Chapter 22
Chapter 22
mu mallaki hankalinmu mu ke fuskantar ƙaddara iri iri meyasa !? Zube wa kasan tiles ɗin tayi tana kuka jikinta har jijjiga yake yi, Sam bata ji shigowar azmi ba sai dai mutyarta taji ta dirar mata a kunne" Ya sunanki ? ta jefa mata tambaya , yunkurawa tayi ta tashi tsaye tana matse hanci ta ce "SEHRISH" Jinjina kai azmi tayi tare da ƙarasawa inda take, tafin hannunta ta sa tana share mata hawaye, sam sehrish bata yi tunanin hakan ba, sannan cikin natsuwa ta ce" nayi takaici dana sa wannan kyakkyawar fuskar zubda hawaye am so sad," cike da mamaki sehrish ke kallonta, azmi ta ci gaba da cewa "kiyi hakuri ko kusa bazanso na raba ki da aikin ba! duk da ina tsoran abunda zai biyo baya, amma zan iya jurewa don ganin na taimaka miki," jin wannan bayani yasa sehrish sauke nannauyiyar ajiyar zuciya, mayar da hannunta tayi a saman shoulders ɗinta taci gaba da cewa" da farko ina so ki fadamun dalilin dayasa ki kayi basaja a matsayin namiji"? Muryar na rawa ta soma magana cikin sheashekar kuka" ƴan uwana ne basu da lafiya rai hannun Allah an kwantar dasu asibiti, kuma doctor ya ce aiki za'a yi musu, shine nake kokari naga nasamu ƙudi na biya musu, ɗayar ma dr yace in har ya wuce 5 ga watan da zamu shiga sai dai a fidda ita Qasar waje ko tarasa ranta.....' kukan ne yaci ƙarfin ta, Cikin lallashi azmi ta ce "daina kuka ya isa haka, na fuskanci matsalarki, duk da ina buƙatar bayani amma bani da enough time, riƙe wannan zamuyi magana an jima yanzu dai taimakon da zan miki shine, zaki ci gaba da aiki a matsayin Namiji kamar yadda kike yi, ko da gigin wasa karki bari su gane cewa ke maca ce ! sannan maganar kuɗi kuma nawa ne ake bukata ? Azmi ta tambaya tana kallon ta, sehrish ta ce "dubu ɗari tara ne" a tunanin ta azmi zatayi shock in taji kuɗin amma sai taji tace"zan iya ansar miki albashinki na wata na shekara ɗaya da rabi ! a baki a ɗunkule amma inaso ki sani ! duk runtsi duk wuya duk kuma duk irin wahalar da zaki fuskarta da wulaƙanci a wurin masu gidan nan, dole kiyi haƙuri ki jure! kiyi musu biyayya sau da ƙafa, ba maganar barin aiki , in kuma har kika ce zaki bari toh sai fa kin biya sauran kuɗin da kika ƙarba kin amince!!? 😰 taji ma tana nazari kafin tace"Eh na amince !!! zuciyarta na wani irin bugawa ba kowa ya faɗo mata a rai ba face Ayaan da jahaan , ynx ana nufin ta ɗaura aure da kaddararta na zama cikin gidan nan! ya ilahi, "Yanzu account number zaki bani na wanda za'a turawa kuɗin aikin nasu," azmi ta faɗa tana kallon cikin idonta, tsananin farin ciki ta gani a fuskar sehrish 😇 cikin jin daɗi tace "babu a wuri na amma zuwa anjima ko gobe zan samu na kawo miki," azmi ta amsa da toh sannan ta kama hanyar fita har takai bakin kofa xata buɗe ta juya ta kalli sehrish dake ta faman sakin murmushi tace "kada ki manta ynx kina ƙarƙashin Iko na! komai zakiyi saida umarnina, idan har kika saba hakan, hmmmm, bata ida ba ta fi ce, sam sehrish bata damu da hakan ba, ita dai indai akan sisters ɗinta ne toh ko fiye da hakan ma zata iya jurewa, Jiki na rawa baiwar Allah ta shige toilet ta dauro alwala taci gaba da zabga nafilfilin miƙa godiya wa ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala, Matsalar su husanna tazo ƙarshe, sauran damuwa ta kau, shin yaya kke tunanin rayuwar sehrish zata kasance a gidan ABBAN SOJOJI ? 