Chapter 96
Chapter 96
fa maca ce tayi shigar maza wlh, amma fa ta iya shiririta," ɗan kallonsa sgr yayi tare da cewa "Wa kenan? "House boy ɗin nan mana, daya kawo mana drinks yanzun nan," Sgr yace "Are u serious ? Adams yace "Of course baka ta6a lura bane? Sgr yace "taya zan lura, bayan ko face ɗin mai aikin bansani ba,' Adams yace "No wonder that's y baka lura da hakan ba, amma fa maca ce wannan hada sa gashin baki, ' ya ƙare maganar yana dariya don kam ba ƙaramin nishaɗi abun ya bashi ba, shigar yarinyar amatsayin namiji kamar ɗan chali chali, "Amma ko meyasa tayi hakan"? Adams ya tambaya yana kallonshi," Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa "Zan bincika, koma wa ya turo ta, zan sani ne, zasuyi bayani," Acewar sgr, "Gsky kam, u ave to investigate about it, kasan mugun mutun bakasan da wata siga zai shigo rayuwarka ba, especially yadda kke da suna haka ba'a rasa enemies masu son kawo muku hari ta bayan fage, ya kamata ka miƙe tsaye akan lamarin wannan mai aikin tukur, kasan da wata manufa yazo domin kuwa wlh maca ce ba namiji ba," Adams ne yake kora masa bayani yana ƙara jaddada masa akan mai aikin Don ayi saurin dakatar da shi daga abunda yake ƙoƙarin aikatawa, 😳 Sehrish fa batasan wainar da ake toyawa ba, Ashe watan cin uban wata yayi acikin gidan nan 😂 bedroom ɗinta ta koma tana safa da marwa, cike da tunanin dariyar da taga abokin sgr nayi mata aranta tace wata'ƙil shigar mazan da nayice ta bashi dariya Allah saki, __________________________________ A hankali motocin marshal Omar suke shiga cikin katafaren gidan General Ishaq wanda ke a Unguwar rimi, Hamshaƙin gidan wanda sojoji ke tsare dashi ta ko'ina, jahad sai faman bin gidan take da kallo ganin haɗuwarsa ta cikin glass ɗin motar, jinjina kanta tayi aranta tace "Aljannar duniya," Juyawa tayi ta kalli hosana wadda ta kwantar da kanta a kafaɗar Jahad ɗin sai faman bacci take shararawa murmushi jahad tasaki tare da cewa "Nasan hosana in taga wannan haɗaɗɗen gidan dole ta susuce,' Mayar da idonta tayi kan glass ɗin tana ƙarewa gidan kallo aranta tace "Allah yasa kamar yadda gidan nan yake da kyau mutanen gidan ma zuciyarsu ta kasance mai kyau ce kamar haka, Ya Allah kasa kasancewar mu acikin gidan nan yasa ƙarshen wahalar mu kenan, Allah yasa mutanen gidan suyi marhaban da zuwan mu kuma su tarbemu hannu bibbiyu kamar yadda goggon katsina tayi mana," ta ƙare maganar tana mai jin wani sabon yanayi atattare da ita, A jere motocin suka tsaya, sajan ɗin dake driving ɗinsu ya fito ya buɗe musu mota, fitow jahad tayi tana faɗin "Hosana ki tashi mun iso fa," daker hosana ta buɗe idonta da sukayi luhu luhu tana bin jahad dake mata magana da ido, daker ta iya sa ƙafa ta futo daga motar tana murje idanunta don taƙara tabbatarwa kanta cewa dagaske ne hamshaƙin gidan da take ganinsu aciki ba mafarki ba, aiko ta shaida hakan, Fitowa Marshal Omar yayi daga tashi motar, yana sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalli su hosana yace " ku biyo ni," Bin bayansa su kayi atare suka shiga hadaɗɗen jigunannan babban falon Aunty babba, wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa ta cikinsa abunka ga ƴan maiduguri dama an shaidasu akan hakan, Wasu irin haɗaɗɗun Sofas ne masu Numfashi sets guda, launinsu Maroon colour, ga sofa tables ɗinsu launinsu, Falon yasha ado da decorative object ga vase ajiye (tukunyar flower) ga