Chapter 83
Chapter 83
saude kuwa aza hannu tayi akai tana faɗin"goggo dan Allah kidaina !! Kidaina zaginsu mana akan abunda basu sani baaa...... tunkan ta ida goggon tasa hannu ta buge mata baki, dafe baki sauden tayi don taji zafin bugun, Ci gaba da magana goggon tayi a birkice tana kuka, " Ae dama nasani ba wanda zai goyi bayana akan magana ta, amma ni nasani wlh ku ƴa'ƴan ZAINABU ne, dama haka uwarku take kamar ku ɗinnan, shegen taurin kai da kafiyar tsiya, kunnan ta kamar na zomo, fitinanniyar yarinya ƙiri-ƙiri ta guji jini na, dama sai da nace mata cikin jikinta na Abusufyan ne amma taƙi yarda ae dama nace mata jiki magayi amma taƙii ji, kunnan ƙashi ko ae ynx nasan taji jiki bawan Allah bai mata komai ba amma taƙisa, wlh cikinsa ne ku ƴa'ƴansa ne amma kunƙaryata ni, ga falo falon kunnuwanku nan irin na abusufyan shima dayake baijin maganata kangararre ne yaƙi jin magana ae gashi nan...... Zuba kawae goggon katsina takeyi ba ƙaƙƙautawa kai kace radiyon da bata da saiti, notikan kanta sun kwance sai faman zazzaga musu bala'e take yi, tana yi musu magana akan mutanen da basu san da zamansu ba, tashi su kayi atare su ka tsaya suna kallonta haƙika sun tsorata da tsohuwar tuni idonsu ya cicciko da kwalla, Goggon katsina bata dakata da surutun ba har sai da Saude tace "goggon kiyi hakuri dan Allah, nima na yarda cewa su ƴa'ƴan Uncle sufyan ne, sai yanzu na ƙara lura da kamannin nasu dagaske ne abunda kika faɗa, saude na gama faɗan maganar ta kalli su hosana tayi musu alamar su amince suma da maganarta don asamu ta lafa, Cikin sauri suka zube saman guiwowinsu agabanta tare da cewa "Dan Allah kiyi haƙuri goggonmu, munyi miki laifi, tabbas mu jininki ne mu ƴa'ƴan abusufyan ɗinki ne, ki yafe mana munsa kin zubda hawayenki," Sanyi goggo taji aranta dama ita burinta kawai su amince cewa su ya'yansa ne, hannu tasa tana share hawayenta, bayan ta kammala ta miƙa hannayenta tare da ruko nasu ta tsayar dasu tsaye fuskarta da murmushi sai kace ba wadda tagama sharbar kuka tace " Alhamdulillah har hankali na ya kwanta ynx, amma fa kun wahalar da gaggonku sosae kun sani ina ta faman zubda hawaye na, da ace abusufyan na nan kuma yasan abunda ku kayi ma goggonsa tabbas sai ya muku dukan tsiya" , Sunnar da kai su kayi tare da cewa "ayi mana afuwa goggonmu, bazamu ƙara ba insha Allah," Murmushi tasaki tare da cewa " ku koma kuzauna ƴa'ƴana, yanzun nan zan kira mahaifinku a waya ku gaisa," 🙆♀️🙆♀️🙆♀️ BossLady❤️ Inaso naji ta bakin ku game da annoucement ɗina nasan kowa ya karanta, sannan comment akan page ɗin yau 👏👏👏 *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ🌹❤️ *Mallakin* *🌹Hafsat Bature Moh'd*🌹 ~BossLady~💋 Page 81-82 part 2 *Meaning of name sehrish is an arabic name, ma'anar sa kuma Glamorous Personality* 🌹 Har haɗa baki suke yi wurin cewa "mahifinmu kuma ! A waya !?. Da ƴar dariya a fuskarta tace"Eh mana, ae kullum sai ya kira ni mungaisa,' tayi maganar ayayin da ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinta don ta ɗauko wayarta, Hannu suka aza akai alamar sun shiga uku, ita kanta saude tama rasa me zatayi abun ya ɗaure mata kai, lamarin goggo sai addu'a tsufanta da rigima yazo mata, "Kada ku damu kunji kawai, ku kwantar da hankalin ku, in ta kawo muku wayar ku amsa ku gaisa dashi amatsayin mahaifinku, Uncle sufyan ya riga da yasan rigimar Goggonmu wayayye ne shi zai fahimce ku," Saude ce tayi musu wannan bayanin, jiki