Chapter 65
Chapter 65
yace “ki riqe nabaki sadaka idan kinason agogon ma da zoben duk na cire miki Ni dama na daina kwalliya takaba nakeyi Kuma bazan qarason wata mace ba a duniya tunda na rasa Meenah" Girgiza masa kai takeyi tana kuka me gunji ya dora hannunsa a bakinsa yashe “dallah malama kiyi shiru Meenah batason kuka" gumtse bakinta tayi ya juya zai fita Mai Martaba ya budo qofar ya shigo yaja ya tsaya da sauri yace “ya subhanallah Rasheed meye hakan?" Murmushi yayi ya sosa sumarsa yace “ai harkai zan iya kyautarka indai akan Meenah ne" zaro ido Mai Martaba yayi yace “nidin Rasheed" dariya yayi harda riqe ciki yace “kaidin har wata daraja ce dakai ta musamman da zatasa naqi fansar dakai akan Meenah?" Girgiza kai Mai Martaba yayi yace “naji banida ita Sanya kayan naka muje masauki" juyawa yayi ya kalli Juhud ya tsugunna yace “don Allah mamana kibani aro Allah niba barawo bane zan dawo miki dasu yau dinnan aidai bake kika sani ba nine nasa kaina nabaki kyautarsu ko?" Miqa masa tayi yace “aafah Hajiya in kinsan ba tsakani da Allah kika baniba bar kayanki" Dauke qwallah Mai Martaba yayi yace “karbi tsakani da Allah tabaka" yasa hannu ya karba Yana sawa Yana waqarsa “Meenal Aso kin matar da zuciyata ta mace! ki tausaya karki sani bangare na yaudara!! Ina gudun duniya!!!" Da wannan ya fice Mai Martaba ya dubeta yace “likitana ya tabbatar min da zai samu sauqi fah karki damu" ficewa sukayi suka barta da kallon Kareem dake kwance kamar gawa ta juya itama ta fice kamar mahaukaciya ta nufi block nasu ta fada gado domin tabawa zuciyarta hutu daga sabon tashin hankalin daya tunkarota ga Baffa'am dinta a gabanta Amma yakasa ganeta to waima meye asalin dalilin sukurkucewarsa ne haka Shiba Mai mgn ba Amma surutai rarrara kamar Wanda ya qone a qeya miqewa tayi tare da cewa “tabbas lkc yayi da zan sakawa Mafi cancanta Alkhairinsa....." Tunaninta ne ya tsaya cak da tunawa da Kareem shikuma da yake cikin halin ni yasu dora hannu tayi akanta daidai lkcn da wayarta tayi ring ta wawurota Ya'isha tace “na dade inason tsegumta miki watanni biyu baya anga Big Cele a Tanzania to tsoron jagula wannan dofanannen auren naki da Ya Kareem yasa Mom ta Hanani fada miki wai Kuma yau sainaji me kankat ankawo mikishi har qasarku" Cikin kuka tace “shine me gata ko rashin galihu yasa kukaki fadamin labari mafi soyuwa a duniyata Ya'isha ko ku fada ko karku fada Rana irin wannan zatazo gashi tazo Baffa'am ya dawo zamana da Kareem ya qare....." Da qaraji Ya'isha ta katseta da cewa bakida hankali ne karki soma wlh Kareem yafi kowa buqatar taimakonki kinaganin fa a halin da yake" jan zuciya tayi tace “meye ribata dama uwarsa ta rantse indai na haihu saiya sakeni to kafin ma na haihu zanbar mata gidan danta nima a dole nake zaune don halacci" magana Ya'isha keson yi mata ta kashe wayarta can Mom ta kirata tace “idan kin kwantar da hankalinki akwai labari me dadin dadi da nakeson baki" Muryarta harta dashe tace “kun boyemin abinda na cancanci nasani Mom meyesa" murmushi tayi tace “saboda kada muyi mahaukata biyu a dangi shiyasa Meenah kifa nutsu motsi kadan zakiyi ki fada rami mijinki yafi kowa buqatarki to kibi sannu kada santsi ya debeki"haka Mom ta rinqa bata kalamai wai ita a dole saita kwantar mata da hankali batasan qara tashin hankalinta