😢 yinin ranar da fara'a a fuskarta hakoranta a washe kamar mai tallar maclean, cikin jin daɗi suka gudanar da aiki a kitchen tare da azmi don shirya dinner, tunanin yadda zata sake ɗaukar wayar junaid takira husanna ta ce su turo mata account number, har zuciyarta take jin ƙaunar azmi saboda tayi mata rana ! Har abada kuwa ji take bazata taba sa6a mata ba! tayiwa kanta alkwarin zatayi mata biyayya bazata taba bijire mata ba ko taci amanarta ba, A 6angaren junaid kuwa, bayan ya tashi daga bacci da jimawa ya wuce masallaci daya dawo ya tsaya a filin da suke buga ball na gidan tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan, yunwa ce tasa shi shigo wa ciki after magrin prayer, muryasa suka dinga ji yana kiran "tukur ! , Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish, cikin ɗauki ta ajiye wanke wanken da take yi agaban fanfo, na kayan da suka yi amfani dasu, Karasawa tayi wurinsa yana zaune saman 3 seater, yana daddana wayarsa, cikin girmamawa tace"gani ya ya junaid" ta kirasa da hakanne saboda ya hana ta ce masa yalla6ai, girman jiki ne kawai dashi da kuma tsawo fuskarsa ce kawai zata nuna maka cewa yaro ne sharkaf, ta6e baki yayi tare da ɗan jefa mata kallo ya ce" ƴunwa nake ji, " ya faɗa a shagwa6e, yana kallon ta cikin zumuɗi ta ce " a shirya ma abinci a dining ko nan zan kawo maka,? ta tambaya tana kallon wayar hannunsa kamar ta fisge ta saboda ita take bukata, ɗan yatsina fuska yayi kafin ya ce" No a tsarin gidan nan bama iya cin abinci in ba tare da junan mu ba, duk yunwar da mutun ke ji dole sai an tattara an haɗu a table aci a tare, don haka kawo min coffee kawai, zan jira brothers ɗina su dawo sai mu ci dinner a tare," Wannan haɗin kan nasu ya burge sehrish sosai, suna son junansu, juya wa tayi, taje da tadawo hannunta dauke da cup din saman ɗan plate ɗin da ake aza sa, miƙa masa tayi tana kallon fine face ɗinta, Ƙarba yayi tare da faɗin"thanks" komawa dining room ɗin tayi, tana goggoge chairs ɗin dake kewaye dashi, daga inda take tana satar kallonsa shi da yake zaune a falo, Bayan ta kammala ta koma kitchen ɗin, azmi ta samu tana a ciki tana ganin ta ta ce "yawwa mlm tukur ayi maza a fara jera abincin a dining ko," sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya, azmi tace "gsky hajjaju yar daru ce! da ita duk aka shirya wannan ƙaryar," murmushi kawai sehrish take yi tana wasa da yatsun ta, Ba tare da bata lokaci ba, suka soma shirya abincin, tana kaiwa tana jera masu, Ƙiris ya rage a fara kiran sallar magrib, bayan sun girma shiryawa azmi ta wuce ɗakin ta , sehrish kuwa falo ta wuce, anan ta samu Junaid yana sharar bacci, ya mimmiƙe kafafuwansa a saman doguwar kujerar, Alhamdulillah thanks to Allah ta fadi hakan, ƙyalle ido tayi ta ga inda ya ajiye wayarsa saman chest ɗinsa, Cikin sanɗa ta soma tafiya a hankali a hankali take takawa, har ta idasa isa gabansa, leƙa fuskansa tayi kyakkyawa mai annuri, dimples ɗin nan nasa a lotse, kamar ba bacci yake yi ba, Hannu takai a hankali ta ɗauki wayar tasa cikin rashin sa'a ta zame daga hannunta ta faɗi kasa ta daki haɗaɗɗen tiles ɗin dake kasa, har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113