daga dakin sai Mai Martaba ne ya qarasa shiga ya kamo hannunta Babu musu ta miqe tanaci gaba da kukanta idonta lullube da alqyabba ya fito da ita harabar gdan Ya'isha ta nufosu da sauri suka sanyata a mota tana qarawa kukanta sauti tana Kiran sunan Baffa'am Sarki junior dukkan wanda yake a gurin hatta Mai Martaba Saida tasashi sharar hawaye. Hakanan suka nufi unguwar da gidan nasa yake Mai gadi ya bude musu suka shiga sukayi parking Aunty Hamida ce take riqe da hannunta har cikin gdan suka haura da ita saman itama kamar dayan sashin dakuna biyu ne sai wani qarami da alamun local kitchen ne wanda koda zaka buqaci wani abu da dare basai ka sauka ba, daya cikin dakunan suka bude suka shigar da ita sosai Hajiya Kulsum aminiyar Mom ta qara yimata nasiha akan biyayya ga mijinta itadai Babu abinda da takeyi sai kuka da rawar sanyi zazzabi ne yake neman rufeta Ya'isha ta matso jikinta ta sunkuya tace “ke banza ce wlh Ni banga abin kuka ba to kukan mafita ya zame miki kome?" Dagowa tayi ta sauke idanunta sa suka jima da komawa jajaye saboda kuka tace “shi....shikenan da gaske na rasa Baffa'am dina Ya'isha Kuma akeso nayi rayuwar farin ciki....." Muryarta ne ya kama rawa Ya'isha tace “mun shigai Aunty Hamida ku Kira mijinta zata tayar mana da aljanu" yanda jikinta ke tsuma ne yasa Hamida yarda ta Kira wayar Rasheed ya daga muryarsa can qasa shima rawar tasa muryar takeyi yace “ya aunty Hamida ya akayi?" Cikin zaquwa tace “Meenah ke neman rikice Mana mun kasa gane kanta don Allah kazo idan kana kusa" kashe wayar yayi dake dama Yana gdan duk motsinsu yanaji ya dauki doguwar riga ya saka ya bude qofar ya fito idanunsa kamar garwashi saboda ja dake duk yafisu Rasheed haske shi fari ne sosai daka kalleshi zaka gane kukan shima yakeyi. Kuka Fadila ta saka da ganin yanda yayan nata ya zama wani kalar tausayi tace “tunda yarinyar nan ta shigo zuri'armu muka daina cikakken farin ciki Ya Kareem kaima duk ta susutaka yanzu kukannan don ita kakeyinsa....." Hanya ya saita mata cikin zafin zuciya yace “kowa yaje na gde" binsa sukayi da kallo ya dubi Hajiya Kulsum yace “Mama wlh idan akaci gaba da hayaniya a gdannan tsaf zan haukace brain dina tana neman daina aiki" sumsum suka rinqa ficewa daga gdan saida suka fice gabadaya ya tsaya yana jin tashin motocinsu gabansa faduwa yake daqyar ya tura qofar da sallama ya shiga dakin ya tsaya tsakiyarsa Yana qarenta kallo tana zaune ta dora kanta jikin gado sai tsumar jiki takeyi a sanyaye ya isa gareta ya tsugunna gabanta yakai hannunsa zai dago kanta gabansa ya fadi ya janye ya sake saita idanunsa akanta yace “meye yake damunki?" Kamar me jiran yayi mgn ta dago kumburarrun idanunta suka shiga cikin nasa ya kawar da kansa ya dake zuciyarsa yakai hannunsa jikinta yajishi zafi zau yaja numfashi ya miqe ya dauki wayarsa Yana zagaya dakin can yace “Inada petiant a gdana kazo da wuri don Allah" da haka ya kashe wayar yaci gaba da zagaya dakin can yaji ana qwanqwasa qofar ya sauka ya bude suka shigo tare Dr Razaq ya fara tambayarta yanayin da takeji tayi masa shiru shikam Kareem ido ya kafeta dashi can da tambayar ta isheta tace “Kaje Dr Razaq