Chapter 37
Chapter 37
ina matuƙar tausayawa waɗanda basu da uwa atare dasu basu da wani nasu a kusa da zai kasance tare dasu aduk lokacin suga shiga hali irin wannan Allah sarki much love to our mothers & sisters and so on , Addu'o'e kawai take jero wa daga bakinta tana neman sauƙi a wurin Allah, raɗaɗi iri iri ga matsananciyar damuwar dake damuwanta, wa zata kaiwa kukan ta in ba Allah ba ? A wannan halin wani baccin ya qara ɗaukanta, tun da suka dawo daga masallaci kowa ya koma bedroom ɗinsa wasu suka koma bacci wasu kuma suka kama karatun ƙur'ani kowa da kiwon daya kar6e sa, gaza samun natsuwa yayi tunda ya dawo tunaninsa wane hali yarinyar take ciki? ga kuma promise ɗin da yayi mata nacewa da safe zata ga sako a matsayinsa na bakin aljani, Cikin sauri ya buɗe closet ɗinsa jerin kaya ne iri iri masu tsadar gaske, gidan ƙasa ya duba jerin sababbin barguna ne da zanin gado, hannu yasa ya zaro blanket ɗaya da bedsheet ɗaya sababbi fal masu kyau da tsada, ajiye su yayi a saman bed ɗinsa, gaban dressing mirror ɗinsa ya koma a cikin drawer ɗin dake haɗe da madubin ya janyo gida na farko, Katan katan ne na kwalin sabulu masu kyamshin gaske, dozen ɗaya ya ɗauko tare da wani haɗadden soson wanka acikin ledarsa, a saman blanket ɗin ya ajiye su, Zuba musu ido yayi yana kallo yama rasa me zai yi gani yake kamar sunyi mata kaɗan, sam bayaso ta gane cewa shi ba aljani bane , fita yayi ya wuce ɗakin da suke ajiyar magunguna iri iri da allurar da sauransu tamkar patient room haka yake , saboda suna da military doctor & nurse hakan yasa suka buɗe ɗakin don ko mutun bai lafiya za'aya iya duba sa acikin gidan, yasan cewa dole ta tashi da ciwon kai saboda kukan da tayi kuma dole ta tashi da ciwon ciki, don haka ya ɗauko mata magungunan da yasan zata samu relief, ya zura cikin aljuhun rigarsa, Duk hakan bai ishe shi ba, yana ji aransa cewa dole ta buƙaci abinci akwai yunwa a tattare da ita, Komawa ɗakinsa yayi cikin sauri ya rungumo kayan da ya ajiye a saman gadonsa ya fito dasu, Ya ci sa'a ba kowa har yanzu gari bai idasa washewa ba suna can suna sharar bacci, Lalla6awa yayi a hankali ya wuce bedroom ɗinta tsayawa yayi a kopan ɗakin saboda baiso ace idonta biyu, kasa kunnansa yayi yaji shiru ba motsin komai ɗan tura kopan yayi ya leƙa yana kallonta, Kwance take idonta rufe alamun bacci take amma jikinta sai rawar sanyi yake a haka ta kwana tun jiya dama da bedsheets ɗinta take lullu6a kuma ta 6ata sa, ga tsoron baƙin aljanin daya ziyarce ta daren jiya duk shi ya firgita ta tarasa kwakkwaran motsi balle ta ɗauko wani abu tayi covering jikinta da shi, Ajiyar zuciya ya saki, cikin sanɗa ya kutsa kai ya shiga yana takawa a hankali a gefenta ya ajiye mata kayan, sannan ya zaro lallausan blanket ɗin ya rufa mata a jiki a hankali, har cikin ranta taji shi gaba ɗaya har kanta ya haɗa ya lullu6e mata, sai gata tsulum acikin bargon kamar wata new born baby, smilling yayi alokacin da yaga ya kammala sa mata batare da ansamu matsala ba, Yana fita ya wuce ɗakin azmi tsayawa yayi bakin kofa yayi mata knocking, "Shigo ciki" Ta faɗa daga ciki kutsa kai yayi ya shiga, zaune ya same ta saman sallaya da ƙur'ani a hannunta alamar karatunsa take yi, murmushi tasaki ganinsa tare da cewa "junaid yau kaine a ɗakina i forgt when last ka shigo min,' bai