amace suka amsa mata da cewa "Toh," Sannan ta juya ta koma kitchen saboda tabar girki saman gas, Zuru su kayi suna jiran zuwan gaggon katsina da waya, babban tashin hankalinsu yarda zasuyi waya da mutumin da goggo ta ƙaƙaba musu a matsayin mahaifinsu wanda basu ta6a gani ba kuma basu san kowanene shi ba," suna nan zaune zuciyarsu nata bugawa sai ga goggo ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da waya sai faman zabga murmushi take yi, Koda su ka ganta gabansu ne ya faɗi rass don su a tsorace suke, Miƙa musu wayar tayi tare da cewa "Maza ga mahaifinku nan akan layi kuyi masa magana," Kamar bazasu kar6a ba haka su kayi daker Jahad tasa hannu ta karbi wayar goggon tare da karawa a kunnanta tace ,"Assalamu alaikum," daga can 6angaren taji wata natsattsiyar murya ta amsa mata da cewa "Wa'alaikum salam," sai da jahad tayi jimmmm kafin ta daure ta cije tace "Abba Jahad ce ɗiyarka, ina fata kana cikin koshin lpy," Abusufyan ya amsa mata da cewa "lpy lou Alhamdulillah My daughter, kin yi missing ɗin abbanki kuwa,"? Yanda yayi maganar ba ƙaramin kashe ma jahad jiki yayi ba, sai kawai taji hawaye na ƙokarin zubo mata, Murya na rawa tace "Nayi missing ɗinka sosae abbana, ina kewarka," tayi maganar ayayin da take dab da fashe wa da kuka, cikin sauri tace "Abbana ga hosana ku gaisa, itama tayi kewarka sosae," "Okey bata wayar," ya umarce ta, Miƙawa hosana wayar tayi jikinta na kerma, hannu hosana tasanya ta karbi wayar tare da karawa a kunnata, duk goggo na tsaye tana kallonsu sai faman murmushi take yi, (ta haɗa Bomb) Tashi jahad tayi cikin sauri ta wuce bedroom ɗin saude tana shesshekar kuka tana idasa shiga ɗakin ta faɗa saman gado tare da fashe wa da matsanancin kuka, bakomai bane ya karya mata zuciya ba face tunda suke arayuwa basu ta6a sanin daɗin soyayyar mahaifi ba ga Uban amma bai da amfani," A can kuwa tun da hosana tasanya wayar a kunnanta tace "Abbana dagaske kaine mahaifin mu kamar yadda goggo ta faɗa," On the other hand abusufyan yace "My daughter are u doubting abt ur father? nasan kinyi kewata ne shiyasanya kike kokwanto akaina," aikuwa jin ya tabbatar mata da cewa shi mahaifinsu ne yasanya ta fashe masa da kuka tare da cewa "dama nasani kaine mahaifinmu, ba wancen mugun ba, sai da nace ma Oumma mu bamu kama dashi mummunane shi mai baƙar zuciya amma taƙi yarda, ni nasani ba abban mu bane, babu uban da zaiyi wa ƴa'ƴansa haka, kaine mahaifinmu,......" Katseta yayi tare da cewa "Silent pls, sorry my daughter bana fahimtar zancen ki i was busy now, zan kira anjima,' yana gama faɗan hakan ya kashe wayar saboda baisan inda zancen nata ya dosa ba, shi dai kawae ya amsa kira ne kamar yadda goggonsu ta sanar dashi cewa ƴa,ƴanshi sun zo, sarai yasan rigimarta shiyasa yabisu a hakan, Ganin ya katse kiran yasa hosana fashewa da kuka, wurgi tayi da wayar goggon saman kujerar sannan itama ta miƙe tana ci gaba kuka ta wuce ɗakin saude, Jikin goggo yayi sanyi, ita a tunaninta abusufyan bai kula da yaransa shiyasa suke kuka, don haka taci alwashin zata sashi dole saiya zo nigeria ya ɗauki ƴa'ƴansa ya koma dasu can qasar da yake zaune, a ranta tana cewa "in banda shiririta irin ta abusufyan ka kama hanya ka tafi ƙasar Turƙiya kabar yara cikin damuwa, gashi nan sai faman kuka suke yi, Allah ni da kai ne, saina sanar wa AMMI halin da ake ciki, Ta idasa maganar tata tare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113