Chapter 3
Chapter 3
jikinta ya yi mugun sanyi tuni kwalla ta ciko mata a idonta, saboda ba karamin wahala tasha ba, kusan kullum tana fama zaryar zuwa gidan matar neman aiki, tunanowa da ta yi da halin da 'yan uwanta ke ciki ne ya sa ta ji ba za ta iya hakura ba komai zai faru sai dai ya faru, amma ba inda za ta je sai ta samu aikin da za ta samu kudi, saboda ta san ba wanda zai taimake ta ya ba ta kudi haka nan don Allah face ya nemi wani abin daga gare ta. Tamkar za ta fashe da kuka ta ce, "Don Allah ki taimaki wallahi ko wane irin aiki ne zan iya yin sa. Ki taimaka mini 'yan uwata na kwance asibiti ba ta da lafiya kuma aiki za a yi mata, kudin da doctor ya fada ba mu da su kuma ba mu da wanda zai taimaka mana ni ce kawai nake fafutuka akan yadda zan samu na biya." Ganin yadda yarinyar ta bi tana rokon ta cikin lallami ya sa ta ji tausayin ta ya shiga ranta, "Ya isa haka, share hawayenki. Nawa likitan ya ce kudin aikin nata?" "Dubu dari takwas ne." Ta ba ta amsa tana kokarin goge hawayenta. Jinjina kai hajjaju ta yi jin kudin, "Da a ce ina da su da na taimaka da wani abu amma halin da muke ciki yanzu komai tsada hakan yasa kudi ba sa jimawa a wurina. Amma yanzu abin da nake so na sani ina ne gidanku saboda dare ya yi sosai, na mayar dake gid, idan kuma za ki tsaya nan is shike nan in yaso gobe sai ki koma ko?" Cikin sauri ta ce "Zan tsaya a nan, ba kowa gidan suna asibiti kuma na yi sallama dabsu babzan sake komawa ba har saibna fara biyan kudin aikin, babzan iya jure ganin su cikin mawuyacin hali ba!" Hajajju ta ce "To shike nan amma gobe zan bincika kuma za mu je asibitin tare saboda ba na daukar yaro ba tare da iyayensa ko wani nasa ya sani ba!" Yarinyar ta amsa da, "To!" Larai ce ta shigo dauke da faranti, ta jera sinkin bread guda 3, sai jug mai dauke da tea da kananan kofuna, a jiye masu tayi sannan ta koma ta dauke sauran abin da ta hada musu a kicin. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Hafsat Bature_* ~(Boss Lady)~ Page 3-4 Tun da y'ammatan nan suka ga bread suka gaza samun natsuw, sai kokarin zura hannu suke su dauka, ganin haka yasa ta taso da kanta ta rarraba musu ta bawa kowa nasa, dawowa larai tayi dauke da karamin tray wanda ta baza musu taliyan a ciki ta ajiye masu, zama sukayi suna ta aikin ci, ita dai a hankali take ci tana kallonsu hannu baka hannu kurya suke cunkusa wa a bakin, bakomai yazo mata a ranta ba face y'an uwanta, in ta tuna irin wannan yanayin sai taji komai ya fita ranta. Bayan sun kammala ci , hajjaju ta kai isu zuwa bedroom din da ta ware domin irinsu in ta dauko su anan suke kwana sannan ta yi masu sallama ta fice, tana fita y'an matan kauyen nan suka haye saman bed din dake ciki kuma shi kadai ne, bin su da kallo tayi ganin yadda suka wawware kafafunsu saboda kar tasamu wuri tace zata hau. Murmushi tasaki, "Allah sarki rayuwa ni ina ne bazan iya kwana ba, bed is ur problem, Sisters dina sune damuwata, Cire hijab din dake jikinta tayi, wardrobe din dake manne a bango, ta bude babu wasu kayan kirki a ciki, zannuwan atamfa ne kawai, saka hijab din tayi ciki ta rufe, toilet din dake ciki ta shiga, komai na ciki a tsaftace yake, fari kal! Gaban mirror ta karasa tana kallon fine face