bata amsa ba sai da ya Samu wuri ya zauna agabanta ya lankwashe kafa sannan yace "barka da safiya dafatan kun tashi lafiya,' "Lafiya lou Alhamdulillah ince ko lafiya,' ? ta tambaya tana kallonsa don tasan dalili kawai ke kawo su wurinta, Cikin natsuwa ya ce "meya faru jiya baki fito ba wurin dinner ɗin mu,' "Bani da lafiya ne dama na faɗawa tukur meyasa ka tambaya,? ta faɗa tana kallonsa, murmushi junaid yayi yana kallon azmi ya ce "nasan komai fa ynx!" Ji tayi gabanta ya faɗi duk da batasan me yake nufi ba cikin nuna rashin fahimta tace" me kake nufi da kasan komai junaid? "Ina nufin na gane cewa tukur ba namiji bane maca ce kuma nasan kinsan da haka azmi," shiru azmi tayi tare da yin jigum tana kallonsa ƙarya ta ƙare amma sanin cewa junaid ne yasa bata tashi hankalinta ba saboda sauƙin kansa, "taya akai ka gane hakan"? ta jefa masa tambaya, "Jiya bayan fawan ya bata punishment sakamakon kuskuren 6arawa Ayaan ruwan zafi a hannunsa,' Nan junaid ya kwashe duk abunda ya faru daren jiya ya sanarwa azmi, hankalin azmi ba ƙaramin tashi yayi saboda ita batasan duk wannan budurin da akayi ba da ace tana kusa da bazata bari fawan ya hukunta sehrish ba, a wani 6angaren kuwa taci dariya sosai jin shiriritar da tayi daren jiya don junaid bai 6oye mata komai ba, dakyar ta tsagaita dariyar da take tace masa "ynx me ka yanke akan yarinyar zaka sanarwa yan uwanka cewa maca ce ita ?. girgiza kai junaid yayi tare da cewa "a'a korarta zasu yi nasani koda zasu sani ba yanxu ba sai sun saba da ita sosai, ni ma kuma bazan bari tasan na sani ba insha Allah,' azmi taji daɗin hakan dama tasan hakance zata faru domin junaid yaron kirki ne duk cikin yan uwansa tafi sonsa ji take kamar ita ta haifesa saboda yadda yake respecting ɗinta, "Ya sunanta'? Ya tambaya yana kallonta azmi tace" sunanta SEHRISH" short smile ya ɗan saki kafin yace" ynx azmi pls ki taimake ita, nayi mamaki jiya alamu sun nuna cewa bama tasan menene menstruation ba, tasha wahala sosai akwai kayan da nakai mata pls kice ke ce kika kaimata, sannan ga magani nan ki bata ta sha amma kafin nan ki sama mata abunda zata ji saboda akwai yunwa atattare da ita," ya ƙarasa maganar yana sa hannu cikin front pocket ɗinsa ya zaro maganin ya miƙa mata, ajiye kur'anin tayi akan sallayar kafin tasa hannu ta kar6a tana cewa "kada ka damu insha Allah komai zai tafi dai dai nima ina ji araina tabbas akwai damuwa a tattare da yarinyar, a yanayin da kafaɗa min abunda ya faru jiya ya tabbatarmun da cewa tarasa wani 6angare na ilmi arayuwarta sakamakon wani dalilin,' Har cikin ransa ya ƙara ganin girman azmi a idonsa, itama taga farin ciki a fuskan junaid wannan ya tabbatar mata da cewa akwai wata a ƙasa, Murmushi tasaki kawai Yunƙurawa yayi ya mike ya kama hanyar fita har yakai bakin kopa ya sake jiyowa ya kalli azmi yace"pls & pls take care of her,' Dariya azmi tayi ganin yadda ya susuce aranta tace tun ynx daga daren jiya kawai, Shima fice wa yayi yana murmushi yanzu ya samu natsuwa don haka ya koma bedroom ɗinsa ya kwanta yana jiran safiya ta idasa yi koya samu yaga wannan kyakkyawar yarinyar, Sehrish Motsin mutun da taji a kusa da ita ne yasa ta farkawa tayi mamakin ganinta cikin bargo sai tayi tunanin cewa ko mutuwa tayi ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113