Chapter 8
Chapter 8
, wasu hamshan royal sofa ne aciki , set shida ne a jere , ko da ido ka kallesu kasan zasuyi laushi da dadin zama , duk yawansu basu cike falon ba saboda girmansa ya isa a gina madai madaici gida acikinsa, Komai da ake bukata acikin falo akwaisa sai da ba tarkacen nan na hauka komai a natse , Bin ceiling din tayi da kallo ba irin rufin da tasaba gani bane , wannan na glass , acikinsa akwai light bulbs masu haske wurin , Hankalin hajjaju ba karamin kwanciya yayi ba ganin falon tsit ba kowai sai sanyin a.c dake ratsa sassan jikin mutun, dama zullumin ta ace wadannan sojojin na nan , Ruko hannun sehrish tayi wadda hankalinta ke kan twin stairs din da tagani wato tagwayen bene guda biyu wadanda zasu kai ka upstairs, tsantsararrun gaske , Sehrish tace "hajiya naji tsit ko ba kowa ne ? hajjaju tace "ina ga duk suna wurin aiki , mu samu wuri mu zauna mu jira wata'kil mai aikinsu na nan ," Suna kokarin zama suka ji takon takalmi daga left dinsu , karfaffar maca ce irin giantess dinnan , tana da hasken fata , jikinta na sanye da doguwar riga ta atampa har kasa ta kashe daurin d'an kwalinta , tana ganin hajjaju ce ta saki fara'a tana fadin "me nake gani kamar hajjaju makkatin "? murmushi hajjaju tasaki tare da cewa "kwarai kuwa nice AZUMI ashe kina ciki , nayi tunanin ba kowa ciki ne ," Karaso wa tayi inda hajjaju take tayi hugging dinta tana cewa " I really missed u alot hajjaju kin boye mana nayi expecting din bakya kasar ne ," sakin juna sukayi hajjaju tana dariya tace "Ina nan mana ina zani an gaya miki ynx barin kasar nan sauki ne yadda komai ke kara farashi , yar dubai dinnan danake zuwa kamar hauka ynx nadaina saboda rashin kudi ," Murmushi azmi tasaki , tare da nuna masu wurin zama tace "bismillah ku zauna bari na shiga na kawo muku abin sha , firar zata fi dadi idan kuka jika makoshinku , tana gama fadan hakan tajuya ta nufi hanyar da zata kai ka kitchen dinsu , zama sukayi a tare saman 3 seater , har lokacin sehrish na makale da yar jakarta a kirjinta , sai karewa falon kallo takeyi tana jinjina kyansa , wai itace zata rayu a cikin katafaren gidannan , wayyo dadi boye farin cikinta kawai take yi , ta wani bangaren kuwa hankalinta a tashe yake , saboda batasan ya rayuwarta zata kasance ba a matsayinta na yar basaja , matsayin namiji a gidan sojoji , Dawowa azumi tayi hannunta dauke da tray , plate ne mai dauke da snacks , sai 2 cups da jug , a jiye su tayi a sman table sannan ta janyo shi izuwa gabansu ta ajiye , Koma tayi tazauna tana murmushi , Sehrish kuwa sai kallon matar take yi har taji ta burgeta saboda tana son mutum mai fara'a , Lemu ne a cikin jug din zuba musu hajjaju tayi ta mika ma sehrish , cikin sauri ta karba dama kishi take ji , kurbarsa tayi wani irin sanyi ya ratsa ta ga dadin gaske , Azumi ta bi ta da kallo cikin mamaki tace "in ce ko wannan ne d'an aikin da akace za'a kawo mana"? hajjaju ta danyi guntun murmushi tace "eh shine sunan shi tukur kwararre ne wurin iya sarrafa abinci ," saboda jin karyar da hajjaju ta shirgo akanta yasa ta kusa fetsar da lemun da takurba a bakinta , abunda ya kusa sata ta shake shine da ta ce