bakada maganin matsalata Allah ne kawai zaimin magani" wata iska Kareem ya furzar ya juya ya fice Dr Razaq ya biyosa yaganshi tsaye ya hade kai da garu ya dafashi yace “ka daina Sanya wannan damuwar a ranka Ranka shi dade kanada heart problem idan komai zaike damunka to rayuwarka tana cikin kwale²" Juyowa yayi ya dubi Dr Razaq yace “kana nufin Meenah zata soni nima?" Dariya tambayar tabawa Razaq yace “kama qaddara a ranka tasoka fiye da kowa ta gama karfa ka manta kaine ta fara so a rayuwarta ko ka manta Karin mgnr hausawa da suke cewa so baya tsufa saidai masoyan su tsufa bature kuma yace true love never end" wani murmushi yayi yace “na gde Dr Razaq zan jira lkcn da zan gasqata hakan"............. Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/8, 9:07 PM] Oum Hairan: *0032* Sallama sukayi ya rakashi ya hau motarsa tare da karbar magunguna bai koma gdan ba shima ya shiga tasa motar Yana duba agogo 8:30pm ya jinjina kai ya fice a gdan kai tsaye wani restaurant ya nufa yayi musu siyayyar abinda zasuci ya juya ya koma gdan ya kulle ko Ina ya nufi saman Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya sanya kayan baccinsa ya fito ya bude nata dakin tana zaune inda ya barta har yanzu kukan takeyi gabadaya lamarinta ya tsinka masa lakar jiki da gaske take jin damuwar a cikin ruhinta. Aje ledar dake hannunsa yayi ya tsugunna a gabanta ya kamo hannunta ta fuzge ya zauna sosai a gabanta ya dafe kuncinsa da hannayensa biyu ya zuba mata manyan idanunsa da a baya suke firgitata da sanyata shiga taitayinta baiji a ransa ko yace ta tashi suyi nafila zatayi ba shiyasa ya janyo ledar yace “Ya'isha tace tun shekaran jiya bakici abinci ba ko meye dalili?" Shiru tayi masa yaja fasali ya furzar da iska ya bude ledar ya fara yaga mata Naman yanda zataji dadin ci ya dauko yakai mata bakinta ta kawar dakai yayi murmushi yace. “Lamarinki abun mamaki ne Meenah sai naga kamar kina jayayya da hukuncin ubangiji ne ya kamata ace rayuwarki kadai ta ishenki darasin da duk wani abu da Allah yayi zaki tarbeshi hannu biyu wlh duk da nakasance me qulafuci da addu'ar idan kedin Alkhairi ce gareni ki zama gatana ki zama mallakina bantaba furtawa wani burina a kanki ba na fawwalawa ubangiji na yarda duk abinda yayi daidai ne so Kuma sama taka cikin lkcn da ban tsammata ba kiran Mai Martaba ya shigomin yana fadamin na tanadi sadaki a hannuna daga dubu hamsin zuwa abinda Allah ya horemin nazo masallacin Fada yana nemana bansan meye zai faru ba hakanan na tafi Ina zuwa naga dogare sun budamin na shiga kamar yanda baa nemi izininki ba nima baa nemi nawa ba wlh kudin aljihuna kawai Mai Martaba ya karba dubu tamanin yabada umarnin a daura nidai na nemi guri na zauna Ina jiran naji auren waye zaa daura kawai naji ance yace shi a matsayin waliyinki ya bada aurenki gareni akan sadaki naira dubu tamanin bisa sharadin zanyi miki lefe kamar yanda al'ada ta tsara" Shiru yayi yana mayar da numfashi sannan yaci gaba da cewa to meye laifina cikin lamarin nan Meenah?" A qufule ta dago tace “meyesa bakace bakaso ba?" Murmushi yayi yace “ko bake bace

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82