Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Abban Sojoji Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

karanta message ɗin sai ya tura masu da "Send me your account number,' ganin wannan saƙon cikin zumuɗi jahad ta zari hijabi don tashiga gidan makwabtansu saboda yarinyar gidan nada account number su nan basu dashi, kafin ta dawo husanna tafarka daga bacci saboda cikinta daya katsa, ta soma laluben waya saboda toilet ɗin akwai duhu irin na gargajiyar nan ne ginin ƙasa, nan ta samu yar nokia ɗin da jahad ta ajiye a saman jakar kayansu taɗauka ta shiga da ita toilet ɗin, to ka'ida in ta kunna fitilar wayar ta zukunna sai ta fara buga game tana sukuni, Tana cikin zuƙunno nan wani ƙaton kyankyaso mai fiffike yayi tsalle sai saman kanta, cikin firgici ta tashi a razane nan take wayar dake hannunta ta sulale daga hannunta ta faɗa cikin ramin masan Subhannallah, Can ance a turo account number nan kuma wayar da suke da ita kwalli kwal ta faɗa cikin masai, Zaro ido tayi tare da buɗe baki saboda tsoro, taji haushin kyankyasan nan har taji cewa bazata kyalesa ba dole ya mutu, Nan suka shiga sintiri ita dashi shidai wings ke gare sa, ita kuma da ƙafa take binsa sai faman tashi sama yake yake yi tana binsa da gudu, hada ɗauko takalmi tana kokarin kwaɗesa, Baki a washe jahad ta shigo ta samo account number ɗin yarinyar ta rubuta mata a farar paper, ɗakinsu ta shiga tana neman waya, sama ko ƙasa babu ita ta shiga lalube ko'ina babu, tashiga mamakin ina aka kai wayar bayan babu, tunawa tayi da cewa tabar husanna a kwance tana bacci tabbas tana wurinta , fita tayi cikin saurin tsakar gidan Adai dai lokacin Husanna tafito tana sauke ajiyar zuciya tace"wash Allah da ace ban kashe shi ba dana binne kaina,' "Husanna ina wayar nan take"? jahad ta jefa mata tambaya ita bama ta lura da ita ba sai da tayi magana, nan fa tashiga wurga ido na mara gaskiya shiru tayi tana kallon ƙasa, hakan ba ƙaramin tayarwa jahad da hankali yayi ba, saboda akwai abunda ko ba'a faɗa maka ba zaka fahimta ne ta yanayin mutun,😿*🔥ABBAN SOJOJI🔥* *writer* *HAFSAT BATURE* ~Boss Lady~ *page* *39 to 40* 😁 jiki na rawa ta ƙarasa gabanta cike da tsoro tace" husanna ina waya ? Shiru tayi tana mazurai, hannu jahad tasa ta shaƙo wuyan rigar dake jikinta cikin matsanancin tashin hankali ta sake cewa "tell me where did you kept it ? muryar na rawa husanna tace" wani kyankyaso ne ya hau mun saman kaine shineee...sai wayr ta faɗa cikin....' "Cikin Uban me !? jahad ta tambaya cikin daka mata tsawa, duk tabi ta gama firgita tata cikin takura tace "cikin ramin" Aikuwa rai a tsananin bace jahad ta shiga kai mata bugu ta ko'ina, nan suka shiga dambe, faɗa ya katse me a tsakaninsu kai kace basu son junansu, A ƙarshe jahad tasake ta cikin tsananin ƙunar rai tace"shikenan kinyi farin ciki ko? kada kiyi tunanin ina bakin ciki ne don kin jefa waya, ina bakin ciki ne saboda kinyi mana babbar asara, taimakon da zamu samu na kuɗi a siya miki magani mun rasa, sannan ƴar uwarmu ma mun rasa ta ! saboda daga ni har ke ba wanda ya riƙe numbar da take kira, sannan ita inta kira zata ji waya a kashe kinga shikenan tamu ta ƙare.....' Zuƙunnawa tayi tare da fashe wa da matsanancin kuka, itama husannar koma tayi ta tsaya jikin bango tana shesshekar kuka jin jahad tace sun rasa ƴar uwarsu SEHRISH A cikin wannan yanayin mara daɗi tsohuwa ta same su, shigowa tayi hannunta ɗauke da bakar leda wadda fura ce aciki ta