Chapter 23
Chapter 23
cikin zuciyarta taji faɗuwarnan, tsadaddiyar waya irin wannan, dafe ƙirjin ta tayi tana kallon wayon, ƙarar faɗuwar wayar tasa junaid yunkurin buɗe idonsa daga baccin da yake, cikin sauri ta boye bayan hannun kujerar tana sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarsa yayi ya ci gaba da bacci, jin sakin ajiyar zuciyarsa yasa ta gane ce ya koma baccin nasa, hannu ta zura ta janyo wayar tana kallon screen ɗinta, Alhamdulillah ta fada ganin ba abunda ya same shi, Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye, tana kallon sa, ya aza hannunsa ɗaya a saman stomach ɗinsa, ɗayan kuma a saman kansa, abun yazo mata da sauƙi, don haka cikin sauri ta jona wayar a yatsarsa, nan take wayar ta buɗe, murmushin jin daɗi ta saki, wannan hoton ta sake gani a wallpaper ɗinsa na wannan haɗaɗɗen matashin saurayin, har ranta so take tasan wanene wannan sarkin kyawun nan, Ja da baya tayi a hankali tayi nesa dashi, izuwa gefen stair ta tsaya, contacts dinsa ta shiga ta rubutu numbar goggo, bugu ɗaya wayar ta shiga kuma aka ɗaga, cikin sa'a muryar jahaad taji tana kwaɗa sallama, da farin ciki ta ce"Jahaad ni ce Sehrish! banda isasshen lokaci pls listen to me," a can 6angaren jahad ta natsu tana sauraron abunda sehrish zata ce mata"Nasamu kuɗin aikin account number zaki turomin cikin gaggawa saboda na fadamiki wayar ta yaron gidan ce nake dauka shi kansa baisani ba," tsananin farin ciki ne yasa jahad yin ihu da fadin Alhamdulillah a cikin wayar tasu, ta ce "narasa inda zansa kaina don farin ciki ƴar uwa kice mun kusa barin asibitin nan dama wlh nagaji da zamansa...." sehrish ce ta katse ta ganin zata ja masu lokaci ga tsoran kar junaid ya farka "ke ba surutu zakiyi mun ba ki anso acct number ɗin likitan yanzu yanzun nan ki turamin kada fa ki 6ata lokaci asiri na zai tonu," Tana gama faɗan hakan ta yi rejecting kiran, ta tsaya nan tana jiran shigowar saƙon jahaad, jikinta har rawa yake gudun kar junaid ya farka, har leƙen sa take yi taga ko yana motsi, Safa da marwa tashiga yi kamar mai ɗawafi, Allah Allah take jahaad ta turo saƙon tayi sauri ta kwafa ta mayar masa wayarsa, tana nan tana jira, tajiyo ƙarar shigowar motarsu Ayaan,da wata irin jiniya motocin nasu ke shigowa, aiko nan take junaid ya soma motsi , saboda tsabagen ruɗu 😳, maimakon taje ta ajiye masa wayar ta ruga , sai ta haɗa da wayar duka ta watsa aguje sai bedroom ɗinta. Ana dara ga dare yayi 🐽tashi zaune yayi tare da yin miƙe, da hamma lokaci guda hannu yasa ya rufe bakin nasa, wayarsa ya soma lalube yaga bata nan bai kawo komai aransa ba sai yayi tunanin ko ya barta a room dinsa ne, Shigowarsu brothers ɗin nasa ne yasa shi, sakin fara'a , a jere suka shigo su 7, ƙarasa wa kanal yusif yayi ya russuna tare da rungumesa yace"barka da hutawa my bro ina fata kana cikin koshin lafiya," da fara'a ya amsa masa da cewa "am fine bro kun dawo lpy," kanal ya masa masa da eh, kafin ya wuce, shima khaleed karasawa yayi inda junaid ɗin ke zaune ya rungume sa tare da cewa"My sweet bro ya enjoyment," bai basa amsa ba sai murmushin da yayi masa, haka irfan da jabeer duk suka rungumesa kafin suka wuce ɗakunansu, Ya rage saura twins da fawan, harara fawan ya sakar masa tare da wuce wa ta gabansa yana rera waka cikin zolaya yake cewa"Lalatacce lalatacce ne ko a gidansu wannan haka yake," ɗaure fuska junaid