kwararrene wurin iya sarrafa abincin shin yaushe ta son da wannan ? Sauraron hajjaju ta ci gaba dayi jin tana introducing dinta a wurin azumi " yaro ne mai matukar basira ga wayau , zakiji dadin yin aiki dashi ," takarsa maganar tare da ajiye cup din dake a hannunta saman table din gabanta , sannan ta kalli sehrish tace "tukur wannan itace azumi , itama y'ar aiki ce a gidannan amma taji ssae tana kula da yaran gidan hakan yasa ta zama tamkar uwa agaresu , ina fata zakuji dadin yin aiki da juna ," Dakyar sehrish ta kakaro murmushin dole tace "Insha Allah hajiya ," Ita kadai tasan halin da ta shiga , wannan zaman da tayi ji ta , kamar ta dosa na ass dinta a saman wuta , saboda tsabagen tsoro , A ranta sai maimaita kalmar 'yaya goma sha takwas kuma duk sojoji take yi , Azumi ta janye idonta daga kan sehrish (tukur) ta mayar da idonta kan hajjaju tare da cewa "am inaso na tambaye ki tundazu maganar ke shigemin meyasa kika daina leko mu bayan ina da tabbacin cewa kina zuwa abuja zuwane kawae ke baki yi ," Murmushi hajjaju tayi tare da yin yar dariya tace "ai dole zuwa gidannan ko jaraba ! oh kin manta Abunda ya faru last time dana zo ko ? Ina wannan BABBAN YAYAN nan nasu wani mai shegen kyau tubarkalla kamar d'an sarkin aljanu mai kirar zakunan nan ," dariya azumi tayi tare da cewa "wai wa kike nufi cikinsu , kinsan suna dayawa , akwai major , akwai Captain ga janar , akwai Marshall ga kuma Canal da sauransu , kowa da sunan da ake kiransa " takarasa maganar tana kallonta Sarai tasan wa take nufi amma tafiso taci gaba da zuzutashi don hajjaju ta iya bada labari , taci gaba da cewa "oho nidai nasan shi kadai suke ce ma babban yaya , ina gaya miki last dana zo , lokacin nazo dubiyar wannan younger bro dinnasu mai asthma wanda aka fidda kasar waje akayi masa aikin a kirjinsa , " azmi tace "oh nagane junaid kike nufi ae suna waje suna buga ball ynx yaji sauki Alhmdllh ," Hajjajun ta ci gaba da cewa "ina fadamiki daga zuwa abun arziki , wlh ina shigowa falon nan ni bansan meya faru ba , nasame shi da y'an uwannan nasa sae faman rirrike shi sukeyi sai huci yake yi just like a hungry lion from the bush gaba daya yayi watsi dasu kasa , ya daga dining table yayi wurgi dashi , gabana ya fadi rass banyi aune ba naji yace "don ubanki kama hanya ki fice, ashe ya ganni " Wallahi a tsorace a fujajen nabar gidan don tsabagen rudi , da kafa nakama hanyar fita babban gate din saida wani soja cikin security din gidan nan yace mun hajiya kin manta motarki , sannan fa natuna jiki na rawa nakoma nadauko," Tun kafin ta idasa labarin azumi da sehrish suke ta faman tikar dariya , kamar cikinsu zai kulle , ita kanta hajjajun dariyar take yi , dakyar azumi ta tsaida dariyarta tace "Hmmm sai ynx nagane wa kike nufi , ai da kinsani ba ki daina kawo mana ziyara ba domin shi ba sojan nigeria bane , US ARMY ne ba a kasar nan yake ba yna dai zuwa sometimes in yasamu hutun aiki ," Hajjaju tace "bazaki gane ba ne , yadda na tsorata , ai ko ba don shi ba , wadannan tantiran na gidannan marasa jin magana..." Azumi ta katse mata maganarta ta da cewa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113