Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Abban Sojoji Book One Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

dumi akwai wanda ya zo ba na nan?" Ta yi maganar ne a yayin da take bude kofar motar ta baya, saboda ba ita kadai ta zo ba akwai 'yammatan da ta zo da su daga kyauye. Maigadin ya amsa mata da cewa "E mutane sun zo sosai amma duk ban rike shunansu ba na dai ce musu ba ki nan kin yi tafiya, sai dai akwai yaro d'aya da ya zo neman ki kullum shai ya zo yau dai na ce mashi ya jira ki dawo." D'aga idonta ta yi tana hangen 'yar yarinyar da ke sanye da hijab saman sallaya, mayar da idonta ta yi kan 'yammatan da ke zaune cikin motar, ganin ta bude musu motar amma sun ki fitowa, tsaki ta ja tare da cewa, "Kwana za ku yi ne a cikin motar?" Washe baki su ka yi wata mai surutu a cikinsu ta ce, "Hajiya wallahi dadi motar nan ga wani sanyi da ke ratsa zuciyata kamar kada na fito." Girgiza kai hajiyar ta yi tare da sakin guntun murmushi ta ce, "Ai irin wannan sanyin da kuke sha na A.C ne kuma in mun shiga ciki ma akwai A.C ko ina." Cike da jin dadi suka fito daga motar su biyar ne, kai ka ce wadanda aka kwato ne daga bakin kura kayansu sun yi uban squeezing, ga shi riga daban zane daban dankwali daban, takalman kafafuwansu wari da wari ne, ga wata irin kwalliya da suka dambara a fuskarsu, janbaki ya sauka daga saman labbansu har kumatunsu, kamar wasu mayu. Ga black point din da suka diddiga a hancinsu har izuwa goshinsu, sai faman soshe-soshen kai suke. A haka take dauko su daga kauyen kayau ta gyara su ta sama masu gidanje aiki, a nan take samun kasonta ita ma. Kallon buzun ta yi ta ce "Ka shigo mini da yarinyar." Sannan ta kalli 'yammatan ta ce "Mu shiga ciki amma kusa ni duk wacce ta yi mini hauka kauyensu zan mayar da ita ta je can ta ci gaba da tallar fura a bakin kasuwa." Cikin falo ta shiga da su a daidai lokacin ita ma yarinyar ta biyo su, nan fa suka fara kalle-kalle ganin yadda wurin ya hadu, har kokawa suke yi wurin yunkurin hawa saman lumbutsa-lumtsan kujerun da ke a ciki, dakatar da su ta yi ta hanyar yi musu tsawa, "Kul! Kada wacce ta hau mini saman kujeruna, ga carpet nan shimfide ku zauna, haba ku rinka abu irin na mata mana." Nutsuwa suka yi kowacce ta samu wuri ta zauna, ita da ma ba iri su ba ce da wayewarta wuri ta samu ta zauna ita kadai, yayin da su kuma suka cunkushe wuri daya kamar kifin gwangwani. Shiga ciki hajiyar ta yi tana kwalama mai aikin ta kira, "Larai, larai! Ina kika shiga haka gida sai ka ce ba kowa?" Karasowa ta yi tana hamma alamun daga barci ta tashi. "Sannu da dawowa hajiya, wallahi barci ne ya yi awon gaba da ni da ma na sha maganin mura saboda ta takura mini." Tabe baki ta yi ta ce, "Ni fa ban yarda da ke kullum shan maganin mura anya ba shaye-shaye kika fara ba?" Cikin zolaya ta yi maganar tana kallon ta, Dariya Larai ta yi ta ce, "Haba hajiya Allah ya tsare ni dayin shaye-shaye tsofai-tsofai da ni." Murmushi hajajju ta yi "Ya yi kyau! Yanzu dai akwai abinci gidan na zo da yara ne daga kauye." Girgiza kai larai ta yi, "A'a hajiya sam ban yi tunanin yau za ki dawo ba