takeyi ba suna kashe wayar Dr Khazeem yazo ta dubeshi yace “ya naki jikin batason hayaniya hakan yasa tace “naji sauqi so ganin yanayinta yasashi ficewa ta koma ta kwanta kamar bazata koma asibitin ba saidai taji zucciyarta taqi natsuwa dole ta shirya ta nufi asibitin ga mamakinta saita isheshi a zaune shida Mai Martaba ta dubesu suka gaisa da Mai Martaba yace “kema kina buqatar hutu ya kamata ki koma gda ki haihu acan" jinjina kai Kareem yayi yace “dama inada burin hakan sai na kwanta jinyar nan" da wannan sukaci gaba da tattaunawarsu hankalin Kareem na kanta Mai Martaba yace “ki koma masaukinku ki huta zan kwana dashi muga abinda hali zaiyi"....... _Yau fah saidai hqr da qarancin page din_ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/12, 8:08 PM] Oum Hairan: Duban juna Juhud da Kareem sukayi yayi mata qaramin murmushi ya shafa sajensa tare da nuna mata hanya yace kije ki huta heart kinyi qoqari fah na gde Allah yabada lada" sunkuyar da kanta tayi tare da daukar wayarta tayi musu Saida safe ta fice ta nufi masaukin nasu zuciyarta na kaikawo tsakanin qirjinta da duniyar Rasheed, tana zuwa wanka kawai tayi tayi sallah ta kwanta itakam wannan dare barawon ma kasa satarta yayi gabadaya ta rasa nutsuwarta batajin daidai saina tunanin Rasheed, da asuba tayi sallah ta zauna tanayima iyayenta da Rasheed addu'a tare da fatan sauqi da sassauci cikin wannan jarabawa da suka tsinci kansu a ciki ciwon tabuwar qwaqwalwa a Rasheed abin Babu kyau. Data tashi da ciwon mara ta tashi hakan yasa bata koma asibitin da wuri ba Saida Tasha magani ta dan samu relief sannan ta fita ta nufi hospital din a qofar dakin da Kareem yake ta ishe Rasheed Yana tsaye yana danna waya kamar ance ya dago suka hada ido ya lumshe idanunsa qirjinsa Yana bugawa itama haka ta matsa gabansa tace “barka da sfy Baffa'am" ja tayi da baya lkcn daya kece da dariya yace “shegiya ashe kinsan sunana ai Meenah ce take kirana da wannan sunan" lumshe idonta tayi hawaye ya ciko ijiyarta ta bude akansa ta girgiza kai tare da cewa “ka manta kowa da komai ka manta kamannin Meenah a zahiri Amma baka manta sunanta ba Baffa'am ya akayi hakan?" Yarfa hannu yayi yace “nima to nasani kawai dai kema kinsan idan na kama Wanda ya kashemin Meenah a gabana saina dirmeshi da alburushi ke barima kiji fah koda yake na daina kulaki Meenah kishine gareta batason a hadata da wata a mafarki Ina ganinta kullum Kuma fah tana dan kama dake kadan Amma bakikai kyaunta ba" Mai Martaba ne yajiyo mgnr ta Rasheed tayi yawa ya leqo yaga ashe shida Meenah ne tasashi a gaba sai hawaye takeyi ya qwala mata Kira tayi saurin goge hawayen tace “ok ganinan" ta juya zata tafi ya riqota yace “shifa Wannan mutumin dan raini ne ya rainani yama zaayi Ina mgn da mutum ka kirashi to kaima ka kiyayeni kafin na qundumeka" zaro ido sukayi dukkansu ya dora hannunsa a bakinsa yace “lalalah ashe fah sabo nakeyi kayyy ke haihuwa zakiyi me zaki Haifa?" Ganin batada niyyar tahowa ne Mai Martaba ya fito yaja hannunta yace “idan kika biyewa wannan saiku raba Rana da dare yanayi miki soki burutsunsa" sosai sautin kukanta yake fita batare da tasan kalmar ta subuce ba tace “ta Ina zan fara taimakonsa?" Dubanta Kareem yayi ya kawar dakai yanajin wani abu nayi masa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82