Skip to content

Chapter 72

Chapter 72

Abban Sojoji Book One Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

da motar Hajajju ta shigo da ita cikin gidan, tabbas tagansu a time ɗin suna buga wasan kwallo, kamar yadda dae take kallonsu a yanzu, amma awancan lokacin, shi dasu twins ne da fawan suke kwallon, sa6anin ynx da masu gadin gidan suke buga wasan, "Allah sarki junaid, ji bi yadda yake ta faman shan wahala wurin taro ball suna kwace mashi, maimakon yaji haushi amma sai faman murmushi ma yake yi, shi dae baya gaji da murmushi a face ɗinsa," Tayi maganar nan a lokacin da take ƙoƙarin zuge glass ɗin windon, ta janyo labulen ta rufe, tana sauke ajiyar zuciya, tunanin ta ya koma kan Babban yaya wanda tun da safe take jiran saukowarsa, amma bai fito ba, ko breakfast bai sauko ya ci ba, hakan yasa ta cikin damuwa sosai, "Bari dae na fita naje na tambayi aunty azmee, ko naje na tashe shi in bacci ya ke yi "? tayi maganar a fili, cikin sauri ta ƙarasa saman bed ɗinta, ta ɗauki dogon wandonta ta zura, dama daga ita sai riga dai-dai guiwa, Gashin bakinta kawai ta ɗauko a saman mirror, ta maƙala shi kafin ta fice daga ɗakin, A hankali take tafiya, a main parlor ɗin ta hangi su Abbansu tare da wani Amininsa Alhajin gaske daya kawo masa ziyara, Su biyu suna tattaunawa, saɗaɗawa tayi ta wuce kitchen, anan ta sami aunty aunty azmee tana shirya musu drinks a tray, cikin wasu kofuna masu kyau, "Yauwa rishi dama yanzu nake ƙoƙarin zuwa na tashe ki, kin barni da aiki ko," ? ta tambaya tana kallonta, Cikin jin kunya Sehrish tace"Am sorry aunty azmee wlh, ina shiga bedroom ɗina naje na watsa ruwa, kawai sai bacci 6arawo ya ɗauke ni," Dariya azmee tayi azmee tayi tare da cewa "Bacci 6arawo ko? mutun yaje ya saki baki yana bacci, kuma yazo yace wa mutane wai baisan ya akai bacci ya ɗauke sa ba,' Murmushi sehrish tayi tare da miƙa hannu ta kar6i tray ɗin da azmee ke miƙa mata, Amsa tayi tana cewa "Aunty azmee wanene baƙon da yazo "? "Ki je ki tambaye sa mana, ki ce wanene kai zai baki amsa," Dariya sehrish tayi jin amsar da azmee ta bata, ɗan zaro ido tayi tare da cewa "tab dana sha mari wlh," Azmee tace " ba wani mari wlh, amsa kawai zai baki da yaren da zaki gane," "Ae wannan bugu kenan," ta faɗi tana kokarin fita, har ta sa kai zata fice ta kuma juyo wa tare da cewa " Aunty azmee babban yaya fa, bai fito daga bedroom ɗinsa ba ko lpy,"? "Ki je part ɗinsa mana ki tambaye sa," ta faɗi cikin zolaya, ɗan ta6e baki sehrish tayi tana jinjina kai tace "wai Allah ! ni asuwa? ɗan wake a hotel,"? dariya azmee tayi tare da cewa "ynx dae kije ki kai musu, kin tsara surutu kamar ƴan jarida, " Cikin sauri sehrish ta fice izuwa cikin main parlor ɗin, cikin natsuwa take tafiya tunkan ta isa, tajiyo muryar abokin abban dayazo yana cewa "Ae ni ba ƙaramin daɗin zuwan nan nasu Rafayet da Omar naji ba, koba komai kafin su koma U.s zasu gyara wa wasu zama A Qasar nan," Abba yace "Oh damuwarka kenan, baka damu da bala'en da zai jawo mun ba, kwarama Omar shi da sauƙi, amma rafayet kana ganin last da yazo ya rinƙasa ana kawo masa ƴa'ƴan mutane har cikin gidan nan yana hukunta su, babu yadda zanyi dashi, sai dae nabishi da ido kawai, saboda yafi ƙarfi na,' Dariyar Alhajin yayi tare da cewa "Ae samun ƴa'ƴa kamar Omar da rafayet wlh abun alfari ne, kowane Uba zai so ya mallaki ƴa'ƴa irinsu, gashi ynx