dinta, fanfo ta kunna ta tarba hannuwanta tana wanke fuskanta, bayan ta gama tasa hannu ta cire head din dake kanta, ta yi holding dinsa a hannunta tana kallon doguwar kitson kalabar da akayi mata guda biyu ta zubo tun daga head dinta har zuwa west dinta, tana da Yalwatacciyar sumar kai dark brown colour very smooth ga kwantaccen saken gefen fuska. Fitowa ta yi daga toilet din, samunsu tayi sai minshari suke ja tamkar raguna, wardrobe din ta sake bude wa daya daga cikin zannuwan da ta gani ciki ta dauko, ta shimfida a kasa, ta kwanta Washe gari tunda sassafe suka fita, hajajju ce ke driving yayin da yarinyar take a gefenta , sai kalle kallen hanya take ta glass din motor, hajajju ta ce "Har yanzu baki fadamun sunanki ba ! da age dinki yakamata nasani ko"? tayi maganar ne a lokacin da take kokarin juya sitiyarin motar wurin canza hanya tabi titin da zai kai ka har izuwa asibitin. Murmushi yarinyar tasaki tare da cewa "Sunana SEHRISH amma Oumman mu tana ce mun RISHI , shekarata 17 cif ," jinjina kai hajajju tayi tace "Wow nice name and it really deserves , " cike da jin dadi Sehrish tace "thanks" har suka isa asibitin basu kara magana , Sehrish tayi ma hajjaju jagora har izuwa ICU intensive care unit , inda aka kwantar da sisters din nata, lokacin da suka shiga ciki, da gugu wata kyakkyawar yar matashiya ta taso ta rungume sehrish, tsananin mamaki yasa hajajju sakin baki, sai ta dinga ganin tamkar mafarki take yi, tun da Allah ya halicce ta bata taba ganin yara masu shegen kama irin wadannan ba basu da wani banbanci ko miskala zarratin komai nasu iri daya sak , lokaci guda ta rikice takasa gane wacece ma suka zo da ita, wacece sehrish din don ta saje da dayar, hajjaju bata gama mamaki ba sai da taga dayar wadda take kwance saman gadon marasa lafiya ansa mata Oxygen dakyar take jan numfashi gwanin ban tausayi , nan takara rikicewa saboda itama wacce take kwancen Sak kamaninsu ba banbanci hakan na nufi su y'an uku ne kenan. Kankame ta tayi tana kuka , itama sehrish din kukan takeyi hannunta tasa tana d'an bubbuga bayanta tace "Jahad ki daina kuka hankalina yana kara tashi komai zai tafi dai dai insha Allah, janye jikinta tayi daga nata tace "ina kuka ne ba don kai na ba sai don Husanna dr yace in ba mu fara biyan kudi an mata aiki ba , mutuwa zatayi kuma ynx haka kudin gado ya kare sallamar mu zasuyi ko kudin magani babu ," hankalin Sehrish ba karamin tashi yayi ba, Hajajju dake tsaye tana kallonsu, jikinta yayi mugun sanyi saboda tsananin tausayi, ita kanta wadda sehrish takira da Jahad akwai wound a goshinta, anyi mata dressing da bandage duk jini a jikin sa , hannunta ma akwai kanula alamun anyi mata karin wani abu jini ko ruwa , a kagare hajajju take da taji labarin wadannan y'an ukun lallai bakaramar wahalar rayuwa suka sha ba. Muryar Sehrish ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga "Jahad ga hajajju ku gaisa kuma kiyi mata godiya sbd itace zata sama mun aikin da zan fara yi nasamu kudi nabiya ayi maku aiki," matsawa tayi gaban hajjaju tana share hawayenta cikin girmamawa tace" ina kwana hajiya ," murmushi hajajju tasaki tare da dafa kadarta tace "lafiya lou ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113