wata irin faskekiyar plasma manne a wall ɗin kai komai fa yaji ya haɗu, Babu kowa a falon sai sanyin A.c dake ratsa sassan jikin mutun, "Have a seat," umar ya umarce su sai faman bin ko'ina suke da kallo , a tare suka zauna saman 2 seater suka takure junansu tsoransu dawa zasu fara cin karo, Shima yasamu wuri saman 3 seater ya zauna yana facing ɗinsu idon shi nakan hosana wadda ke ta faman lumshe ido saboda baccin da takeji ga yunwa, Phone ɗinsa ya zaro daga trouser pocket ɗinshi ya danna numbar aunty Babba ya buga mata Calling, Da ƙarfi wayarta ƙirar Iphone 13 pro max ta soma ringing tana ajiye saman bedside drawer gefen lamp, Hajiyar na hakimce tana sharar bacci Saman haɗadɗen gadon nata, jikinta na sanye da riga da wando masu kyan gaske ga laushi kamar sleeping dress haka suke, takurar da ringing ɗin yayi mata ne yasa ta buga uban tsoki a ƙule cikin bacci take cewa "Mtsww Wai wanene ne yake son takuramin ina tsaka da jin daɗin baccina," ta ƙarasa maganar tana buga Uban tsoki rai a bace ta tashi zaune fuskarnan kamar Alkubus a kumbure take don ma Allah yasa akwai kyau da haske ssae da ba ƙaramin muni zatayi ba, Hannu tasa ta fisgi wayar ta duba ta ga wanene, sunan (Marshal Omar ) ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, ae tuni ta wartsake daga baccin da take yi, jiki na rawa ta ɗaga tare da karawa a kunnanta tace "salamun Alaikum," bai amsa mata ba sai cewa yayi "Muna a palor muna jira," Cikin sauri tace "oh to gani nan zuwa," Ta ajiye wayar tare da miƙewa tasa hannu ta ɗauki mayafin kayan jikinta dake ajiye saman gadon, ɗaure shi tayi akanta maimakon tayafa shi a jikinta, sumar kannan nata tasha ƙananun kitson kalaba, A hankali take tattaka steps ɗin benen tana saukowa down, tun da suka ji takon takalmi suka ɗago suna kallonta haƙiƙa sun tsorata da kyawun matar ga yanayinta na marasa son mutane da hayaniya haka, Jinjina kai su kayi tare da kallon juna lokaci guda suka mayar dakansu ƙasa, A second to the last steps na stairs ɗin ta tsaya Curus ! tana kallon tagwayen matan da tagani zaune saman kujerunta sai taga abun kamar a mafarki gadai marshal omar zaune to su waɗannan isassun da suka zauna matan saman kujerunta su wanene ta tambayi kanta, har hannu take sawa tana murza idanunta don ta tabbatar cewa ba mafarki take yi ba, Idasa saukowa tayi har time ɗin bata sauke idonta ba daga nasu Hosana wani irin kallo take binsu dashi kallon neman ƙarin bayani, Muryar Omar ce ta katse ta da cewa "barka da fitowa aunty, fatan na same ku lafiya," Lokaci guda ta saki fuskarta ta ƙarasa ta zauna saman 1 seater tana cewa " Yawwa Omar saukar yaushe? wlh bacci ne ya kwashe ni nasan dae ka ce mun zaka zo nan bfr ka wuce abuja," Omar yace "Eh hakane, ina yaya ishaq ne? "Ae bayan kabar nan, shima yayi tafiya," Ta faɗi tana kallonsu hosana da jahad, wadanda suka sha jinin jikinsu tuntuni musamman da suka gaisheta sai tayi kamar batagansu ba, Miƙewa tayi tare da cewa "bari na kawo muku abun ta6awa," tayi mgnr tare da wuce wa kitchen, tana shiga ta tsaya riƙe da qugu tana sake sake iri iri aranta. "Su wanene waɗancan twins ɗin da Omar ya kawomin a gida? hankali na fa bazai kwantaba har Sai nasan su wanene da kuma matsayinsu a wurinsa," ta ƙarasa tunanin nata tare da shigewa ciki tana shirya musu Abunsha dana ci," Su hosana da jahad kam sunfa shiga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113