asanadinsu darajarka da ta family ɗinku ta ɗaukaka sosai a faɗin duniyar nan, Kowa yabonsu ya ke yi, yakamata karinka alfahari dasu, mu gana mu nan ƴa'ƴan shaggu kamar mata, basa iya ta6akawa ƙasa komai, ga Jabeer nan har asibiti na gina masa in yadawo daga Uk ya ci gaba da kula dashi, amma yaron nan ya watsa mun ƙasa a ido, wai shi yafin karfin ya yi aiki a nigeria, Naji haushi lokacin duk mun lalacewar kasarka ae ƙasarka ce," Cikin nuna takaici Alhajin yakewa Abban wannan bayanin da sallama Sehrish taƙarsa cikin girmamawa ta gaishe su, suka amsa mata sannan ta miƙa musu drinks din suka ɗauka suna sa mata albarka, bayan sun gama ta kama hanyar komawa cikin kitchen, wani irin son Babban yayan ne ya kara shiga ranta, jin yadda Abokin abban nasu ke yabonsa, murmushi kawae take saki, ynx ta kara jin ya kwanta mata luf acikin ranta, Shiga kitchen ɗin tayi tare da ajiye tray ɗin, azmee tace "yanzu sai ki je, ki gyara masa part ɗinsa ko? tayi maganar tana kallonta, Sehrish tace "Yana fa ciki, kuma kince baisan atashe shi yana bacci, kuma baisan ƙara, in nayi kwaratsi fa zai ji harya farka," Murmushi azmee tayi tare da cewa " to ina ruwanki da bedroom ɗinsa? Falonsa zaki fara gyara wa, kafin ya tashi sai ki gyara can ɗin ko ? Sehrish tace "To bari nace" tafice tana fargaba, tana jiyo muryar Aunty azmee tana cewa "Anaso ana kaiwa kasuwa," Ƴar dariya tayi tare da fi ce wa, kai tsaye part ɗinsa ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar, Kamar kullum a buɗe door ɗin parta ɗinsa take, a hankali tashiga tana sanɗa kamar 6arauniya, Sai da tayi tsakiyar falonsa nasa tasoma tunanin wai me ma tazo yi? Saboda ko'ina agyare yake tsaf ba datti ko kaɗan, sai walwali wurin yake har yau tana jinjinawa haɗuwarsa, Murmushi tasaki tana wani tunani aranta, wanda bazai yiyu ba, 😔 Sai da tagama zagaye falon nasa tana tunani iri iri aranta, sannan ta soma gyara sa, babu wani aiki awurin, kawai ta ɗan yi goge goge ne, tsayawa tari riƙe da waist ɗinta, so take ta sashi a idonta, zuciyarta ce ta bata shawara da cewa "ki ɗan leƙa sa, mana," "Anya? idan kuma idonsa biyu fa? In ya kama ni karairaya ni zae yi Allah,' ta bata zuciyarta amsa, "Ke sai ki bari ya ganki? Ae lalla6awa zakiyi a hankali sai ki dan leƙa,' Murmushi tasaki tare da tafiya cikin sanɗa, ta tsaya a bakin ƙopan ɗakin nasa, taci sa'a kopan a bude take, curtains ɗin ta ɗan janye tana leƙensa, 👀👁️ Kwance ya ke yana sharar baccinsa, cikin natsuwa a saman Royal bed ɗinsa, kai ka ce da zallar gold aka ƙera gadon, yadda ya ke wani kyalli ajikinsa, Half body ɗinsa yayi covering ɗinsa da lallausan blanket, hannunsa na dama, ya zagayo dashi har izuwa saitin left ear ɗinsa, yayin da hannunsa na hagu kuma ya ke a saman wide chest ɗinsa, Bin shi take da kallo kamar kura taga nama, wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, ta rufe masa half face ɗinsa, dogon hancinsa kawai take hange, Lumshe ido kawai take, ita kaɗae tasan yanayin da ta shiga, Tana cikin wannan leƙen nasa ko ƙeftawa babu, taji an shaqi wuyanta da ƙarfin gaske, Shaqa ba ta wasa ba, Wani irin tsoro ne ya ziyarce ta, hankali atashe ta zazzare idanunta, Muryarsa ce ta ratsa kunnanta da cewa "meyasa ki ke leƙe na !!"? wata irin zufa ce ta wankowa sehrish, tsananin tashin hankali

Table of Contents

Chapters

113 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113