samo musu don su sha tun safe rabonsu da abinci har izuwa yanzu da ake ta faman kiran sallar isha'e hankali a tashe ta ƙarasa inda jahad take tana faɗin"lafiya meya faru ƴa'ƴan ne me kke wa kuka? Nasan yunwa ce ku kwantar da hankalinku gashi nan na samo mana ƴar fura musha,' Jin wannan maganartata yasa jahad ƙara sautin kukan nata, tana kuka tana magana "ba wannan zararriyar bace nasamu sehrish tace mu tura mata acct number, nashiga gidan makwabtan mu wurin mamee nace taban nata acct number ɗin, sai da na anso ina shigo wa nasamu husanna wai ta jefa wayar cikin masai," Jin wannan maganar yasa tsohuwa sakin ledar furar dake hannunta, tashiga tafa hannu tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan ae kun gama dani shekara 10 kenan wayarnan da ita nake lallabawa ashe kune ajalinta, kun kyauta,' tana faɗin hakanan ta shige cikin ƙuƙuƙun ɗakin nata ta rufo kopa, tunda suka ga hakan yatabbatar masu da cewa ran tsohuwa ya bace, saboda bata taba yi musu haka ba, Gashi ɗaki ɗayane a gidan ɗayan ɗakin ya rushe sakamakon ruwan sama da akayi, ga wani irin sanyi a wajen nan da nan jikin husanna ya soma kakarwa, hankali a tashe jahad ta tashi daga zukunnawar da tayi ta tunkare ta, "zo muje mu lallashe ta tabuɗe mana ɗakin mu kwanta waje sanyi," Haka suka je bakin kopan ɗakin sukai ta kwankwasa wa amma tsohuwa tayi shiru babu alamar zata buɗe, A ƙarshe sai dai suka rungume junansu suka ƙanƙame juna saboda sanyin dake akwai, wannan abun ya tuna musu da wani lokaci daya shuɗe a rayuwarsu mara daɗin ji 😭 Rashin gata baiyi ba a duniya Story by (Hafsat Bature) Rashin kwanciyar hankali yasa ko kwakkwaran bacci bata samu ba a daren jiya, tunaninta meyasa samu wayar tsohuwa ba'a samu tayi tarying amma swich off, hakan na matuƙar tayar mata da hankali tsoronta kar ace wani abu ya same su su duka, Jiki a sanyaye ta kammala shiryawa ta wuce kitchen wurin azmi, "Good morning aunty azmi" ta faɗa tana kallonta, azmi dake faman gyare gyare a kitchen ɗin tace "morning baturiya hope u slept well" yar dariya sehrish tayi ta shiga daga ciki tana faɗin "dame zamu fara ne? Azmi tace "yau fa akwai manyan baki da zasu zo," dafe ƙirji sehrish tayi kamar wadda taji mugun abu tace"suwa!"? dariya axmi tayi ganin yadda ta ɗan raxana, "suna da yawa wasu yau zasu zo wasu sai gobe, daga ciki akwai chief of army staff wato Abban su junaid wanda zai dawo daga ƙasar chaina, amma shi gobe ne zai zo yau dai wasu daga cikin manyan ƴa'ƴansa dake other states ɗin zasu zo domin tarbarsa, Da buɗan bakin sehrish sai cewa tayi "Babban yaya fa shi bazai zo ba,"? girgiza kai azmi tayi tace"oh shirt! ni wannan babban yayan da kike ta faman zumuɗin gani bansan dalili ba,' "Aunty azmi it's just a question ba wani abu ba, naji kince manyan ƴa'ƴansa shiyasa na tambaya,' ta ƙara maganar tana wasa da yatsun hannunta, Kafin azmi tace wani abu junaid ya shigo da sallama, nan fa sehrish ta hau satar kallonsa yayi fes abunsa yayi dressing cikin suit black colour A cikin zuciyarta tace "wai madarar kyau" "Morning azmi how was everthing" ya faɗa shima yana ɗan satar kallon sehrish, Azmi tace "barka dai komai lafiya kana buƙatar wani abu ne"_? sam baiji me tace ba domin idonsa nakan sehrish wadda ita ma shi take kallo, Sai da ta maimaita da cewa"junaid ina magana"? a ɗan firgice ya mayar da kwayar idonsa kan azmi da ɗan

Table of Contents

Chapters

113 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113