Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Abban Sojoji Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

rana har kunyi silar mutuwarta,' Nan fa wuri ya ɗau cece kuce hayani ta cika wurin, mamansu mamee na ƙoƙarin ta kare su amma abun yaci tura, Ga matasan dake waje jira suke kawai a basu dama su halakar da yaran dama haushinsu suke ji saboda rashin basu haɗin kai, basa kula kowa yau ga dama ta samu, Hankalin husanna ba ƙaramin tashi yayi ba ita dake zaune ido biyu tana jin abunda mutane ke cewa ita kuwa jahad har yanzu bata farfaɗo daga suman da tayi ba, Mamee ce ta taimaka ta ɗebo ruwa a cup suka yayyafa mata, da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi idonta sunyi jawur, bala'i biyu ga raɗaɗin da take ji a zuciyarta ga kuma abunda tafarka taji mutane na cewa, ganin cewa dagaske hukunta yaran zasuyi su kashe su suma, yasa mamee gudu izuwa gidansu cikin hanzari ta laluba school bag ɗinta, wayarta ta ɗauko ta dannawa ƴan sanda kira, taci sa'a an ɗaga nan tayi reporting akan abunda ke faru tare da basu address na anguwar, Abunda yasa tayi hakan kwara hukuncin da ƴan sanda zasu ɗauka akan wanda ƴan unguwa zasu ɗauka, kisan wulaƙanci zasu yi masu ba bincike, Lokacin da ta koma gidan dakyar ta samu hanyar shiga mutane sun cunkushe ko'ina, Ta raza na da ganin wasu matasa guda biyu hannunsu ɗauke da galons na fetur ga ashana a hannunsu kira suke abasu hanya su ƙone mayun, saboda rashin imani matan dake cikin gidan suka shiga basu hanya, haka aka janyo su waje daga cikin ɗakin sai kuka suke yi gwanin bantausayi, Zazzaga musu fetur ɗin suka soma yi ajikinsu nan take numfashin husanna ya soma hau hawa, jahad kuwa ta ƙanƙameta tarungume ta ajikinta sun rungume juna suna jiran ta Allah ta kasance, A dai-dai wannan lokacin jiniyar motar ƴan sanda ta karaɗe ko'ina, mota guda suka yo sai a kopan gidan dandazon mutanene da suka gani ne ya tabbatar masu da cewa nan ne address ɗin da yarinyar ta basu, Tabbas a ranar sunga bakar rana, dakyar ƴan sanda suka kwace su, suka sanya su a bayan kanta suka tafi dasu, Mamee da mamansu sun sha kuka saboda tausayin ya rayuwar yaran zata kasance ? Case ya koma hannun police sai yadda hali ya bada, a police station suka kwana ana investigation akan mutuwar tsohuwar, ga baƙar yunwa ga tashin hankali, duk yaran su firgita matuka ga kwanan cell sai uban sauro dake cizonsu,_ 😭•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·• *ABBAN SOJOJI* _mallakin_ *HAFSAT BATURE* _wannan ƙirƙirarran labari ne wasu abubuwa ma daga cikinsa ƙirƙirarsu akayi domin ilmantarwa faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa_ _gargaɗi ko da gigin wasa ban yarda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba batare da iznina ba, wahala tace ban shiga harkar kowa ba kuma nima bana so a shiga tawa kowa ya tsaya iya matsayinsa_ *page* *43* to *44* _The Father Of soldiers Kamar yadda su husanna suka kwana a cell ba bacci itama haka ta kwana ido buɗe, banbancin shine su suna cikin matsanancin hali, ga sauro ga yunwa ga ba wanka komai ya hargitse musu bayin Allah, Zuciyarta ce ke matsanancin buga mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa, ƴan uwanta na cikin mawuyacin hali, saboda aduk lokacin da wani abu mummuna ya faru dasu sai taji a jikinta, zuciyarta ce ke matsanancin buga mata, zufa ce ke ta faman sintiri a jikinta, kai kace akwai zafi ne Alhalin yanayin garin sanyi ne, dukkan ilahirin jikinta sai makekketa yake yi, sam zama saman gadon