Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Abban Sojoji Book One Complete Hausa Novel 1,095 words 0 views Progress saved
Download Book

ta koma kamar d'an chali chali , ga gashin bakin da suka sanya mata , ya hau radau ya zauna , haka jagirar da suka samata , ta zauna cuf , duk wani abu na ado na jikin y'a mace babu shi a tattare da ita yanzu , Shin koya wannan wasan kwaikwayon zai kasance ? mezai faru ranar da suka gane cewa sehrish macace ba namiji ba ? Kowa yasan ya sojoji suke 👊. Tunda a sussuba suka kama hanyar zuwa abuja , ita da hajjaju , zuciyarta sai dar dar take yi mata , a natse hajjaju ke driving dinsu , yayin da sehrish ke gefenta , idonta nakan glass din motar , tana kallon yadda suke wuce wurare daban daban , zahiri tana kallon bishiyoyin da suke giftawa na cikin dajijjikan da ke a side road kamar suna gudu da kafafuwansune , a hankali zuciyarta ta sauya mata akalar tunaninta izuwa rayuwarsu ta baya , nan take taji wasu zafafan hawaye na sintiri a idonta , zuciyarta ce ta soma yi mata magana "Sehrish kowane d'an adam yana da irin tasa kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa ne domin ya gwada imaninsu , kiyi kokari ki cinye wannan jarabawar , ki rungumi kaddara a duk yadda tazo miki dama can rutacce ne daga Allah dukkan tsanani yana tare da sauki ! Allah yana sane daku kuma shine gatanku ," Hannu tasa tana clearing face dinta saboda bata so hajjaju tagani , tunanin y'an uwanta shine yafi komai tayar mata da hankali , bata san wani gidan mahaukata bane zasu juri daukar nauyin haukan ta ba idan akace yau husanna tarasa ranta , haka abubuwa suka dinga zuwa mata aranta har suka isa garin abuja, wuraren karfe 2:30 na rana , Wannan ne karo na farko da ta fara yin tafiya mai nisa irin wannan , tunda suka shiga take kallon manya manyen gine gine , har suka iso gidan da zasu wato gidan Abban sojoji , sehrish ta razana da ganin katafaren ginin mai matukar girman gaske da daukar hankali , irin gidan da ta saba gani a cikin mafarki, Lokaci da idonta suka sauka kan Narka narkan sojojin dake tsare da babban gate din gidan sai da taji gabanta ya fadi rass , bakake ne wulik dasu sanye cikin uniform dinsu , ga bindigu rike a hannunsu , ga wasu guns din soke a west dinsu , Wani irin miyau ta hadiye ganin an tsaida motarsu , nan take taji zufa na gangaro mata ta cikin sumar kanta , guda biyu ne suka karaso inda motar tasu take , d'aya ne yasa hannu yayi knocking , hajjaju ta zuge glass din , ita kanta a tsorace take cikin en ena tace "barka dai sannu ku da aiki ," amsa yayi da "yawwa muna bukatar sanin daga ina kke kuma wurin wa kka zo "? Da sauri hajjau ta dauko wayarta cikin yar purse dinta ta shiga neman number abban, yatsun hannunta sai kakarwa suke , kira d'aya tayi masa ya daga , bayan sun gaisa ta sanar masa da abunda ke faruwa, ya umarce ta da ta basu wayar , mika musu tayi daya daga cikinsu yasa hannu ya karba tare da karawa a kunnansa , juyawa hajjaju tayi tana kallon sehrish wadda tuni ta ta gama tsuma , ta nannade wuri d'aya ta matse jikinta , idon nan sunyi furi furi kamar wadda tayima sarki karya , muryar sojan taji yana cewa "take your phone , u got permission to go in , but firstly we must check the car ," kallon sehrish tayi tare da cewa " mu fita zasu bincika motar ," bude mota sehrish tayi ta fita , itama hajjajun ta fito , suka tsaya suna jiran su gama binciken nasu , Matsawa Sehrish tayi kusa da hajiyar tayi kasa kasa da murya tace "hajiya amma nan barrack din sojoji ne ko "? cikin rashin natsuwa hajjaju tace " A'a gida ne na sojoji dae not a barrack ni bana cikin kwanciyar hankalin wadannan sojojin sun firgitani , sai kace wasu masu safarar miyagun kwayoyi za'a tsare mu ! that's why ban cika son zuwa gidannan ba ! ," takarasa maganar tana yatsina fuska , Jikin sehrish ya gama yin sanyi , bin jikinta tayi da kallo tasha kayan maza , ga uban burgujejan wandon da tasa kamar zata tashi sama, kara kankame jakar dake hannunta tayi wacce ke kumshe da y'an kayan da hajjaju ta bata kyauta , Hatta purse din hajjaju sai da suka bincika , zuciyar sehrish sai bugawa takeyi tunanin ta masu gadi sun kasance haka da ban tsoro ina ga y'ay'an gidan da taji ance they're all soldiers 😒 Muryar sojancce ta ratsa kunnanta "lemme see your bag "! cikin sauri ta mika mar jakan , zazzago kayan ciki yayi kasa yana duddubawa , trousers ne da riguna na maza , da hijabai da ta kudundunesu saboda sallah , bayan ya gama checking dinsu ya dago ya zuba mata ido yana kallonta , nan take taji fitsari ya cika mata mararta , sunnar da kanta tayi kasa , jikinta na rawa , Ji tayi yasa hannunsa ya dankwashi kanta yana cewa "mara kunya kana namiji baka iyasa Cap akan ka , kai ga d'an daudu ko ? sai dai kasa abu na mata ka nannade kai kamar wani limamin masallaci ", Karasa maganar yyi tare da wurga mata jakar , sannan ya juya ya tafi , hannu tasa ta dafe wurin don taji zafin rankwashinta da yayi mata wannan gabjejan hannun nasa , dole ita ta zukunna ta kwashe kayanta daya zubar a kasa , A karshe dai Sun sami shiga ciki , a jiyar zuciya Sehrish tasaki , time dinda motar tasu ta wuce babban gate din ta shantalelen titin da zai kai ka can cikin gidan , A hankali take bin ko ina da kallo ta cikin glass din motan , tana kara jaddada haduwar ginin , taga wurare daban daban masu ban sha'awa , sai ta dinga tunanin cewa kodai tabar nigeria ne domin daga inda kasa kafarka cikin gidan kamar ka fita daga 9ja ne 😔 ihu da sowar da taji ne yasa takai idonta wurin , y'an matasan samari ne kyawawan gaske suke wasan football , acikin playing field n gdn , gwanin burgewa tabisu da kallo har sai da suka wuce su , A wurin da aka ware na parking space , hajjaju ta tsaida motarsu , wurin cike yake da motocinsu Na gayu ga kuma jibjibgan motocin irin na sojojin man Waigawa hajjau tayi ta kalle ta tace "sehrish ki natsu dan Allah in mun shiga kada ki jamun , kuma kada ki manta sunan ki tukur daga ynx ," cike da gamsuwa ta masa mata da "Toh" Fitowa sukayi daga motan suka miki hanyar data zata sada ka da babban falon gidan , tuni sehrish ta raina kanta , tamkar karta taka kasan tiles din take ji saboda wani irin design ne mai daukar ido , duk yadda ka taka saiya bada sauti kwas kwas , Komai na cikin living room din mai tsadar gske ne , kana gani kasan bana nan bane , an kawata shi da expensive furnitures

Table of Contents

Chapters

113 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113