yayi don ya tsani tsokanarsa da fawan ya ke yi, A tare Ayaan da Jahan (Masoya 😂) suka ƙarasa kowanne ya manna masa kiss a cheeks ɗinsa kafin suma suka wuce ciki, Shima junaid ɗin tashi yayi ya shiga ciki domin ɗauro Alwala saboda liman na ta kwaɗa kiran sallah, A bangaren sehrish kuwa, tana nan maƙale da wayar junaid a hannunta, zuciyarta na harbawa, sai zagaye ɗakin take tana faɗin, nashiga ukuna ynx ya zanyi in junaid ya nemi wayarsa ya rasa, in kuma ya ganta a hannuna nasan dukan tsiya zan sha, kuma su kore ki daga aiki ace mun 6arauniya, yanzu ya zanyi ni nasamu na mayar masa da wayarsa wayyo Allah na, Ƙarar shigowar message ne taji ƙirrrr! da sauri ta duba, account number ne jahad ta turo mata, cikin sauri ta laluba cikin drawer chest, inda ta ajiye diary din da take rubutu acikinsa Wanda tazo dashi , biron da ta saka a tsakiyar littafin ta dauko ta bude page tayi copying numbers ɗin, tana gama wa , ta mayar ciki ta ajiye, Sannan ta yi hanzarin deleting sakon daga wayar tasa, fitowa tayi daga ɗakin tana leken ko akwai mutun, duk basu kai da fito wa, har tasa hannu zata koma ciki taji alamun mutun, junaid ɗin ne ya fito yana naɗe hannun rigarsa, da alama masallaci zai wuce, Ba karamin dadi taji ba, yana fi ce wa, ta lallabawa cikin sauri ta shiga ɗakinsa ta ajye masa wayar a saman nightstand, Fito wa tayi tana sauke ajiyar zuciya, yanzu abunda ya rage mata takai ma azmi acct number ɗin, ɗaki ta koma, ta ɗauki diary ɗin ta yago papern data rubuta numbar, ta fito ta tunkari ɗakin azmi, dayake ba nisa yana kusa da nata, wannan ne karo na farko da ta fara shiga ɗakin ta, Sallama tayi, azmi dake zaune saman sallaya ta amsa da "wa'alaikum salam shigo ciki," Cikin natsuwa sehrish ta shiga ciki, wuri ta samu ta zauna kusa da ita ta lankwashe kafarta tayi zaman cin tuwo, Cazbaha take ja, a hannunta ɗan murmushi tayi tace"wai malam tukur ne yau a ɗakin namu kodai mafarki nake ne? Cikin jin kunyarta sehrish ta ɗukadda kai tana murmushi, "tabbas kuwa shine to mara ba lale marhaban daga ganin wannan gashin bakin naka akwai magana," dariya ce ta kubce ma sehrish, ta shiga 6a66aka ta, daga bisa ni ta tsagaita tare da cewa "aunty azmi dama acct number ɗin ne na kawo miki," ta karasa maganar tana miƙa mata paper ɗin, karba azmi tayi tare da fadin"kin tabbata ta likitance? Sehrish ta ɗaga kai tare da cewa "Eh tashi ce," "Toh shikenan kije kawai insha Allah zuwa gobe za'a tura masu kudin," Azmi ta fada tana adana takardar a saman carpet din, Godiya sehrish tashiga yi mata har da matse ƴar kwalla, murmushi azmi tayi tace "Ki gode wa Allah, domin shine abin godiya, kuma shine silar shigowarki gidan nan! ," jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayanan azmi, daga bisa ni ta tashi ta fice, A bangaren su twins kuwa lokacin da suka shiga ɗakinsu suka tarar angyara ko ina tsaf, jahan ya kalli ayaan tare da cewa "yaushe zaka daina wannan gangancin ne !," ya faɗi hakan rai abace, cikin rashin sanin laifin daya aikata yace "what do you mean? tsoki jahan ya saki tare da ƙarasawa gaban dressing mirror, yakai hannu ya ɗauko kwalbar maganin nan ya ce"wannan nake nufi !" ɗafe kai Ayaan ya yi tare da faɗin "Omg!! am sorry for that, ni kaina na manta ban mayar ba," harararsa jahan yayi ya ce "we're sorry for our self dai !
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113