ai, da na girka muku abinci." A jiyar zuciya ta saki kafin ta ce, "Koma mene dai laifina ne da ban sanar da ke cewa yau zan dawo ba. Yanzu dai na san muna da bread, ko shayi ne ki hada musu da indomie." Amsawa ta yi da, "To hajiya!" sannan ta juya ta nufi hanyar kicin din. Hajiya ta nufi dakinta saboda tana bukatar ta d'an watsa ruwa ta canza kayan jikinta. Rokon Allah yarinyar take yi a cikin zuciyarta, Allah Ya sa ta samu wannan aikin ko ta samu ta taimaki 'yan uwanta wadanda suke cikin wani mawuciyan hali, muryar d'aya daga cikin 'yammatan nan ta jiyo tana mata magana, "Ke kin iya kunna kallo ki kunna mana mu kalla." Girgiza kai tayi alamar a'a, ba wai don ba ta iya ba sai don tsoron kada hajajju ta yi mata fada har ma ta kore ta ta hana ta samun aikin. Tana jin su suna cewa, "Karyar banza babu wani ta iya kawai ba ta kunna mana ne 'yar bakin ciki." Dagowa ta yi ta kalle su harara ta watsa musu ta ce, "E na iya ba zan kunna ba ne ba ku da hannuwa ne ku?" Tsit suka yi ganin yadda ta daure musu fuska sun yi tunanin 'yar shiru-shiru ce, ashe ita ma ta iya fada. Fitowa hajjaju ta yi jikinta sanye da kayan barci, riga da wando ruwan madara, ta daure gashin kanta da ribbom, hannunta rike da waya kirar Infinix Hot 10, suna ganin ta suka gyara zamansu cikin natsuwa. Wuri ta samu ta zauna a saman 3 seater, yadda za ta ji dadin yi musu magana, yarinyar na jingine jikin 2 seater wadda ke bangaren dama su kuma suna duban ta ta sashen hagu. A nutse ta soma magana, "Ku na riga da na yi muku bayanin komai ko?" Da'ga kai suka yi alamar e. Ta ci gaba da cewa, "Yanzu abin da ya rage mini shi ne na koyo muku yadda za ku gudanar da aikin naku don ba zai yi yu ku je gidan mutane a matsayin 'yan aiki ba, a haka kaca-kaca da ku ba tsafta ba. Dole ne kusan yadda za ku tsaftace kanku, da tsaftar muhalli da kuma yadda za ku tsaftace abincin da za ku girka. Kuna bukatar sanin abubuwa sosai daga wajena, kuma insha Allah zan nusar da ku." Ta mayar da idonta kan yarinyar ta ce "Yammata kin yi shiru ga shi ni ban san ki ba amma yanzu ina son na san me yasa kike nema na ne?" Bude baki ta yi za ta fara magana amma ganin yadda 'yammatan kauyen nan suka zuba mata ido kamar zomaye, hakan ya sa ta kakare ta kama in ina. Muryar hajjaju ce ta sa su janye idonsu akanta, "Ku fa matsalarku ke nan sai shegen kallo salon gulma ko?" Sunkuyar da kansu kasa suka yi amma kunnuwansu na bude don su ji me za ta ce? Cikin sanyin murya ta soma magana, "Da ma na ji an ce kina taimakawa ki sama wa yara aikatau shi ne na zo ni ma ki taimaka ki samo mini don Allah!" Dafe kai hajju ta yi da hannunta na hagu ta ce "Kash! Da na san wannan ya kawo ki da tun dazu na ce ki koma gida saboda yanzu babu wadanda suka yi mini magana akan na samo musu 'yar aiki, wad'annan 'yammatan da kika gani su ne kawai suka rage na mika su ga wadanda na yiwa alkawarin zan sama musu 'yan aiki amma yanzu babu wani da ya yi mini magana. Ki yi hakuri 'yata!" Tamkar an d'aga guduma an buga mata a kai haka ta ji,

Table of Contents

Chapters

113 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113