ya gagare ta, tadawo ƙasa jikinsa ta jingina bayanta, tausayin rayuwarsu ce ta kamasu, tun suna cikin ciki ƙaddarar su ta soma, sun sha baƙar wahalar rayuwa, ba irin tashin hankalin da basu gani ba, wani lokacin har tambayar kansu suke wai Allah baya sonsu ne? astagfirullah 😥 Amma hakan baisa sehrish tadaina nafilfilin da take yi ba, yau ma rashin tsarkin da bata dashi ne ya hanata yin sallolin, addu'o i kawai take faman maimaitawa duk wacce ta zo mata a bakinta, Amma fa a daren nan tasha kuka, kamar ba gobe, dole mane sehrish tayi kuka domin kuwa halin rayuwar da suke ciki duk juriyar mutun yaji sai ya matse kwalla, fargabarta wane hali su husanna ke ciki tana tsoran ta rasa jininta, na biyu wane hali mahaifiyarsu take ciki shin tana raye ko ta mutu? na uku wanda shine take jinsa sosai a ranta wato zuwan SGR, BABBAN YAYA, tarasa me yasa ya tsaya mata a zuciyarta meyasa take jinsa, meyasa take fargabar ganinsa, Zuciyarta tana azalzalarta akan son ganinsa, idanunta na kwaɗayin sa shi a idonta, Amma a ƙarshe tayi addu'ar Allah yasa ya zama alkhairi agare ta !!! sai da asuba bayan ta shiga toilet ta canza pad ɗin cikinta, sanna fa bacci yayi awon gaba da ita, A can ciki kuwa suna shiryawa zuwan Abban nasu, farin ciki a gun junaid ba'a magana, saboda ya gama tsara shagwa6ar da zaiyi masa in yazo, sannan akwai abunda yake burin ya sanar dashi , Har garin Allah ya waye sehrish batasan meke wakana ba, aunty azmi ta shigo ta same ta tana sharar bacci, ganin yadda jikinta ke kerma ya tabbatar mata da cewa sehrish ba lafia ba, har jikinta ta ta6a temperature ɗin jikinta yayi zafi, Don haka bata attempting tayar da ita ba, kawai sai dai ta gyara mata blanket ɗin jikinta, sannan ta fice, ganin cewa aiki zai yi mata yawa time zai iya ƙure mata, saboda baƙin da zasu zo yau, da buƙatar su kammala girke girken da zasuyi da wuri, Kanal yusif ta nema ta sanar dashi halin da ake ciki na rashin lafiyar mai aikinsu tukur, taji daɗi da yasanar da ita cewa, akwai chefs da zasu zo kada ta samu damuwa, tun 7 suka ƙaraso, kwararru ne a fannin sarrafa abinci kala-kala, su biyu ne, chef ummu da abokiyar aikinta momina, azmi taji daɗin zuwansu, nan fa kowa ya naɗe hannun riga aka soma gudanar da aiki, Tuni ƙamshi ya soma gauraye ko'ina harta cikin hancina, irin ƙamshin da ke tada mutun daga bacci, Wurin 9 na safe, jirginsu hajiya azeema yayi landing daga legos, ƙanwar Abbansu ce, hamshakiyar attajirar mai kuɗi ce, tatara har sunyi mata yawa, a tare da ita akwai Captain najeeb da Talal ƙannensu kanal yusif ne da take ruƙo a wurinta, saboda bata ta6a haihuwa ba, lalura ce ta same ta na rashin aihuwa, gashi Allah ya jarabce ta da sonsu kamar hauka, Hakan yasa Abbansu ya mallaka mata su, a wurinta suka taso har suka girma, Kanal yusif ne ya ɗauko su daga airport, izuwa gidan murna agunsa har ba'a magana, saboda ganin captain najeeb da Talal, an jima ba'a haɗuba duk da suna ƙoƙarin sada zumunci, aiki ne ya ke hanasu wani time ɗin, saboda aikin soja ba aiki bane na zama wuri ɗaya ba, Bayansu sai general Ishaq wanda ya kasance shina first born a wurin abbansu wato yayansu gaba ɗaya, wanda ke zaune a kaduna state, tare da matarsa yazo shuwa'arab ce suna kiranta da Aunty Babba, saboda tana auren babban yayansu gaba ɗaya, sun zo ne tare da Hafsat yarsu ɗaya tilo, wadda take karantar military nurse, ynx haka ta kammala karbar training ɗinta aiki take

Table of Contents

Chapters

113 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113